Home » Ya Kamata Gwamnan Kano Ya Duba Hukuncin HISBAH na Haramta Sana’ar Downloading

Ya Kamata Gwamnan Kano Ya Duba Hukuncin HISBAH na Haramta Sana’ar Downloading

Editor
A+A-
Reset

Ahmed Ilallah

Lokaci na shudewa, zamani na chanjawa, kowane zamani ya na zuwa irin nasa nishadin, yanayin tattalin arzikin sa, tayadda jama’a ke yin sana’oin su domin su rayu.

Kamar yadda zamani ya shafe sana’oin sayarwa da yin recording na kasset da CD, sabo da ci gaban technology. Babu yadda za a ce kawai, saboda matsala guda ko fiye, wanda wannan kuskuren a kan iya gyara ta, ta jawo rushe wani bangare na tattalin arziki, shi wannan sana’ar downloading nan sana’ace da ke samawa dubban mutane aiyukan yi, har wa yau dubban mutane sun dogara domin rayuwar su.

Sana’ar downloading da a ke tura fina-finai, wakoki, karatu, wa’azi da sauran su, ba kawai nishadantarwa bane, har harkar karuwar ilimi da sauraran wa’azi take bawa gudunmawa.

To Kodak masu wannan sana’ar suna aikata wani laifi, na downloading abin da ya sabawa dokar HISBA, kyautuwa yayi hukumar tayi aiki tukuru wajen gyarawa masu sana’ar kurakuren su.

Sannan kuma ba duk mai downloading ne ke tura waka ko fina-fina bai ba, wasu ma kawai karatu suke ta’ammali da shi.

Ya kamata gwamnatin Jahar Kano tayi duba wannan dakatawar da a ka yiwa masu downloading domin masalahar al’umma, da kuma yanayin rashin aikin yi da illar hakan a tsakakkanin matasa, wanda sune sukafi yawa a cikin wannan sana’ar.

Wannan doka ta HISBA kan iya con karo ta tanade-tanadan Hukumar Censorship ta Jahar Kano.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.