Home » Shin Wai Dole Ne Sai An Banka Wa Nijeriya Wuta Domin Cika Burin Tinubu?

Shin Wai Dole Ne Sai An Banka Wa Nijeriya Wuta Domin Cika Burin Tinubu?

Editor
A+A-
Reset

Farfesa Yusuf Usman

Yan Nijeriya za su iya tuna cewa a ranar Kirsimeti ta shekarar da ta gabata ta 2025 ce Amurka ta kawo wasu hare-hare ta sama wanda ya saɓa wa mutunci, da kima, dayancin Nijeriya.

Shugaba Trump ya sanar da harin ta sama a dandalinsa na soshiyal midiya da saƙo kamar haka a takaice “A wannan dare ƙarkashin umarnina a matsayina na Babban Kwamandan Askarawan Amurka, an kaddamar da gagarumin mummunan hari kan gungun Yan Taadda na ISIS a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, da suke ta kai wa musamman Kiristoci da ba su ji ba, ba su gani ba hari suna kashe su, lamarin da aka kwashe shekaru da dama, kai za a iya cewa ɗaruruwan shekaru ba a taɓa ganin irinsa ba.

Ba inda bamabaman na Amurka suka auka illa cikin wata gona da babu kowa a cikinta, da ke kauyen Jabo a ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato. Jabo ƙauyene na manoma da Allah Ya huwace musu kasar noma, ba daji ko wata mabuya ta miyagun mutane; ba ta da wani tarihi na ISIS, ko yan fashin daji koyan ta`adda. Hankalin su kwance babu wani labari da aka taɓa ji na matsalar tsaro a yankin da har za a samu dalilin kai musu wani hari ta sama.

Sakkwato ko Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba su da wani tarihi na yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi. Gaskiyar batu ma shi ne wadanda tashe-tashen hankula suka fi shafa a yankin a shekaru aru-aru su ne Musulmi da `yan fashin daji suke ta kashewa.

Abin da tunanin Trump yake nunawa shi ne Trump dai cike yake da rudu da karairayi da aka kitsa da ke ƙarewa ga zurfafa matsalolinmu na ƙabilanci da na addini. A nasa tunanin matsalolin tsaro na Nijeriya, tushen su akida ta addini, kuma kasancewa kan gaba wajen kare bukatun Kiristoci kawai, bai tsaya ga jahilci da kuma hadarin gaske ba, har ila yau yana nuna gazawa wajen tunani. Wannan ganganci da rashin hankali na harin na soja da Trump ya sa a yi, tono gidan rina da kuma jefa rayuwar yan Nijeriya da dama da ba su ji ba, ba su gani ba ne cikin haɗari, kamar yadda aka samu ƙaruwar kai hare-hare da satar jamaa a al`umomi da ba su da kariya.

Manufar wannan muƙala ita ce yin wasu jerin tambayoyi da suka jibanci juna, duk da na san ba zan samu wata gamsasshiyar amsa ba. Me ya sa sai a ranar Kirsimeti ne Donald Trump zai sa a kai harin, kuma me ya sa sai tsakiyar Babbar Daular Musulunci ta Sakkwato? Yana iƙirarin cewa manufar kai harin ita ce kare Kiristoci, sai dai akwai buƙatar kallon wannan dalili nasa da idon basira.

Shin an sanar da Majasar Dokoki ta Kasa ko Hukumomin Soja kafin kai wannan hari? Me ya sa gwamnatin tarayya ba ta ce uffan a kai ba? Me ya sa sai Ministan Harkokin Waje, maimakon Ministan Tsaro ne zai kasance kan gaba wajen fitar da bayanai ga jama`a? Kuma me ya sa magoya bayan IPOB ne ake ta gani suna iza wutar?

