Kungiyar Kano First Great Mobilization Team ta ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan al’umma da tattara goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma Jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban kungiyan, Hon. Ada’u Liman, ya bayyana cewa ƙaddamar da shirin wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarinta na faɗaɗa ayyukan siyasa da wayar da kan jama’a, tare da ƙarfafa goyon baya ga shugabannin da take marawa baya a Kano da sauran sassan Najeriya.
Ya bayyana Hakan ne a wani taron maneman labarai da a ka yi a Kano ranar Litinin a press center.
Yace a ƙarƙashin shirin, ƙungiyar ta tanadi shugabanni daga ƙananan hukumomi na yankin Kano ta Kudu, waɗanda za su jagoranci ayyukan wayar da kai, haɗa kan mambobi da kuma tattara goyon bayan al’umma.
Hon. Liman ya kara da cewa First Great Mobilization Team tana da burin kare martabar Gwamna Abba Kabir Yusuf da tallafa wa gwamnatinsa, tare da ƙarfafa goyon bayan jama’a ga shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ya ce kungiyan za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da manufofin ƙungiyar, ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta da faɗaɗa ayyukanta a faɗin Jihar Kano.
Shirin dai yana gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙasa da Safayo na Jihar Kano, Abduljabbar Umar Garko, wanda ƙungiyar ta bayyana a matsayin jagoranta.
Ƙungiyar ta nuna kyakkyawan fata cewa shirin zai samu nasara cikin ɗan lokaci, tare da addu’ar Allah Ya sanya albarka a cikin ayyukanta, Ya kuma ba ta damar cimma manufofin da ta sanya a gaba.
Hon. Liman kuma bayyana zaɓen 2027 a matsayin wani muhimmin lokaci da take shirin taka rawa wajen neman nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Jam’iyyar APC, ta hanyar wayar da kan jama’a da tattara goyon baya a faɗin jihar.
