Home » Auren Gatan Kano: Komabayane Ga Tattalin Arziki Da Karuwar Talauci

Auren Gatan Kano: Komabayane Ga Tattalin Arziki Da Karuwar Talauci

Editor
A+A-
Reset

Ahmed ILALLAH

Shin siyasa ne, ko addini, KO bukatuwar al’ummah a kashe makuden kudaden raya kasa domin yiwa mutane aure?

Shin wai menene tunanin shugabanni da al’umar mu, wajen yakar talauci da gina Tattalin arziki?

Shin menene tunanin shugabanni irin na jahar kano dama sauran Jahohin Arewa kan makomar miliyoyin matasan mu da ba san alkibilar da suka fuskanta ba?

A wannan makon ne, Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da Auren Gata ga mutum 3,000 (an daura aure 1,500), har ma aka yiwa wannan ma’aurata hidimar fara zaman aure.

Wannan abun da jahar Kano tayi, tamkar jahar ta dau guba ne ta daddaka a cikin ta, yayin da take cikin cikin tsananin ciwo.

Jahar na daga cikin Jahohin da suke koma baya wajen daidaita yawan al’umar ta.

Jahar Kano ce Jaha ta bakwai da a tafi yawan haihuwa a Nigeria, a kiddiga a duk rana ana haihuwar yara sama da 1000 a jahar Kano.

A kiddiga ta mutanen da sukafi talauci, kashi na 66.3% na mutanen jahar Kano suna cikin kangin talauci.

A cikin cigaban ilimi, Jahar Kano da tafi kowace Jama’iyya yawan Jama’a a Nigeria, tana mataki na 18 a wajen bunkasar ilimi, wanda kawai kaso 38.6% na al’umar jahar ne suke da ilimi.

Ita kanta harkar lafiya ma na fuskantar kalubale a Jahar Kano.

Jihar Kano ce ke da mafi girman adadin mace-macen mata masu juna biyu, inda ake samun 377.8 cikin 100,000 na haihuwar da aka yi cikin rai.

Wannan adadi ya zarce burin ƙasa na mace-macen mata masu juna biyu da aka sanya a matsayin 288 cikin 100,000 na haihuwar da aka yi cikin rai.

Duk jahar da bata warware wannan matsalolin ba, tana sake cusa kanta ne cikin talauci da Koma bayan tattalin arziki. Tana sayawa kanta ne rashin tsaro da ta’addanci.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.