Home » Ku Kalli Masu Kashe Kwallon Kafar Nijeriya

Ku Kalli Masu Kashe Kwallon Kafar Nijeriya

Isiyaku Ahmed
5 views
A+A-
Reset

Abdulgafar Oladimeji

Miliyoyin masoya kwallon kafa a Nijeriya suna ci gaba da nuna damuwa kan abin da za a iya bayyana wa a matsayin raguwar da koma baya ga daraja da martabar wasan kwallon kafa a ƙasar nan wacce ta fi kowace ƙasa yawan masu sha’awar kwallo a fadin Afirka.

Kwanakin Nasararorin Kasarnan Sun shude, kwanakin da Nijeriya ta rike tutar alfaharin kwallon kafa na Afirka a fadin duniya.

Bayan kasancewar kwallo ita ce kadai abin da ke hade kan kabilu sama da 500 a Nijeriya, ita ce kuma alamar da ake gane kasar a duniya.

A shekarar 1980, Nijeriya ta lashe kofin kasashen Afirka wato (AFCON) karo na farko a tarihinta. Haka kuma ta kara daukaka sunanta bisa lashe gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 16 (U-16), wadda a wancan lokaci ake kira Kodak Cup, a kasar China.

Wannan nasara ta samu ne karkashin jagorancin Jagoran Yan wasa kyaftin Nduka Ugbade tare da abokan wasansa da kuma Mai horaswassu Sebastien Broderick.

A shekarar 1993 kuma,Koc Fanny Amun ya jagoranci ‘yan wasa irin su Kanu Nwankwo, Wilson Oruma da su Karigbe Ojigwe zuwa samun nasarori a matakin duniya.

Tun kafin haka, a shekarar 1989, tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 ta Nijeriya tayi wani abin al’ajabi da har yanzu ake kira keata Al’ada“Miracle”, inda ta kai wasan karshe na gasar FIFA U-20, duk da cewa daga karshe ta sha kashi a hannun Portugal mai dauke da taurarin Yan wasa irin su Luiz Figo.

Har zuwa shekarar 2000, Nijeriya na daga cikin kasashen da ke da karfin gaske a fagen kwallon kafa a duniya.

A shekarun 1994 da 1996, tituna a sassa daban-daban na Nijeriya sun cika da murnar da tsalle tsallen jama’a, biyo bayan lashe kofin Kasashen Afrika. na AFCON karo na biyu a kasar Tunisia,da samun halartar gasar cin kofin duniya a Amurka karo na farko, da kuma lashe lambar zinariya a wasan kwallon kafa na Gasar wasanniin guje -guje da tsalle tsalle ta Olympics a Atlanta.

Wadannan lokuta sun kasance Wani tarihi mai daraja da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da tunawa da shi.

Sai dai, ba zato ba tsammani, al’amura suka sauya, kuma kwallon kafar Nijeriya ta fara samun koma baya da rauni mai tsanani.

A yau, kwallon kafa wasan matasa a Nijeriya ba ta bunƙasa kamar yadda ake fata,, Har ma kasashe da ake kallon kanana irin su Nijar, Rwanda, Lesotho da Zimbabwe suna hana Nijeriya samun tikitin shiga manyan gasannin duniya.

Tambayar anan wadda da ke bakin masoya kwallo ita ce, Me ya faru da kwallon kafar Nijeriya?

Gwamnatin Taraya

Gazawar gwamnatin tarayya wajen kula da yadda ake tafiyar da harkokin kwallon kafa ta yi matuƙar illa ga cigaban wasan,
Rashin kulawa da sakaci da aka nuna cikin shekaru 15 da suka gabata ya ba da dama ga mutane marasa da basu cancanta ba shiga harkar, tare da aiwatar da abubuwan da ke cutar da kwallon kafa ba tare daan hukuntasu, ko Kuma daukar kwakkwaran mataki ba.

Wannan ya jawo rugujewar tsarin wasan da kuma jefa jama’a cikin damuwa.

Dokokin da ke tafiyar da harkokin kwallon kafa a Nijeriya sun tsufa kuma sun zama marasa amfani, da basu dace da zamanin ba,amma gwamnati ta kasa sabunta su, lamarin da ya hana ci gaba.