Idan an waiwayi baya za a ga cewa a ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 2025 a Makurdi ta jihar Binuwai aka soma kitsa batun ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi, bayan kisan-kiyashi da aka yi a kauyen Yelwata, a lokacin da Shugaba Tinubu ya je jajanta musu – abin da ba a taba yi wa sauran al`umomin Arewa da irin wannan ya auku gare su ba.

Waɗanda suka yi wa Shugaban Ƙasa rakiya su ne Babban Hafsan Hafsoshin Hafsoshi (CDS) Jana CG Musa, da Shugaban `Yan Sandan Nijeriya (IGP) Kayode Egbetokun, da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) George Akume da kuma Babban Mai Ba Da Shawara Ɓangaren Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu.

A lokacin da Shugaban Ƙasa ya mayar da wannan asarar rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, ta zama fagen siyasa da kuma mayar da batun ya koma na addini, na san cewa akwai abin da ake kitsawa. A bainar jamaa ya kira tare da neman Babban Hafsan Hafsoshi da Babban ShugabanYan Sanda, wadanda dukkan su Kiristoci ne, da su miƙe tsaye, tare da ba su umarnin a kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Jawabin da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya yi a wajen Babban Taro na 80 na Majalisar Ɗinkin Duniya a New York a ranar 25 ga watan Satumba na 2025, inda ya bayyana goyon bayan Nijeriya ga samar da yan tacciyyar ƙasa ta Falasdinawa, bai yi wa Israila da magoya bayanta Amurkawa daɗi ba.

An kunna wutar ƙaryar cewa ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi a Nijeriya ne a lokacin da wasu ƙungiyoyin kiristoci masu waazi na Amurka tare da wasuyan jam`iyyar Republican a Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka bazama kafofin yada labaru suna ta yada wannan labari na ƙarya gadan-gadan.

Wannan gangamin da farfaganda ta karya suka sa Gwamnatin Tinubu yin abin da ake cewa motsi ya fi laɓewa tare da mayar da martani amma mai rauni. Babban Mai Ba Da Shawara Bangaren Tsaro, Nuhu Ribadu ya jagoranci wani ayari da ya hada da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, da Karamin Ministan Harkokin Wajen Ƙasar nan, da Babban Hafsan Hafsoshi, da Babban Shugaban Lamuran Leƙen-Asiri na Soja (CDI), da Babban Shugaban `Yan Sandan Nijeriya suka tafi Amurka domin dakatar da bata sunan Nijeriya. Sun sadu da Pete Hegseth, Sakataren Yaƙi na Amurka, da Dan Majalisa Riley Moore, wanda shi ne ke yaɗa labarin ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi.

Ayarin wakilan ya sanya hannu a wata yarjejeniya da ake zargin Amurkawan ne suka tsara ta, da ke bayanin cewa idan Nijeriya bata cimma wasu sharudɗa ko bukatu, Trump zai dauki matakin soja kai tsaye. Har yanzu dai wadannan sharudda suna nan a matsayin sirri, kuma `Yan Majalisar Dokoki ta Tarayya, da muka zaɓa domin tambayar bangaren zartarwa, sun kasa tambayar bayanan da suka shafi taron.

Ɗan Majalisar Dokoki ta Amurka Riley Moore ya ziyarci Nijeriya a ranar 8 ga watan Disamba, na 2025 domin gano gaskiyar batu a kan tursasa wa Kiristoci, daga nan ya hau jirgi ya koma Washington, DC,

Ya kai wa Trump rahoto. Jihar Binuwai kawai ya ziyarta, ya juya domin taimaka wa Trump yanke shawara a kan daukar matakin soja.

Ban sani ba shin dariya zan yi, ko kuka ko fushi a lokacin da na karanta jaridar New York Times ta ranar 18 ga watan Disamba na shekarar 2025, da ta ba da rahoton cewa magoya bayan karairayin ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi a Majalisar Amurka da Majalisar Dattawa sun dogara ne kacokan a kan wani bincike mara makama ballantana tushe da wani maƙetaci dan ƙabilar Ibo mai sayar da sikundireba ya yi ta shafin matambayi ba ya bata na google/gugul, a zaune a ɗan ƙaramin shagonsa da ke kasuwar Anaca a Jihar Anambara, a matsayin daga wajen sa ne suka samo shaidar ana yi wa Kiristoci kisan-kare-dangi a Nijeriya.

