Ɗaliban Najeriya mazauna ƙasar Indonesia, tare da haɗin gwiwar ɗalibai ‘yan ƙasashen waje daban daban, sun gudanar da gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya ta Shekarar 2026 cikin nasara da ƙasaitar al’ada.
Wannan taro mai muhimmancin tarihi an gudanar da shi ne ƙarƙashin jagoranci da kariya ta Sardaunan Hausawan Indonesia, Alh. Abdallah Rabiu Daura, tare da haɗin gwiwa da goyon bayan shahararren ɗan jaridar na, Abdulbaki Aliyu Jari, wanda shi ne ya samar da dabarar gudanar da wannan taro domin ɗaga darajar harshe da al’adar Hausa a duniya.
Taron ya sami halartar Shugaban Ɗaliban Najeriya na Ƙasar Indonesia, Haruna Kawuwa, a matsayin Babban Baƙo na Mutunci (Special Guest of Honor), tare da halartar tarin ɗalibai da baƙi daga ƙasashe daban-daban kamar: Indonesia, Thailand, Philippines, Sudan, Bangladesh, Afghanistan, da Pakistan.
A yayin gudanar da shirin, Sardaunan Hausawan Indonesia, Alh. Abdallah Rabiu, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki, inda ya fayyace tarihin daular Hausawa, masarautu masu ɗinbin tarihi kamar Masarautar Daura, da kuma irin zaman lafiya, mutunci, da haɗin kai da al’umar Hausawa ke da shi da sauran al’ummomin duniya.
Abubuwan da aka gudanar a taron sun haɗa da, Gabatar da jawabi da hotuna akan gine ginen al’ada, sutura, da sarautun Hausawa, Gabatar da nau’ukan abincin al’ada na Hausawa wanda ya burge baƙin ƙasashen waje ƙwarai da aniyya.
Wani hanzari na musamman inda aka koyar da ɗaliban ƙasashen waje yadda ake furta kalmomin Hausa, wanda ya haifar da farin ciki tsakanin mahalarta.
Baƙin ƙasashen waje sun nuna farin ciki sosai, inda suka bayyana cewa wannan rana ta kasance wani muhimmin kwarewa da ba za su ɓata mantawa da shi ba.
Daga: Abdallah Rabiu &
Abdurrashid Lawal & Abubakar Hadejia
