Home » IHRC-RFT Ta Yi Kira Ga Gaggawar Sake Duba Tsarin Shari’ar Manyan Laifuka

IHRC-RFT Ta Yi Kira Ga Gaggawar Sake Duba Tsarin Shari’ar Manyan Laifuka

Isiyaku Ahmed
A+A-
Reset

A matsayina na Shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama kuma Mai Sharhi Kan Harkokin Tsaro, ina ganin ya kamata mu faɗi gaskiya ba tare da boye ta ba: a lokuta da dama, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suna yin aikinsu yadda ya kamata.

Suna kama waɗanda ake zargi, suna gudanar da bincike, tattara bayanai da hujjoji, sannan su miƙa waɗanda ake zargi gaban kotu domin a yi musu shari’a.

Sai dai abin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a shi ne abin da ke faruwa bayan an kai waɗannan mutane gaban kotu.

A wasu lokuta, mutum da ake tuhuma da manyan laifuka kamar kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami ko wasu manyan laifuka, bayan an kama shi kuma an fara masa shari’a, sai bayan ɗan lokaci a ga ya sake fita cikin al’umma.

Wannan yana haifar da tambayoyi masu yawa: Ina matsalar take?

Ba muna kira ne da a tauye haƙƙin wanda ake zargi ba. A matsayina na mai kare haƙƙin bil’adama wanda yasan doka da shari’a, na yi imani cewa kowa yana da haƙƙin adalci, kuma wanda ake zargi ba za a ɗauke shi mai laifi ba har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

Amma kare haƙƙin wanda ake zargi bai kamata ya zama barazana ga haƙƙin waɗanda aka cutar da kuma tsaron al’umma ba.

Dole ne a yi la’akari da nauyin laifin, haɗarin da ake iya fuskanta, yiwuwar tserewa, tsoratar da shaidu ko lalata hujjoji wajen gudanar da shari’ar, kamar yadda doka ta tanada.

Saboda haka, muna kira ga Mai Girma Attorney-General na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Kwamishinonin Shari’a na Jihohi, Majalisar Dokokin Tarayya da Majalisun Dokokin Jihohi, Chief Justice of Nigeria, Chief Judges na Jihohi, da duk masu ruwa da tsaki a harkar shari’a da su gaggauta duba wannan lamari, gudanar da bincike kan matsalolin da ke haifar da irin wannan yanayi, tare da ɗaukar matakan da suka dace.

’Yan sanda suna yin ƙoƙarinsu; tsarin shari’a ma dole ya tabbatar da cewa ƙoƙarin jami’an tsaro bai tafi a banza ba.

Idan jami’in tsaro ya jefa rayuwarsa cikin haɗari wajen kama wanda ake zargi da aikata babban laifi, bai kamata tsarin shari’a ya kasance hanyar da zai sake komawa kan titi ba tare da an tabbatar da cewa an bi dukkan matakan doka yadda ya kamata ba.

A lokaci guda, muna jaddada cewa adalci dole ne ya kasance daidaitacce: a kare haƙƙin wanda ake zargi, a kare wanda aka cutar, a mutunta aikin jami’an tsaro, sannan a tabbatar da cewa wanda aka tabbatar da laifinsa ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Kama wanda ake zargi mataki ne na farko; tabbatar da adalci shi ne abin da ya kamata ya biyo baya.

Muna kira ga hukumomin shari’a da su ɗauki mataki cikin gaggawa kafin wannan yanayi ya ƙara raunana amincewar jama’a ga tsarin shari’a da kuma ƙoƙarin jami’an tsaro na yaƙi da aikata laifuka.

Sa hannu:

Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Country Director, IHRC-RFT Nigeria Chapter
Shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama kuma mai Sharhi Kan Harkokin Tsaro

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.