Home » Shin, Wa Zai Faɗa Wa Shugaban Ƙasa Gaskiya?

Shin, Wa Zai Faɗa Wa Shugaban Ƙasa Gaskiya?

Isiyaku Ahmed
A+A-
Reset

Farfesa Usman Yusuf

Bayan kallon wani faifan bidiyo da aka nuna Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Kaduna, ranar Asabar, 24 ga Oktoba, na kasa daurewa ba tare da yi masa addu’a ba.

Bayyanarsa da yadda yake motsi sun tayar mun da hankali matuƙa, musamman yadda tafiyarsa ta kasance kamar ba ta da daidaito kai ka ce yana koyon tatatata tafiya ta nuna ne, alamun rauni da kuma rawar da ake gani haɗe da karkarwa a hannunsa na hagu.

A matsayina na likita mai fiye da shekaru arba’in na ƙwarewa a fannin aikin likitanci, ina cikin damuwa game da lafiyar Shugaban Ƙasa da kuma ko zai iya jure wahalhalun yaƙin neman zaɓe ko ba zai iya ba, da ɗawainiyar gudanar da nauyin mulkin Nijeriya, ko kuma ci gaba da wani wa’adin mulki na shekara huɗu da yake nema.

Nijeriya, da rayukan ’yan ƙasa fiye da miliyan 200, sun fi burin kowane mutum ko wata ƙungiyar masu muradi girma ba kaɗan ba. Ya kamata Shugaba Tinubu da iyalinsa su yi la’akari sosai da ko janyewa daga takarar sake zaɓensa za ta fi zama alheri a gare shi da kuma ƙasar nan. Yana buƙatar samun kulawar likitoci da ta dace, da hutawa.

  1. Yaƙin Neman Zaɓe: Farko Mai Baƙin Ciki?

Yawan mutanen da suka halarci bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na zaɓen 2027 a Kaduna ya bayyana a matsayin abin takaici. Duk da irin dukiyar da jam’iyyar ta tanada, filin wasa da aka ce yana ɗaukar mutane 5,000 ya bayyana babu cunkoson jama’a sosai, duk da kasancewar gwamnoni da dama, da ministoci, da masu ba da shawara kan harkokin siyasa da ƙungiyoyin magoya baya.

Idan wannan ƙarancin halartar jama’a yana nuna rashin gamsuwar jama’a a faɗin ƙasar, to Shugaba Tinubu da tawagarsa ta yaƙin neman zaɓe suna da dalilin damuwa ƙwarai. Babu wata dabara ta sarrafa labarin siyasa ko ƙawata shi da za ta iya maye gurbin amincewar jama’a.

  1. Matasanmu: Fushin da Ba Za a Yi Watsi da Shi Ba

A yayin ziyarce-ziyarce da tarurruka da matasa da na yi kwanan nan a jihohin Arewa maso Yamma guda shida, wato Kaduna, da Katsina, da Kano, da Jigawa, da Sakkwato da Kebbi, na ci karo da matuƙar rashin gamsuwa da jam’iyyar da ke mulki. Ihun da suke yi na cewa “Ba ma yi” ya isar da saƙo bayyananne na rashin gamsuwa.

A Kaduna, wani matashi ya shaida mun cewa duk lokacin da ya ji ina magana, yana samun kwarin gwiwar cewa ba duk mutanen birane ne suka yanke hulɗa da wahalhalun talakawan Nijeriya ba.

Na tunatar da waɗannan matasa cewa suna da ikon tsara makomarsu, amma dole ne su yi amfani da wannan iko cikin hikima da lumana. Kada su koma zagin mutane, ko tashin hankali, ko amfani da duwatsu, ko adduna ko bindigogi.

Dole ne su tsara kansu, su wayar da kan jama’a, su shiga harkokin siyasa, sannan su yi amfani da katunan zaɓensu wajen bayyana ra’ayinsu a rumfunan zaɓe. Su kaɗa ƙuri’unsu, su raka akwatunan zaɓe, sannan su tabbatar an ƙirga/ƙidaya ƙuri’unsu.

  1. Maguɗin Zaɓe: Shin Za a Ƙirga Ƙuri’un Jama’a?

Akwai ra’ayoyin da ke nuna cewa an riga an yanke shawarar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027, kuma za a ayyana Shugaban Ƙasa Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da la’akari da abin da masu zaɓe suke so ba.

Masu yaɗa wannan ra’ayi suna dogara ne da irin dimbin kuɗaɗen da jam’iyya mai mulki take da su na gudanar da yaƙin neman zaɓe, da kuma tunanin cewa talauci, da yunwa da rashin tsaro za su iya hana mutane fitowa zaɓe a yankunan da ake ganin suna adawa da gwamnati.

