Home » Kotu ta Umarci a Kama Direban da ya Murkushe Babur Mai Darajar N16m a Kano

Kotu ta Umarci a Kama Direban da ya Murkushe Babur Mai Darajar N16m a Kano

Isiyaku Ahmed
4 views
A+A-
Reset

Babbar Kotun Majistire ta Kano, karkashin jagorancin, Mai sharia Hadiza Muhammad Hassan, ta bayar da umarnin kamo mata Bala Salisu, direban Babbar motar dakon kaya trailer, wanda ake tuhuma da murkushe babur din wasanni mai darajar Naira miliyan 16.

Babur din mallakar Salisu Abubakar Tangland, wanda aka fi sani da Buzzy Pele, jami’in kula da walwalar na Kungiyar Masu Tseren Babura Ta Kasa ya lalace matukar lalacewa.

A zaman da ya gabata, Kotun ta bayar da belin wanda ake tuhuma, sai dai kuma, wani abin mamaki shi ne, lokacin da aka ci gaba da shari’ar, lauya mai gabatar da kara, Barrister Usman Abdullahi, ya shaida wa kotu cewa Bala da wadanda suka karbi belinsa basu halarci zaman Kotun ba na wannan lokaci.

Lauyan gwamnati ya bayyana wa Kotun cewa an tsara cewar jiya Alhamis ne domin fara sauraron shaidun masu gabatar da kara, amma wanda ake tuhuma ya gudu ba tare da wani dalili ba. Bisa ga haka, ina rokon wannan kotu mai alfarma a karkashin Sashe na 351 na Dokar da ta bayar da umarnin a kamo mata wanda ake tuhuma tare da kira ga wadanda suka karbi belinsa da su bayyana a gaban wannan kotu don yi wa kotu bayanin dalilin da ya sanya wanda ake tuhuma ya gudu bayan sun karbi belinsa

Bayan sauraron rokon Lauyan gwamnati, Babbar Majistire Hadiza Muhammad Hassan ta amince da rokon kamar yadda aka nema.

An gurfanar da Direban a gaban kotun ne bisa tuhumar sakaci da tuhumar tukin ganganci, wadanda suka saba wa Dokar Fenal Kod

Ana tuhumar Direban ne da murkushe babur din mai kara a kan gadar Tamburawa yayin cunkoson ababen hawa a Kano.

Anyi ta kokarin gudanar da sulhu a wurin ‘Yan sanda kafin zuwa kotu, amma sulhun ya gagara, tilas ta sanya mai kara ya garzaya kotu domin neman taimakon Shari,a

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 27 ga Afrilu, 2026, domin ci gaba da sauraro.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.