Daga wannan bincike lalube nasa a gugul ne suka bai wa Shugaba Trump shawarar ya bada umurni Sojojin Amurka su kaima Nijeriya haru. Gaskiya waɗannan `yan majalisun dokoki na Amurka sun ba ni kunya, saboda suna da cikakkiyar masaniyar irin kayan aikin da suke da shi don gano gaskiya in har da gaske suke yi suna son sanin gaskiyar. Abin da ban takaici cewa ba gaskiyar ba ce a gaban su.

Babu wani ɓoye-ɓoye a fili yake cewa masu fafutukar neman ɓallewa na Biafra su ne ainihin masu wannan ƙulle-ƙullen da tura wadannan bayanai na karyar ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi ga duniya. Bayanin da ya sa Shugaba Trump ya amince da ƙaryar ana kai wa Kiristoci hari da kashe su a Nijeriya an gano cewa suna fitowa ne daga IPOB, wata ƙungiyar `yan aware ta Ibo.

Ƙungiyar IPOP ta daɗe tana yada bayanai na karya cewa ana yi wa Kiristoci kisan-ƙare-dangi a Nijeriya, ta amfani da rediyon su na Radio Biafra da kuma soshiyal midiya. Ta kuma ƙulla kawance da wasu `yan majalisun dokoki na Amurka, da coci-coci, da ƙungiyoyi masu zaman kansu na Kiristoci. Dabararsu ita ce raba kan ƙungiyoyi na kabilu da addinai da siyasa da ke Nijeriya ta hanyar da addini.

Manyan manufofi guda 3 na IPOB su ne:

  1. Ƙirkiro da Biafra: Bayan juyin mulkin soja na zubar da jini da hafsoshin soja yan ƙabilar Ibo suka yi a ranar 15 ga watan Janairu na 1966 da ya yi sanadiyyar kisan shugabannin siyasa da na soja, yawancin su ‘yan Arewa, an jefa Nijeriya cikin yaƙin basasa na tsawon wata 30 da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da raba miliyoyin jamaa da matsugunin su.

IPOB da magoya bayan ta, da yawancin su ko dai ba a haife su a lokacin ba, ko kuma sun yi ƙanƙanta su iya tuna abin tsoro da razanarwar da ke tattare da yaƙin na basasa, kuma manyan su, ba su yi masu karatun – ta-natsu ba, suke ganin a yanzu za su iya cimma wannan buri a lokaci na zama lafiya, ta hanyar ƙarya da sunan addini, abin da waɗanda suka gabace su, suka kasa cimma a fagen – daga.

  1. A Nijeriya, da yake zaɓen Shugaban Kasa na ci gaba da ƙaratowa, kungiyar IPOB da magoya bayanta sukan ƙaddamar da zage-zage, da sharri, da barazanar tashin hankali ko ɓallewa ga `yan arewa, da ƙoƙarin tursasa wa masu su zaɓi ɗan takarar Ibo ko goyon bayan a mayar da dan takaran shugaban ƙasa ya zama ya fito ne daga Kudu-Maso-Gabas. Wata dabarar kuma ita ce karyar ana yi wa Kiristoci kisan-kare-dangi.
  2. Wata kuma yaudarar kan su da su masu yada karyar da ruruta ƙiyayya ke yi ita ce Shugaba Donald Trump zai ba su katin bisa na musamman na tafiya Amurka (special visa status) saboda kasancewarsu Kiristoci da ake tsana da zalunta kamar yadda ya yi wa fararen fata na Afirka ta Kudu.