Waɗannan zarge-zarge ne masu girma da tsanani da suke buƙatar bincike da tantancewa. Ingancin zaɓen zai dogara ne da ’yancin kai da gaskiyar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da yadda hukumomin tsaro za su gudanar da aikinsu, da kuma ikon ’yan Najeriya na kaɗa ƙuri’a cikin ’yanci tare da tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri’unsu.

Duk wanda yake tunanin lalata tsarin zaɓe ya sake tunani. Duk wani yunƙuri na hana ’yan Nijeriya damar amfani da haƙƙinsu na zaɓe dole ne a yaƙe shi ta hanyoyin da doka da kundin tsarin mulki suka tanada.

Tawayen jama’a da suka faru a ƙasashen Nepal da Bangladesh sun tuna mana da haɗurran da ke iya tasowa idan ’yan ƙasa suka yi imanin cewa ba a la’akari da ra’ayoyinsu.

Zaɓe mai inganci, da mutunta zaɓin jama’a da kuma warware koke-koken siyasa cikin lumana su ne kawai hanyoyin kare ƙasa daga rikice-rikice.

  1. Kudu maso Yamma: Ina Tsoffin Masu Sukar Gwamnati Suke?

Shiru da wasu fitattun masu sukar gwamnati daga yankin siyasar Kudu maso Yamma suka yi, duk da zarge-zargen nuna fifiko ga ƙabila, da cin hanci da rashawa, da hauhawar basussuka, da talauci da yaɗuwar rashin tsaro, abu ne da ya kamata a lura da shi.

A lokacin mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wani tsohon shugaban ƙasa, wanda ya lashe kyautar Nobel, fitattun shugabannin addinin kirista, ƙungiyoyin ƙabilu, masu fafutukar kare haƙƙin bil’Adama da wasu sassan kafafen yaɗa labarai — duk daga Kudu maso Yamma — sun kasance a sahun gaba wajen ƙalubalantar manufofin gwamnati.

Wasu daga cikinsu sun yi gargaɗi kan abin da suka kira “Fulanisantar da Musuluntar da Najeriya”.

Shin batutuwan da a da suke ɗauka a matsayin muhimman abubuwa ga haɗin kan ƙasa sun daina zama masu muhimmanci ne? Ko kuwa ƙabilanci, biyayya ga siyasa da kusanci da masu mulki sun sauya ma’aunin da suke amfani da shi wajen tantance abubuwa ne?

Ba za a riƙa kare ƙa’idoji bisa zaɓin wanda yake kan kujerar Shugaban Ƙasa ba. Dole ne a riƙa buƙatar masu mulki su ba da amsa kan ayyukansu a kowane lokaci, ba tare da la’akari da ƙabila, ko addini ko jam’iyyar siyasa ba.

  1. Tikitin Musulmi da Musulmi: Shin Yana Rarraba Kan Ƙasa?

A ranar 11 ga Agusta, 2022, bayan sanarwar da jam’iyyar APC ta yi game da tikitinta na shugaban ƙasa da mataimakinsa, na wallafa wata makala mai taken: “Tikitin Musulmi da Musulmi na APC Ba Don Allah Ba Ne, Kuma Ba Don Ƙasa Ba Ne.”

Na ba da hujjar cewa tikitin da ya ƙunshi ’yan takara masu addini ɗaya bai nuna yadda ya kamata haɗin kan ƙasa, da adalci da kuma yanayin Nijeriya a matsayin ƙasa mai mabiya addinai daban-daban ba.

Wannan tikiti ya taimaka wajen buɗe hanyar da Tinubu ya bi har ya zama Shugaban Ƙasa, amma na yi imanin cewa illolinsa ga haɗin kan ƙasa, musamman a Arewa, sun kasance masu lahani.

Maimakon ƙarfafa haɗin kai da fahimtar cewa ’yan ƙasa abu ɗaya ne, wannan tsarin ya taimaka wajen ƙara rashin jituwa da rarrabuwar kai tsakanin Musulmi da Kiristoci musamman a Arewa.

Da dama daga cikin ’yan Nijeriya da suka goyi bayan tikitin bisa dalilan addini na iya kasancewa suna tambayar kansu ko abin da suke fata ya tabbata.

Sauƙaƙa batutuwan addini zuwa wasu ƙananan bayanai marasa zurfi yana sa a kasa fahimtar sarƙaƙiyar harkokin mulki da kuma irin abubuwan da al’ummomi daban-daban suke fuskanta.

