Home Hausa Kira Ga Mai Girma Gwamna: Za A Samu Karancin Manoman Shinkafar Ranin Bana A Jigawa

Kira Ga Mai Girma Gwamna: Za A Samu Karancin Manoman Shinkafar Ranin Bana A Jigawa

by Editor
0 comment

Daga Ahmed Ilallah

Jahar Jigawa tana daga cikin muhimmiyar jaha don bunkasa noman Shinkafa da korar yunwa  a Nijeriya.

Ba kawai gwamnatin Tarayya ba, hatta Bankin Raya Kasashen Africa da Bankin Duniya suna da buri a kan jihar Jigawa, duba da matsayinta na gaba a noma a Jigawa, musamman noman Shinkafa.

Kauracewar Manoma ba karamar cikas da koma baya zai kawo ba wajen kudirin Gwamnatin Jahar Jigawa na bunkasa noma.

Ita kanta kudirin Gwamnatin Tarayya na korar yunwa da bunkasa noma a wannan kasa, sai ya samu cikas.

Kamar yadda bayanai da dama suka bayyana a kan yanayin bugon Alkama ya kasance a bana, cewar a noman da a kayi na Alkama a bana a kwai kalubale masu yawa, duk da kasancewar Gwamnatin Malam Umar Namadi ta yi duk abin da ya kamata.

A noman alkamar bana Manoma dewa sun yi asara, wasu amfanin da suka girba yayi kasa matuka a kan lissafin abun da zasu samu.

A karamin binciken mu na sa kai, ya nuna cewar dewa a cikin manoman mu, musamman masu noman Shinkafar Rani da sauran noman cimaka irin su masara, wake da sauran su, sun kauracewa jeji. Dewa na ganin yanzu noma na neman fin karfin talaka.

A kwai dalilai da dama da suka sanya wannan manoma kauracewa gonakan su. Ga kadan  daga abin da muka gano.

Faduwa a Noman Alkamar Bana.

Faduwar da manoman suka yi a kakar alkamar bana, ya sanya musu tsoran komawa gona, kasancewar tattalin arzikin su, ya susuce a noman da suka yi.

Wasu a cikin su, sun fada komar bashi, ganin cewar kayan noman da suka yi ma bashi suka karba, dewa a yanzu ma, suna cikin rigimar warware wannan bashin.

Tsadar kayan noma da Talauchi ga Manoman

Akasarin manoman rani, in aka cire manoman da suke noma a HJRVDA, dukkan su sun dogara ne da amfani da Injinan Ban Ruwa don yin bayi.

Tsadar Man Fetur, wanda a yau ya kan kai N730 a wasu gidajan sayar da man a yankin Hadejia, da kuma fama da talauchin da Manoma suke, ya tilastawa manoma hakurin da yin noman a bana.

Tsoran Chanjin Yanayi (Climate Change) da Ambaliya

Daga cikin dalilan da suka bawa noman alkamar bana chikas, a kwai Chanjin Yanayi, a lokacin da amfanin ke bukatar tsananin sanyi, sai gashi ana fama da tsananin zafi.

Ya zama dole a samu hadakar aiki tsakanin hukumar muhalli da hukumar noma ta jaha domin kawo sauyi da sauki a kan harkar noma a Jigawa.

Sanarwa barazanar ambaliyar ruwa a bana, wannan dalili ya sanya tsoro a zukatan manoman, domin gudun tamka asara.

Wannan sune wasu daga cikin dalilan da ya sanya akasarin manoma tsorata a bana.

Amma fa dukkanin manoma sun gamsu da kudiri da kuma jajircewar Maigirma Gwamna a kan bunkasa  noma a Jigawa.

Kuma suna da yakinin cewar a gwamnati na da niyyar tallafawa noma a bana ma.

Kira ga Maigirma Gwamna a kan a duba wannan matsaloli da samawa dukkanin manoma tartibiyar hanya ta dogon zango don kawo karashen wannan matsaloli da kuma bunkasa noma gaba daya.

You may also like

©2024. Stallion Times Media Services Ltd. All Rights Reserved.