Mene ne ɓoyayye a ciki da Kiristocin Arewacin Nijeriya, da ya kamata su sani fiye da waɗannan masu yaɗa ƙiyayya da ajandar ɓallewa ba za su farga ba? Gaskiyar ita ce wasu yan siyasa da ba su san ciwon kan su ba, za su yi amfani da su a farfagandar haddasa ƙiyayya ta IPOB da kuma neman kuriarsu a 2027, kamar yadda jam`iyya mai mulki ta yaudari Musulmin Arewa su zaɓi Musulmi-Musulmi a babban zaben da ya gabata na 2023. A yanzu dai an gane cewa damfara ce.

Ta ya wata ƙungiya ta yan Nijeriya za ta bazama duniya tana yaɗa karya da kiran a kai wa ƙasarsu hari na soja, tambayar da mutum zai yi kenan? Manufarsu ita ce, tsananin ƙiyayya ce ga Addinin Musulunci da kuma Musulmin da ke Arewacin Nijeriya, da ta musu katutu a cikin zuciya, ta sa suke waɗannan abubuwa. Tambayar da ke cikin zuciyar kowa da ke Arewa ita ce, ta ya duk wani mutum mai hankali da ke yankin zai yarda ko amince wa ko zaɓar wanda ya ƙi jininsa, da addininsa, da aladunsa da yankin?

Biyo bayan hare-hare ta sama da Amurka ta kawo Nijeriya ta sama, Ministan Harkokin Waje na Nijeriya Yusuf Tuggar, ya bayyana a kafofin labaru. Ya ce Nijeriya ce ta ba Amurka bayanan tsaro kafin harin, kuma sau biyu yana magana da Sakataren Harkokin Waje na Amurka Rubio na tsawon minti 19, da kuma tsawon minti 5 kafin ƙaddamar da harin. Ya ce dukkan su sun amince cewa sanarwar da za ta biyo bayan harin, ta kasance ta nuna cewa ba an kai harin ne saboda addini ba.

Fitowa kafofin yaɗa labaru da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya yi, ya haifar da ƙarin tambayoyi fiye da amsoshin:

  1. Da gaske ne Nijeriya ta bai wa Amurkawa bayanan na sirri domin kai harin da ya nuna an kai shi ne a filin gona da babu kowa a ciki a ƙauyen Jabo Sakkwato?
  2. Wane ne ya tsara kiran? Nijeriya ko Amurka?
  3. Shin bai kamata kiran ya zama tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Tinubu ba ne kamar yadda tsari ya tanadar?
  4. Izini guda ɗaya ko fiye da ɗaya Nijeriya taba Amurka domin kawo harin ko kuma akwai ƙarin wasu hare-haren nan gaba, kamar yadda shi Trump da kansa ya ce akwai ƙarin wasu nan gaba?

`Yan Nijeriya suna sa ran su ji tare da ƙarin tabbaci daga Shugaban su kuma Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, ko a ƙalla Ministan su na Tsaro, amma ba daga Ministan Harkokin Waje ba. Shirun da suka yi ya haifar da wasu tambayoyi kamar haka;

  1. An sanar da Hukumomin Soja kafin Amurka takai wannan hari, kuma sun amince da shi? Da alama dai Janar CG Musa, Ministan Tsaro bai san da batun harin ba, domin kuwa an gan shi yana ta tiƙa rawa a wajen bikin cikarsa shekara 58 a duniya a ranar kai harin. Makon da ya biyo baya an kuma ganin shi a wajen wani biki da addua ta coci don isarsa gida a lokacin dayan Nijeriya ke jira su ji tsokacinsa.
  2. Akwai wani abu da harin ta sama na Amurka ya yi da Sojojin Saman Nijeriya suka kasa yi?
  3. Trump ya fito fili ya bayyana cewa hare-harensa ta sama da ya kai tsakiyar Daular Musulunci ta Usumaniyya Sakkwato ya yi ne domin ceto Kiristoci da yake ƙauna. Me ya sa Ministan Tsaro da Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro waɗanda dukkan su Kiristoci ne ba su wakilci gwamnati wajen yi wa `yan Nijeriya bayani a kan wannan mataki na soja ba?
  4. Me ya sa gwamnati ta aika Ministan Harkokin Waje da na Labaru waɗanda dukkan su Musulmi ne, su yi magana a kan batu na soja?
  5. Naɗa Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro da aka yi a ranar biyu ga watan Disamba, na 2025, bayan an cire shi daga matsayin Babban Hafsan Hafsoshi a ranar 24 ga watan Oktoba na 2025, an yishi ne da nufin lallashin Kiristocin Arewa cewa Tinubu fa yana son ya lashe zaɓukan 2027 da kuma bin umarnin Trump.