Yanzu Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa sun sake dawowa neman ƙuri’un Musulmi, waɗanda da yawa daga cikinsu suke jin cewa gwamnati ta yi watsi da su. Haɗin kai bisa addini ba zai iya maida gurbin rashin cika burin jama’a ba.

  1. Rashin Kyakkyawan Gudanar da Bambance-Bambance da Siyasar Addini da Ƙabila

Bambancin da ke tsakanin al’ummomin Njjeriya ya kamata ya zama tushen ƙarfi, ba makamin amfani da shi wajen neman goyon bayan siyasa ba.

Sai dai akwai ƙarin damuwa cewa ana amfani da bambance-bambancen ƙabila da addini domin cimma muradun siyasa, musamman a Arewa.

Irin waɗannan ayyuka suna ƙara rashin yarda tsakanin al’ummomin da ya kamata su haɗa kai wajen fuskantar manyan matsalolin da suke barazana ga rayuwarsu da makomarsu a yankin Arewa.

Dole ne shugabancin ƙasa ya haɗa kan ’yan ƙasa bisa muradu na bai ɗaya, da daidaiton haƙƙoƙi, da adalci da manufa ta bai ɗaya ga ƙasa.

  1. Malaman Addinin Musulunci: Ina Matsayin Ƙungiyar Musulmi Wajen Faɗin Gaskiya?

Malaman addinin Musulunci suna da babban nauyi na kasancewa lamirin ɗabi’a na al’ummar Musulmi. Aikin su shi ne yi wa al’ummar Musulmi jagora, da tabbatar da adalci da kuma faɗa wa masu mulki gaskiya komai ɗacinta, ba tare da la’akari da illar da hakan zai iya haifarwa a siyasance ba.

Sai dai kash, yayin da ’yan Nijeriya suke fuskantar yunwa, da talauci, da rashin tsaro da cin hanci da rashawa, da yawa daga cikin shugabannin addini suna bayyana kamar ba sa son ƙalubalantar masu iko.

Shin mun mayar da Musulunci zuwa tarihin da ake bayar da labarinsa da kuma bukukuwan da ake gudanarwa a fili, maimakon rayuwa da koyarwarsa ta hanyar adalci, da tausayi, da gaskiya da kula da waɗanda ake zalunta?

Ba za a taƙaita jagorancin addini da yin addu’o’i a tarukan siyasa ko nuna goyon baya ga masu mulki kaɗai ba.

Ya kamata jagorancin addini ya haɗa da yin magana a kan rashin adalci da kuma watsi da ’yan ƙasa masu rauni da buƙatar taimako.

Dole ne malaman addinin Musulunci su yi zurfin tunani game da nauyin da aka ɗora musu da kuma irin tarihin da suke son bari a bayansu.

Dukkanmu za a yi mana hisabi a gaban Allah.

  1. Shugabannin Addinin Kirista

Shugabannin addinin Kirista ma suna da muhimmiyar rawa wajen kare mutuncin ɗan Adam, da inganta adalci da kuma sanya jami’an gwamnati su ba da amsa kan ayyukansu.

Bishop-bishop na Katolika da sauran shugabannin Kiristoci sun yi magana da babbar murya a lokuta daban-daban a kan harkokin mulki, da cin hanci da rashawa, da rashin tsaro da rashin adalci a cikin al’umma.

Bai kamata a sa ran shugabannin addini su goyi bayan wata jam’iyyar siyasa ba. Nauyin da ke kansu shi ne kiyaye ƙa’idojin ɗabi’a na addininsu, da kare masu rauni, da inganta zaman lafiya da jituwa, da kuma dagewa cewa jami’an gwamnati su sauke nauyin da ke kansu.

Nijeriya tana buƙatar shugabancin ɗabi’a mai ƙarfin hali, da bin ƙa’ida da kuma daidaito daga dukkan al’ummomin addini.

  1. ’Yan Siyasa: Bikin Cin Moriyar Arziki a Teburin Yaƙin Neman Zaɓe?

‘Yan siyasar Nijeriya suna fuskantar matsalar rashin amincewar jama’a.

Da yawa daga cikin ’yan siyasar da ke kewaye da Shugaba Tinubu suna bayyana kamar sun fi damuwa da samun muƙamai a cikin tsarin gudanar da yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki, maimakon magance wahalhalun da talakawan Nijeriya suke fuskanta.

Wasu daga cikin su ba za su iya tabbatar da cewa iyalan su za su zaɓe su ba, amma suna gabatar da kansu a matsayin waɗanda ba za a iya tafiyar da siyasa ba tare da su ba. Ba sa son rasa damar da albarkatun kuɗi na yaƙin neman zaɓe za su iya samarwa.

