Home Hausa Yadda Chanjin Yanayi Ya Shafi Noman Alkama Na Bana A Jigawa

Yadda Chanjin Yanayi Ya Shafi Noman Alkama Na Bana A Jigawa

by Editor
0 comment

Ahmed Ilallah

Duk da cewar Gwamnatin Jahar Jigawa da Gwamnatin Tarayya ta Mai da hankali da bayar gagarumar gudunmawa ga manoma a bana, don bunkasa noman Alkama a bana, sai ga shi a bana ba a samu amfanin da ya kamata a samu ba.

Gwamnati Tarayya tasa ran noma Alkama Tan 1,250,000 a bana.

Gwamnati ta bada gudunmawar kashi 50 ga manoma a kalla 250,000 domin aikata akalla Hecta 200,000 zuwa 250,000 a Jigawa.

Zan iya tuna wata magana ta karfin gwiwa da Gwamna Umar Namadi yayi, na karfafa gwiwa a kan Noman Alkama na Bana, a wata hira da yayi da Yan Jarida a fadar Shugaban Kasa a Abuja.

Kamar yadda Jaridar The Guidance ta 5/1/2024 ta rawaito, Malam yace “……. Jigawa ce ta farko a Noman Alkama a wannan kasa ……, ko a yanzu daga Hecta 120,000, jigawa kawai an bata Hecta 40,000, wannan zai nuna maka yadda mukayi fice a kan harkar noman Alkama.

A girbin Alkama na bana, akasarin manoma sun sha kashi a bana, dewa daga manoman sun yi asara, dewa sun shiga rigima da kamfanunuwa da mutanen da ke bada bashin Noma.

Wannan yanayi na Karamin kalubale bane a harkar cigaban Noma na zamani.

Yana da kyau a yi nazarin dalilan da yasanya a ka gaza samun amfanin da a ka zata za a samu.

Duk a bin da a ke bukata kama da takin zamani, iri da sauran kayan noma, kusan an samar da su.

Chanjin Yanayi (Climate Change) ya bada gagarumar gudunmawa a matsalar rashin samun amfani mai kyau na Alkama a kakar Bana.

Babban yanayi da Alkama take so, na fisabillahi, sune sanyi da hazo. Amma shin sati nawa a kayi a na sanyi da hazo a bana?

Tsananin zafi da rana Kan tauye Alkama. Shin yaya zafi ya kasance a lokacin da alkamar ke neman sanyi?

Bayan Noman Alkama ma, kadda hukumomi da manoma su ankara, shi kansa noman shinkafar rani kan iya samun wannan matsalar.

Kusan abubuwan da kan sanya Chanjin Yanayi ya kawo illa ga manoma, shine rashin masaniya ga manoma  na shi kansa matsalar Chanjin Yanayi da alakar sa da noma.

A bangaren gwamnati babu kyakkyawar alaka, hadaka da aiki tare tsakanin hukumomin da suke kula da Chanjin Yanayi da Ma’aikatar Noma.

Ya kamata hukumomi da al’ummah su maida hankali wajen yaki da Chanjin Yanayi da samar da dabaru ga manoma don kaucewa fadawa irin wannan matsala.

You may also like

©2024. Stallion Times Media Services Ltd. All Rights Reserved.