Home » Kano Online Media Chapel Ta yabawa Kamfanin Dala Food Nig Da Kamfanin POP Cola

Kano Online Media Chapel Ta yabawa Kamfanin Dala Food Nig Da Kamfanin POP Cola

Isiyaku Ahmed
9 views
A+A-
Reset

Kungiyar yan jaridun yanar Gizo ta ƙasa reshen jihar kano, Online Media Chapel ta yabawa kamfanin Dala Food Nig limited da Kamfanin POP Cola, bisa irin girmamawa da karramawar da kamfanunuwa suka yiwa kungiyar, a yayin taron ƙarawa mambobinta ilimi da sanin makamar aiki da yadda za’a koyi amfani da fasahar AI (One Day Capacity Building).

Shugaban kungiyar Abubakar Abdulkadir Dangambo ne ya bayyana haka, yayin gudanar da taron ranar Talata a ma aikatar sufuri ta jihar Kano.

Kamfanin Dala Food Nig limited sun turo ma’aikatan su, inda suka dama kunun tsamiya aka rabawa mahalarta taron cikin girmamawa, manyan baƙi da kananan kowa ya yaba da kunun.

Su kuma kamfanin POP Cola suma sun turo ma’aikatan su, inda suka kawo ruwa da lemuka kala-kala aka rabawa mahalarta wannan taro.

Dangambo ya kara yabawa kamfanunuwan duba da yadda aka tura musu buƙatar hakan a kurenren lokaci, kuma suka amince suka zo wajen taron da kayayyakin nasu.

A ƙarshe Abubakar Dangambo ya yi musu fatan alheri da kasuwa mai albarka cikin harkokin su.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.