Home » Ma’aikatar Lafiya ta Shawarci Al’umma da Su Bai wa Lafiyarsu Muhimmanci a Yayin Azumi

Ma’aikatar Lafiya ta Shawarci Al’umma da Su Bai wa Lafiyarsu Muhimmanci a Yayin Azumi

Isiyaku Ahmed
3 views
A+A-
Reset

Nabilusi Abubakar K/Na’isa

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta yi kira ga daukacin al’umma da su kula da lafiyarsu tare da bin shawarwarin likitoci domin kauce wa matsalolin da ka iya tasowa yayin azumi.

A cikin wata sanarwa da Mai magana da yawon ma’aikatar ya fitar, ya taya al’ummar Musulmi murnar sake samun damar shaida watan Ramadan, tare da jaddada muhimmancin kiyaye lafiya a wannan lokaci na ibada.

Ma’aikatar ta
ja hankalin masu fama da cututtuka masu tsanani ko na dindindin kamar su ciwon suga (diabetes), gyambon ciki (ulcer), hawan jini da sauran makamantansu da su tuntubi kwararrun likitoci kafin su fara azumi.

Hakan zai taimaka wajen sanin yadda za su daidaita shan magunguna da bin tsarin abinci cikin aminci.

Haka kuma, an shawarci al’umma da su guji yawan zirga-zirga a cikin tsananin zafin rana domin kauce wa bushewar ruwan jiki da sauran matsalolin da zafi kan haifar.

Domin tabbatar da lafiyayyen azumi, Ma’aikatar na shawartar jama’a da su tabbatar suna.


Sha isasshen ruwa tsakanin lokacin buda baki da sahur da Cin abinci mai gina jiki domin lafiyar su. Dakuma, bin umarnin likita wajen shan magunguna.

Gaggauta zuwa asibiti idan an ji jiri, kasala mai tsanani ko wata alama da ba ta saba ba.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar al’umma, tare da yi wa daukacin jama’ar jihar fatan samun Ramadan mai albarka, lafiya da kwanciyar hankali.


WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.