Home » Kungiyoyin Ayyukan Gaiyya Na Tarauni Sun Sha Alwashin Yashe Magudanun Ruwa Domin Kaucewa Ambaliyar Ruwa

Kungiyoyin Ayyukan Gaiyya Na Tarauni Sun Sha Alwashin Yashe Magudanun Ruwa Domin Kaucewa Ambaliyar Ruwa

Editor
A+A-
Reset

Adamu iliyasu Hotoro

Kungiyoyin ayyukan gaiyya da ke mazabu goma na Karamar Hukumar Tarauni sun sha alwashin ci gaba da gudanar da aikin yashe magudanun ruwa da kwashe shara da ke tare hanyoyin ruwa a fadin karamar hukumar, domin rage barazanar ambaliyar ruwa a damunar bana.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ayyukan gaiyya na Karamar Hukumar Tarauni, Ado salisu Bashir shine ya bayyana hakan a lokacin da kungiyoyin suka gudanar da aikin yashe magudanun ruwa a unguwanni uku da ke Layin Dagaci.

Ado salisu Bashir ya bayyana cewa, kungiyoyin sun dauki wannan mataki ne bisa la’akari da muhimmancin tsaftace magudanun ruwa kafin da kuma lokacin damina, domin tabbatar da cewa ruwan sama yana samun damar gudana ba tare da cikas ba.

Ya ce za su fadada wannan aikin zuwa sauran mazabu da unguwanni na Karamar Hukumar Tarauni, tare da hada kai da al’umma wajen tabbatar da tsaftar muhalli da kuma kare gidaje da hanyoyi daga illar ambaliyar ruwa.

Shugaban kungiyar ya kuma yi kira ga mazauna Tarauni da su guji zubar da shara a cikin magudanun ruwa, domin hakan na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa toshewar hanyoyin ruwa da kuma haifar da ambaliya.

Ado salisu ya bukaci al’umma da su rika tsaftace muhalli a kai a kai tare da kai rahoton duk wani magudanar ruwa da aka samu yana bukatar kulawa, domin a dauki matakin gaggawa.

Daganan shugaban kungiyar Ado salisu Bashir ya godewa Gwamnan jihar Kano, injiniya Abba Kabir Yusif, da shugaban karamar hukumar Tarauni, Ahmed Ibrahim Muhammad sekure dakuma ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano,dakuma ma’aikatar raya karkara bisa yadda suka bawa kungiyoyin aiyyukan gaiyya kayan aikin da suka kamata don cigabada da gudanar da aiyyukan gaiyya a fadin jihar nan.

Dagacin unguwa uku Alhaji Mahe muhammad ya yabawa kungiyoyin ayyukan gaiyya bisa jajircewarsu da sadaukarwar da suke yi wajen tsaftace muhalli da taimakawa wajen kare lafiyar al’umma.

Daganan ya kara da cewa, aikin yashe magudanun ruwa ba nauyin kungiyoyin ayyukan gaiyya kadai ba ne, don haka ya kamata dukkan mazauna Karamar Hukumar Tarauni su hada hannu domin tabbatar da tsaftataccen muhalli da kaucewa ambaliyar ruwa a wannan damina.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.