Inji Farfesa Usman Yusuf
Farfesa Usman Yusuf ya mayar da martani kan sabuwar majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC, wadda Sanata Abdulaziz Yari zai jagoranta a matsayin Babban Darakta, inda ya yi mata fatan rashin nasara yayin da take shirin zagayawa domin tallata gwamnatin Tinubu ga ’yan Nijeriya gabanin zaɓen 2027.
A wata hira da ya yi da Symfoni TV (https://youtu.be/xZ9ED0uKu7w), Farfesa Yusuf ya ce majalisar yaƙin neman zaɓen ta ƙunshi haɗakar mutane iri-iri “na gari, da marasa kyau da kuma munana”, tare da nuna shakku a kan sahihancin wasu daga cikin mutanen da aka zaɓo domin yaƙin neman goyon bayan gwamnati.
A cewarsa, ’yan Nijeriya suna jiran mutanen da za a tura su sassan ƙasar nan domin tallar gwamnatin Tinubu da kuma shawo kan jama’a su sake zaɓarta a 2027.
Ya ce: “Shugaba Tinubu ba zai gudanar da yaƙin neman zaɓe irin yadda aka saba gani ba. “Ya ƙara da cewa ’yan Nijeriya ba za su ga Tinubu yana zagayawa ƙasar nan domin neman ƙuri’a kamar yadda tsohon Shugaba Marigayi Muhammadu Buhari ya yi ba.
Yusuf ya kuma yi zargin cewa Tinubu ba shi da ƙoshin lafiyar ko ƙarfin jikin da zai iya gudanar da irin wannan yaƙin neman zaɓe na ƙasa bakiɗaya, yana mai cewa Shugaban Tinubu ba zai iya fuskantar jama’a kai tsaye ba.
Ya ce saboda haka gwamnatin Tinubu ta ba ’yan siyasa, da wasu malaman addini da mawaƙa da ‘yan fim kwangilar “sayar mana da wannan yaudarar”.
Game da naɗin Sanata Abdulaziz Yari a matsayin Babban Darakta na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen kuwa, Yusuf ya amince cewa zaɓen tsohon gwamnan Zamfara mataki ne na dabarun siyasa, amma ya tambayi abin da Yari zai gaya wa mutanen Arewa.
Ya ce: “Ina kyautata zaton cewa Shugaba Tinubu ya cema Sanata Yari ne: ‘“kaje ka yi magana da mutanenka, je ka samo mani ƙuri’u.’”
Sai dai Yusuf ya ce a yanzu Sanata Yari jam’iyar shi bata da farin jini wurin jama’a, yana mai cewa bai yarda tsohon gwamnan Zamfara zai iya samun nasarar shawo kan mutanen Arewa su goyi bayan Tinubu ba.
Farfesan ya kuma yi nuni da irin goyon bayan da Arewa ta bai wa Tinubu a zaɓen 2023, inda ya ce kashi 62 cikin kashi 100 na ƙuri’un da Shugaban ya samu sun fito ne daga Arewa, musamman Musulmin Arewa.
Ya ce yanzu kam jama’a za su tambayi kansu wace irin riba suka samu daga wannan gwamnati, sannan su kwatanta halin da jihohin Arewa suke ciki da wurare kamar irin su Legas.
Ya ce: “Jihar Legas, jiharsa, ba ta zaɓe shi ba amma Katsina, jihata, ta zaɓe shi. Don haka mutane za su kwatanta su auna: Me Legas ta samu? Me Katsina ta samu? Me ya sa za mu sake zaɓenka?”
Yusuf ya ce wato lissafin abu ne mai sauƙi, domin siyasa tana da alaƙa da lamuran cikin gida, kuma tana da alaƙa da abin da ke cikin aljihun jama’a. Ya jaddada cewa ’yan Nijeriya suna fama da tsadar rayuwa, ga talauci da yunwar da aka kawo masu kuma da taɓarɓarewar tsaro.
Ya kuma tambayi abin da Sanata Yari zai gaya wa mutanen Zamfara, kasancewar shi tsohon gwamnan jihar.
Ya ce: “Me za ka ce wa mutanen Zamfara? Shin yanzu tsaro a Zamfara yafi inganta fiye da yadda yake a da kafin gwamnatin ku tazo?”