Amincewa da ɗan takara a bainar jama’a da kuma bayyana biyayya ga shugaba ba su zama hujjar samun goyon bayan jama’a na gaskiya ba.

Haka kuma, raba kuɗi, da abinci da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen jan hankalin masu zaɓe ba zai iya rama gazawar shugabanci ba.

Ainihin gwajin shugabanci shi ne ko ’yan ƙasa suna da tsaro, da ayyukan yi, da abinci, da ilimi, da kiwon lafiya da kuma kwarin gwiwar cewa makomarsu za ta kasance mai kyau.

’Yan siyasar da ba za su iya nuna ingantaccen sauyi a rayuwar jama’a ba, bai kamata su ɗauka cewa kusanci da masu mulki yana tabbatar musu da samun ƙuri’un jama’a ba.

  1. Tsaro: Bala’in da Bai Kamata Mu Saba Da Shi Ba

Rashin tsaro a Nijeriya yana ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka fi buƙatar kulawa cikin gaggawa, musamman a Arewa.

Al’ummomi suna ci gaba da fuskantar kisan mutane, da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, da hare-hare da kashe jami’an tsaro, da kuma hare-haren ’yan bindiga, da Boko Haram, da ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Manoma a yankuna da dama na Arewa ba sa iya zuwa gonakin su. An raba iyalai da muhallan su, yara sun rasa damar samun ilimi, sannan ana tilasta wa al’ummomi biyan kuɗin fansa domin a saki ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su.

Kada mu taɓa bari kisan ’yan Nijeriya marasa laifi ya zama wani abu da muka saba da shi.

Ba za a taɓa samun zaman lafiya a kowace ƙasa da take da irin waɗannan matsaloli da suka addabi Nijeriya ba: cin hanci da rashawa, da mummunan shugabanci, da yunwar da manufofin gwamnati suka haifar, matsanancin talauci, ɗimbin yaran da ba sa zuwa makaranta, da rashin aikin yi ga matasa, da hauhawar jarabar amfani da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, da yaɗuwar ƙananan makamai da bindigogi, da kuma guba ta rashin yarda da ƙiyayya bisa ƙabila da addini da ’yan siyasa masu son kai suke haddasawa.

Dole ne a auna aikin Gwamnatin Tarayya bisa ikonta na kare rayuka, da tabbatar da tsaron al’umma, da dawo da damar zuwa gonaki da makarantu, da ƙarfafa hukumomin tsaro da kuma gurfanar da masu aikata laifuka a gaban shari’a.

Yaudarar siyasa ba zai maye gurbin sakamako na zahiri da za a iya aunawa ba.

  1. Sarkin Katsina: Mai Martaba Ya Faɗi Gaskiya da Hikima

Akwai wata magana da ta dace a riƙa maimaitawa: “Idan gwamnati ta gaza, ina manyan dattawan ƙasa masu hangen nesa suke?”

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi kakkausar suka ga tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari da Gwamna Dikko Umaru Radda, a lokacin ziyarar da suka kai fadarsa.

Sarkin ya bayyana cewa manoma a ƙananan hukumomi 12 na Jihar Katsina ba sa iya zuwa gonakinsu saboda ayyukan ’yan bindiga, yayin da makarantu da dama a yankunan da abin ya shafa suke ci gaba da kasancewa a rufe.

Ya kalubalanci tawagar kan ayyukan shugaban ’yan bindiga Bello Turji, inda ya ce:

“Turji yana cikin daji mai nisan kilomita 100 daga nan. Ku je ku kamo shi, sannan ku dawo ku yi yaƙin neman zaɓe.”

Ya kuma jaddada irin dimbin kuɗaɗen fansa da haraji da ‘yan bondigs ke tilasta wa ’yan ƙasa biya.

Da yake kwatanta taken gwamnatin nan na “Sabunta Fata” (Renewed Hope) da abin da jama’a suke fuskanta a zahiri, ya lura cewa mutane da dama suna fuskantar abin da ya kira “sabunta yunwa” (renewed hunger).

Ya gargaɗi ’yan siyasa da kada su dogara da raba shinkafa da kuɗi domin samun ƙuri’u. Ya tunatar da su cewa mutane za su karɓi irin waɗannan kyaututtuka saboda larura, duk da haka su zaɓi wasu ’yan takara.

Ya kuma tunatar da tawagar cewa shugabanni za su yi wa Allah bayani kan alkawuran da suka gaza cikawa.