Haka kuma, gwamnati ta kasa sa ido kan yadda ake kashe kudaden da ake warewa domin bunkasa kwallon kafa,Wannan ya haifar da son zuciya, almundahana, da kuma tauye hakkin wasu.

Gwamnati ta kuma ta raina muhimmanci da amfani nada kwararru a mukaman wasanni, lamarin da ya jawo rashin kwarewa da rashin ingantaccen shugabanci a bangaren kwallon kafa.

Gwamnonin jihohi kuwa suna kallon mukaman wasanni a matsayin wata hanya ta bai wa ‘yan siyasa ko magoya bayansu lada, maimakon nada mutanen da suka cancanta.

‘Yan Majalisu

‘Yan majalisar dokoki na Nijeriya, a majalisar dattawa da ta wakilai, sun kasa gudanar da cikakken aikin sa ido kan harkokin kwallon kafa.
Rashin yin wannan aiki yadda ya kamata ya kara jefa bangaren cikin matsaloli.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikinsu suna daukar batun zabar ‘yan wasa da tafiye-tafiyen kasa da kasa a matsayin wani bangare na ayyukan mazabunsu, maimakon barin kwararru su gudanar da su.

Hukumar NFF

Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF), wadda ke kula da harkokin kwallon kafa a kasar, na fuskantar suka mai tsanani kan gazawarta wajen bunkasa wasan.

A shekarar 2015, hukumar FIFA ta bayyana damuwa kan yadda ake amfani da kudaden da aka bai wa NFF domin ci gaban kwallon kafa.
Sai dai a shekarar 2016, NFF ta mayar da martani, inda ta musanta wadannan zarge-zarge, tana mai cewa dukkan matakan da suka dauka sun bi ka’idojin kudi.

Sai dai duk da wannan bayani, ana ci gaba da ganin alamun tabarbarewa a fannoni da dama, ciki har da:
Rashin ingantaccen alkalanci
Karancin filayen wasa masu kyau
Raunin tsarin gasar lig
Gazawar kungiyoyin Nijeriya a gasannin Afrika naCAF,
Raguwar tagomashin tawagar kasa,
Rashin kwarin gwiwa a tsakanin ma’aikatan NFF.
Duk da dimbin kudaden da ake kashewa daga gwamnati, tallafi, da gudummawa, NFF har yanzu ba ta iya nuna sakamako mai kyau ko gamsarwa ba.

Haka kuma, ana zargin cewa tsarin daukar ma’aikata da Masu horaswa a hukumar ba ya bin cancanta, inda aka fi bai wa wasu dama saboda alaka ko son rai.

Hukumonin Yaku Da Cin Hanci

Duk da koke-koke da hujjoji kan yadda ake karkatar da kudaden da aka ware domin bunkasa kwallon kafa, hukumomin yaki da cin hanci ba su nuna cikakken kwarin gwiwa ba wajen gudanar da sahihin bincike.

Tsohon dan wasan kasa, Harrison Jalla, ya bukaci ICPC da EFCC su dauki matakin gaggawa domin binciken zarge-zargen rashawa a bangaren kwallon kafa.

Sai dai bincike ya nuna cewa ICPC ta ce ba ta samu hujjar da za ta kai ga gurfanar da wasu jami’an NFF gaban kotu ba, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu sun riga sun samu wanke kansu a kotu.

Sai dai bangaren masu shigar da kara sun yi watsi da wannan bayani, suna mai cewa batutuwan da ake magana a kai sun bambanta, kuma akwai bukatar ci gaba da bincike.

Kafofin Yada Labarai

Kafofin yada labaran wasanni a Nijeriya sun kauce daga rawar da ya kamata su taka na wayar da kan jama’a da rike gaskiya, zuwa kare muradun wasu mutane.

Sabuwar duniyar kafafen sada zumunta na zamani ta samar da masu tasiri (influencers) da ake amfani da su wajen kare masu daukar nauyinsu, maimakon su taimaka wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkar kwallon kafa.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.