Yusuf ya ce Zamfara tana da muhimmanci sosai a gare shi, domin ya yi karatu a Government Secondary School, Gusau (Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gusau) kuma ya tuna irin jihar da ya sani shekaru da dama da suka gabata.
Ya ce duk lokacin da yaga yadda jihar Zamfara take yanzu sai ya zubar da hawaye, yana mai bayyana sauyin da jihar ta samu a matsayin abin jimami da raɗaɗi, idan aka kwatanta da yanayin zaman lafiya da ya sani a lokacin da yake girma a jihar.
Dangane da shirunsa na baya-bayan nan kuwa, Yusuf ya bayyana cewa ya yi shiru ne yana kallon yadda abubuwa suke gudana tare da jiran ganin yadda gwamnati da majalisar yaƙin neman zaɓenta za su fuskanci jama’a a kan ƙalubalen da ’yan Nijeriya ke ciki tsundum.
Ya ce: “Ku dai kalli yadda komai zai kasance, da yadda za su yi abin da suke shirin yi, domin dukkansu suna ta kai komo ne don basu san abin da za su yi ba.”
Ya ce yana jiran saƙon gwamnati na gaskiya, ba farfagandar da ke fitowa daga Abuja ba. Ya soki ’yan siyasa da masu karɓar haraji waɗanda ke gabatar da alkaluman ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya, da ajiyar kuɗi da nasarorin gwamnati ba tare da danganta su da rayuwar yau da kullum ta ’yan Nijeriya ba.
Ya ce: “’Yan siyasar Abuja suna magana ne a kan alkaluma waɗanda ba su da wata alaƙa da rayuwar mutanenmu ko kaɗan. Babu.”
Yusuf ya kuma yi tambaya a kan yawan mutanen da aka sanya a Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen, inda ya ce sun haura 100, yana tambayar ko kasancewar gwamnoni da dama, da ‘yan majalisa da sauran manyan ’yan siyasa zai haifar da wani gaggarumin canji.
Daga nan sai ya yi nuni da sabon sauyin siyasar da aka samu a Jihar Osun (Oshun), yana mai cewa hakan alama ce ta abin da zai faru idan aka bai wa ’yan Nijeriya dama su bayyana ra’ayoyin su ta hanyar ƙuri’unsu.
Yusuf ya ba da shawarar cewa jam’iyyar APC ta kalli abin da ya faru a jihar Osun a matsayin darasi, yana mai cewa kada jam’iyyar ta ɗauka cewa samun babbar majalisar yaƙin neman zaɓe, da ta ƙunshi gwamnoni, da ’yan majalisa da sauran manyan ’yan siyasa kai tsaye zai tabbatar mata da samun ƙuri’u.
Ya tambaya: “Ashe Osun bai kamata ta koya musu darasi ba?” Yana mai nuni da cewa abin da ya faru a jihar ya nuna cewa tsarin siyasa da muƙamai kaɗai ba su isa su sa masu zaɓe su amince da jam’iyya ba.
Ya ce APC na iya ƙoƙarin gabatar da abin da ya faru a Osun a matsayin shaida cewa Shugaba Tinubu na da ƙwarewa wajen tafiyar da dimokuraɗiyya, inda gwamnati za ta ce Shugaban ya bar komai ya gudana cikin lumana.
Sai dai a cewar Yusuf, gwamnatin Tinubu ta ƙware wajen tsara labari da kuma karkatar da fassarar abubuwan siyasa ta yadda za su amfane ta a ce tana da gaskiya.
Ya ce: “Su ƙwararru ne wajen karkatar da labari. Amma akwai iyakar abin da za ka iya karkatarwa. Idan ka wuce gona da iri wajen karkatarwa, sai abin ya koma akasin haka.”
Yusuf ya ce saboda haka abin da ya faru a Osun ya kamata ya zama manuniya da hannunka-mai-sanda ga APC yayin da take shirin zaɓen 2027.
Ya ce: “Don haka Osun nuni ne, kuma alama ce. Muna jira. Muna jira. Bari su ba da labarin su. Mutane suna jira cikin haƙuri.”
A ƙarshe, ya jaddada cewa ’yan Nijeriya suna kallo kuma suna jiran Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC ta zo gaban jama’a ta bayyana dalilan da ya sa ya kamata su sake zaɓen Tinubu a shekarar 2027.
Ya ce: “Muna jiran labarin da za su ba da. Mutane suna jiran su cikin haƙuri.”
