Home » Kwamitin Yaki da Miyagun Kwayoyi na Kano Ya Kama Dan Ta’ammali da Kwalaben Kodin 151

Kwamitin Yaki da Miyagun Kwayoyi na Kano Ya Kama Dan Ta’ammali da Kwalaben Kodin 151

Isiyaku Ahmed
A+A-
Reset

Kwamitin kar-ta-kwana na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi da daba a Kano, karkashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado Esq. ya samu nasarar kama wani hamshakin me ta’ammali da kayan maye dauke da kwalaben kodin guda 151 a dakinsa tare da gurfanar dashi a gaban kotu.

Kotun mai lamba 44 da ke Gwammaja a Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Muhammad Alhaji Isa, ta yanke wa Jabiru Umar Sanda Zage hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan samunsa da kayan maye, da kuma wata shekara ɗayan kan laifin ajiye mata a ɗakinsa.

Lauyan da ya gabatar da shi a gaban kotun, Auwal Abdulkadir Sani Esq, ya bayyana cewa kwamitin ƙar ta kwana dake yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi na Kano, ƙarƙashin Muhyi Magaji Rimin Gado, ya kama shi da kwalaben kodin 151 a ɗakinsa tare da mata uku cikin maye.

An gurfanar da shi bisa zargin shiga ƙungiyar masu aikata laifuka, ta’ammali da kayan maye, bai wa mata da masu aikata laifuka mafaka, da kuma damun jama’a.

Kotun ta yanke hukuncin ne kan laifukan kayan maye da ajiye mata a ɗakinsa. Sai dai bayanan da aka samu ba su fayyace ko zai yi zaman ɗaurin a lokaci guda ko ɗaya bayan ɗaya ba.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.