Hukumar IHRC-RFT, Reshen Nijeriya, ta nuna matuƙar damuwa kan sabbin rahotannin tashin hankali a Jihar Niger, bayan harin da aka kai al’ummar Lumman-Ba’are da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, inda aka kashe dagacin garin, wasu daga cikin iyalansa, wanda ake zargin ko rikicin sarauta ne rikicin cikin Gida.
Abin da ya ƙara tayar da hankali shi ne rahotannin hare-haren ramuwar gayya da aka kai daga baya, a garin Wawa da gadar Ori wanda duka garin Fulani ne masu son zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Bassa, mai tazarar kilomita kusan sittin daga lumman-ba’are, inda aka kashe yara da tsofaffi daga al’ummar Fulani masu tarin yawa. Wanda yawancin su Yan gudun hijira ne na wani taaddanci da akayi musu, wanda suka samu mafaka a Garin Wawa.
Wannan yanayi na nuna barazanar rikicin da zai iya rikidewa zuwa karin hare-hare da ramuwar gayya, wanda zai jawo ƙarin asarar rayuka da dukiyoyi tare da rusa zaman lafiya tsakanin al’ummomi.
Muna kira kai tsaye ga Gwamnan Jihar Niger da hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, domin gano musabbabin hare-haren, tantance waɗanda ke da hannu, da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a kotu.
Muna jaddada cewa babu wani rikicin sarauta, ƙabilanci ko na al’umma da zai halatta kashe fararen hula. Baya halatta a rama kisan kai da wani kisan kai. Ɗaukar doka a hannu ba ya haifar da Ɗa mai ido, sai dai ƙarin matsaloli.
Muna buƙatar gwamnati ta gaggauta kare dukkan al’ummomin da ke cikin haɗari, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, taimaka wa waɗanda abin ya shafa, tare da samar da hanyar sasanci da sulhu tsakanin al’ummomin.
Gwamnati ba za ta jira sai an sake zubar da jini kafin ta ɗauki mataki ba. Kare rayukan al’umma wajibi ne, ba alfarma ba.
IHRC-RFT tana kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su guji ɗaukar fansa, yada jita-jita da kalaman tunzura jama’a. Adalci dole ne ya kasance bisa hujja, ba ƙabilanci ko ramuwar gayya ba.
Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan duk waɗanda suka rasa rayukansu, tare da kira da a tabbatar da adalci, dawo da zaman lafiya da mutunta haƙƙin rayuwar kowane ɗan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba.
