Home » Madobi Ta Raba Kayan Makaranta Ga Ɗaliban Firamare 8,900 a Mazabu 12

Madobi Ta Raba Kayan Makaranta Ga Ɗaliban Firamare 8,900 a Mazabu 12

Editor
A+A-
Reset

Hassan Mukhtar Abubakar

Shugaban Karamar Hukumar Madobi, Alhaji Suleiman Danazumi, ya bayyana cewa za a raba kayan makaranta ga ɗaliban firamare guda dubu takwas da ɗari tara (8,900) a mazabu goma sha biyu (12) da ke cikin ƙaramar hukumar, bisa sahalewar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da shirin rabon kayan makarantar a Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Madobi.

Alhaji Suleiman Danazumi ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na inganta harkokin ilimi da kuma tallafa wa ɗalibai, musamman wajen samar musu da kayan karatu da za su taimaka musu wajen samun ilimi mai inganci.

Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa yadda yake ba harkar ilimi muhimmanci da kuma ƙoƙarinsa na samar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

Danazumi,ya jaddada aniyar gwamnatin ƙaramar hukumar Madobi na ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar wajen inganta harkokin ilimi da samar da yanayi mai kyau ga ɗalibai domin samun ilimi mai inganci.

A nasa jawabin, Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Madobi, Lawan Sani Gora, ya bayyana jin daɗinsa bisa wannan shiri na rabon kayan makaranta, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa wa iyaye da kuma ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen halartar makaranta da ƙwazo.

Alhaji Sani Gora ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano da shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan namijin ƙoƙari na tallafa wa ɓangaren ilimi, tare da jaddada cewa Sakatariyar Ilimi za ta tabbatar da an gudanar da rabon kayan cikin tsari da adalci domin kayan su isa ga ɗaliban da aka tanadar wa shirin.

Sign:Hassan Mukhtar Abubakar

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.