Saƙon da Mai Martaba Sarkin Katsina ya isar ya bayyana babban tazarar da ke tsakanin kalaman yaƙin neman zaɓe da ainihin rayuwar jama’a.

Abin da mutane suke buƙata shi ne tsaro, da abinci, da makarantu masu aiki, da damar zuwa gonaki, da ayyukan yi da ’yancin rayuwa ba tare da tsoro ba.

Waɗannan matsaloli suna buƙatar amsoshi masu inganci da za a iya tabbatarwa, tare da ɗaukar matakin gaggawa.

  1. Gwamnatoci Goma Sha Huɗu, Tambaya Ɗaya Mai Tayar da Hankali

Alhamdulillahi, na rayu tsawon lokacin da ya ba ni damar sanin gwamnatocin Nijeriya guda goma sha huɗu, tun daga gwamnatin Janar Yakubu Gowon, wanda ya mulki ƙasar daga 1966 zuwa 1975, har zuwa gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu ta yanzu, wadda ta fara a 2023.

A tsawon waɗannan gwamnatoci, na shaida hanyoyi daban-daban na tafiyar da mulki da kuma kawo ci gaba.

A ra’ayina, rashin taka-tsantsan, da yin abubuwa ba tare da jin tsoron hukunci ba, da kuma alamun rashin tausayi wajen gudanar da harkokin gwamnati a ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Tinubu, abubuwa ne masu tayar da hankali matuƙa.

Na yi gargaɗi game da wannan a wata makalata dana rubuta ranar 1 ga Fabrairu, 2026, mai taken:

“Shin Sai Nijeriya Ta Ƙone ne Saboda Burin Tinubu?”

Damuwata har yanzu ita ce, kada burin siyasa ya taɓa zama abin da aka fifita a kan walwala, tsaro da makomar Nijeriya da ’yan ƙasarta.

Kammalawa: Shin, Wa Zai Faɗa Wa Shugaban Ƙasa Gaskiya?

Nijeriya tana a wani muhimmin lokaci a tarihinta. Rashin tsaro, da yunwa, da talauci, da tsananin tsadar rayuwa da hauhawar bashin gwamnati, da zarge-zargen cin hanci da rashawa da nuna fifiko ga wasu ƙabilu, da kuma yaɗuwar rashin gamsuwar jama’a, duk suna buƙatar shugabanci na gaskiya da cibiyoyin gwamnati masu ɗaukar alhakin ayyukansu.

Shugaban Ƙasa yana buƙatar mutanen da ke kewaye da shi waɗanda za su faɗa masa gaskiya, ko da kuwa gaskiyar ba ta masa daɗi.

Yana buƙatar masu ba shi shawara waɗanda za su fifita ƙasa a kan muradunsu na kansu; shugabannin addini waɗanda za su fifita adalci a kan biyayya ga ’yan siyasa; ’yan siyasa waɗanda suka fahimci cewa riƙe muƙamin gwamnati amanar jama’a ce; da kuma ’yan ƙasa waɗanda za su nemi a riƙa yi wa masu mulki hisabi cikin lumana.

Damuwar da ake nunawa game da lafiyar Shugaban Ƙasa Tinubu ya kamata a magance ta ta hanyar binciken likitanci na ƙwararru da kuma yin la’akari na gaskiya game da ikonsa na sauke nauyin da ke tattare da muƙaminsa.

Idan manufofin gwamnatinsa sun gaza samar da alheri ga ’yan ƙasa, dole ne a amince da gazawar kuma a gyara ta. Idan amincewar jama’a ta ragu, dole ne a sake gina ta ta hanyar ayyukan zahiri da za a iya gani.

Zaɓen 2027 dole ne ya kasance na ’yanci, da adalci, da gaskiya da sahihanci. Dole ne a bai wa ’yan Nijeriya damar zaɓen shugabannin su ba tare da tsoratarwa, ko maguɗi ko hana su amfani da haƙƙinsu na zaɓe ba.

Duk wani sauyin shugabanci dole ne ya gudanar dashi ta hanyoyin da kundin tsarin mulki da tsarin dimokuraɗiyya suka tanada.

Da alamu harkokin siyasar ƙasa sun fara motsawa a ƙarƙashin ƙafafun jam’iyya mai mulki, amma hukunci na ƙarshe yana hannun al’ummar Nijeriya.

Tambayar da har yanzu take nan ita ce: Shin, Wa zai faɗa wa Shugaban Ƙasa gaskiya?

Game da marubucin: Farfesa Yusuf ƙwararre ne a fannin cututtukan jini da kansa da kuma dashen ɓargo.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.