Idan har gaskiya ne zargin da ake yi cewa ana yi wa Kiristoci Kisan-ƙare-dangi, yaushe ne aka yi haka? An yi ne a lokacin da Kiristoci suke shugabantar kusan duka hukumomin tsaro na Nijeriya? Janar Musa Kirista ya shugabanci hukumomin tsaro na soja a matsayin CDS, da Shugaban Hafsoshin Soja, da CDI, da IGP, da Babban Shugaban Hukumar DSS dukkansu Kiristoci ne.

Da matuƙar ban takaici a dinga ganin shirye-shirye a wasu manyan tashoshin talabijin na Nijeriya sun shiga sahun masu yaɗa labarun ƙarya na ana yi wa Kiristoci Kisan-ƙare-dangi, tare da yin watsi da ƙaidojin aikin jarida. Waɗannan shirye-shirye sun zama dandalin takaici inda masu gabatar da su, da kuma baƙin da suka gayyatowa ke yin bayanai masu tunzura jamaa, da raayoyi na ƙarya da ke karfafa abin da suka sa a gaba, su daƙile baƙin da suke da bambanci raayi da na su.

Shugaba Tinubu bai iya tafiyar da bambance-bambancen da ke tsakanin yan Nijeriya ba. Don son zuciya ya ƙara yawan giɓin bambanci na ƙabila da na addini domin cimma burinsa na cin zabe, ta yadda da farko ya fitar da tikitin tsayawa takara ta Musulmi da Musulmi a 2023, yanzu kuma ya mayar da hankali ga kuriun Kiristocin Arewa a 2027 ta hanyar nuna yana tausayin su bisa karairayin ana musu kisan-ƙare-dangi kamar yadda ya nuna wajen naɗin Shugaban Hukumar Zaɓe, mutumin da a shekaru 6 baya, ya yi rubuta ra`ayinsa da ke mara baya ga wadannan karairaki.

Tinubu ya lalata duka manufofinsa na alheri da ya hau mulki da su ta hanyar gudanar da mulki na ƙabilanci, da son kai, da ba a taɓa ganin irin sa ba, da tsarin da bai damu da batun tsaro da kula da jin dadin yan ƙasa ba. Gazawarsa wajen kare dukayan ƙasa ba tare da laakari da addinin su, ya cusa ƙin juna a tsakaninyan Nijeriya tare da bai wa gwamnatinsa da ta gaza ikon yin sukuwa da zamiya yadda ta ga dama.

Da alamu cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ko dai yana sane, ko bai sani ba ya ɗora Nijeriya a turbar wargajewa. A idon duniya kuwa ya mika wa Amurka da Faransa `yancinmu, kuma ya bari a jefa Nijeriya cikin yaƙi na kaikace da Amurka ke yi da ƙasar Sin.

Dole ne mu duka mu ba da ta mu gudunmawar wajen hana Nijeriya aukawa cikin ruɗani da a yanzu muke gani a Sudan, da Somaliya da Libiya. In kunne ya ji, jiki ya tsira.

Usman Yusuf Farfesa ne Ɓangaren Nazarin Cututtuka da Suka Shafi Lafiyar Jini da Dashen Ɓargo

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.