Abdullahi Musa Gyadi
A karamar hukumar Rano, mata da dama ne suka amfana da tallafin awaki don bunkasa sana’o’in su na kiwo.
Da ya ke kaddamar da bada tallafin awaki don bunkasa sana’ar ta kiwo ga matan da suka fito daga mazabun yankin, shugaban karamar hukumar Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano ya shawarce su da su tabbatar sun kula da su ci gaban rayuwar su.
Wannan na cikin sanarwar manema labarai da jami’in yada labarai mai lura da shiyar Rano Malam, Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya rabawa manema labarai bayan kaddamar da shirin a sakatariyar karamar hukumar ta Rano da ke yankin.
Shugaban karamar hukumar Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano ya kara da cewa, shirin yana daga cikin tsare-tsare da manufofin gwamnatin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf da majalisar karamar hukumar na inganta sana’o’i’in mata da sauran matasa a bangarori daban daban.
Daga nan ya shawarci al’ umar karamar hukumar da su ci gaba da baiwa gwamnatin jiha bisa jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf da karamar hukumar hadin kai da goyon baya tare da addu’o’i don samar karin ayyukan bunkasa rayuwa a yankin.
Shugaban sashen gona na karamar hukumar Hassan Abdu Garko yace kimanin mata dari ne suka amfana da tallafin daga mazabun yankin guda goma
Wasu daga matan da suka amfana sun mika godiya da alkawarin kula da awakin har su hayayyafa.
