International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), Nigeria Chapter, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su zurfafa bincike kan abubuwan da ke iya haifar da cin hanci da rashawa a wasu hukumomin tsaro.
Daya daga cikin matsalolin da ake yawan korafi a kai shi ne rashin wadataccen albashi da walwalar jami’an tsaro, tare da rashin isassun kayan aiki.
A wasu lokuta, jami’i na iya samun mota ta aiki amma shi ne zai nemi kudin man fetur, gyara da service; haka nan akwai batun uniform da sauran bukatun aiki. Wannan yanayi na iya jefa jami’ai cikin matsin lamba da neman wasu hanyoyin samun kudaden gudanar da aiki.
Wani abin da ya fi tayar da hankali shi ne zargin tilasta wa wasu shugabannin matakai ko na jihohi samar da “return” ga wadanda suke sama da su.
A cikin bayanan da suka iso hannunmu, akwai zargin cewa a wata hukumar tsaro ana neman makudan kudade daga wasu shugabannin jihohi a kowane wata, daga N5m zuwa N10m, har ma da zargin wasu wurare suna kaiwa N30m.
IHRC-RFT ba ta ayyana wannan zargi a matsayin tabbataccen laifi ba. Muna kira ne da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar lamarin, gano hukumar da take da wannan dabi’a.
Ba za a iya samun ingantaccen tsaro ba idan jami’an da ake sa ran za su kare rayuka da dukiyoyin jama’a suna aiki cikin rashin kayan aiki da matsin lamba na kudi.
Muna kira ga gwamnati da hukumomin bincike da su dauki wannan batu da muhimmanci, domin idan ba a yaki cin hanci da rashawa ba, cin hanci da rashawa zai iya raunana tsarin tsaro da kansa.
