Home Hausa Yawaitar Yan Ta’adda Da Ta’addanci A Arewa Maso Yammaccin Nijeriya: Shin Ina Mafita?

Yawaitar Yan Ta’adda Da Ta’addanci A Arewa Maso Yammaccin Nijeriya: Shin Ina Mafita?

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Ahmed Ilallah

Shin lokaci baiyi ba da al’umar wannam yankin,  zasu farka ba daga dogon baccin da suke ciki ba, alhali gobara na cinye gidajen su ba kaukautawa ba?

Kai ko a yau dinnan, jaridar Blueprint ta rawaito an sace fasinjoji a kan hanyar Kankara ta jahar Katsina.

Ko a hantsin wanna rana Gidan Redion BBC ya ruwaito yadda Yan Ta’adda suka dawo cin zarafin al’ummah a garuruwan da a baya a ke ganin an sami saukin wannan bala’in, har ma da sace matayen aure.

A irin ruhotannin da a ka bayyana a tsakanin watan February zuwa watan March na wannan shekarar an sace mutane bila adadin, akasarin su da ga wannan yankin.

A 29 ga watan February, Yan Boko Haram sun sace wasu yan gudun hijira kimanin mutane 200 dewa daga ciki yara, a Karamar Hukumar  Ngala ta Jahar Barno.

A ranar 7 ga watan March Yan Ta’adda dauke da Makamai suka sace Yan Makaranta 287 a Makarantar Sakandare dake Garin Kuriga a Jahar Kaduna.

Har ila yau, a 18 a watan March na wannan shekarar nan Yan Ta’adda sun sake sace mutane 87 a Karamar Hukumar Kajuru ta Jahar Kaduna.

Sai gashi a jiya ma Yan ta’addar sun sake sace wasu mutane a Jahar Zamfara, jahar da ta yi kaurin suna da aikin ta’adancin yan fashin daji.

A yanzu za a iya cewa babu wani yanki a wannan kasa da yake cikin tsananin rashin tsaro da tashin hankalin yan bindiga kamar Yankin Arewa maso Yamma.

Babban abin takaicin shine, dukkanin Ministocin Tsaron nan daga wannan yankin suka fito. Duk da cewa Babban Ministan Tsaro, Mohammad Badaru Abubakar tsohon gwamman Jigawa, Jahar sa na daga cikin masu zaman lafiya, amma Karamin Ministan wanda shine tsohon gwamnan Zamfara, wanda Jahar sa tayi kaurin suna na rashin tsaro.

Ya kamata mutanen wannan yankin su yi dogon nazari na dalilin da ya sa Gwamnatin Tinubu ta bawa Tsoffin Gwamnonin wannan yankin guda biyu, Badaru Abubakar da Matawalle, tsohon gwamnan Zamfara, wanda dukkanin su ba a fannin tsaro suka kwarance ba.

Ya kamata ace, in har Shugaba Tinubu Tinubu zai kai kwararre a fannin kudi ya rike masa hukumar kudi ta kasa, to ya kawo kwararrai ya rike masa harkar tsaro, musamman a wanna lokacin da kasarnan take cikin barazanar tsaro, musamman wannan yankin namu na Arewa maso Yamma.

Wannan tsari na Shugaba Tinubu tamkar rashin damuwa ne da yadda wannan yankin ya ke ciki. Domin yankin da ya fito ba ya cikin wannan barazana.

Ya kamata mutanen Arewa muyi tunanin mafita a kan wannan masifa, kamar yadda mukayi sake ta’addanci ya daidaita Arewa maso Gabas, kadda kuma muyi baccci wannan ta’addancin ya sake rusa mana Arewa Maso Yamma.

Kuma a fakaice sauran yankunan suna kokarin samun yancin cin gashin kansu.

Ya zama tamkar wajibi da gwamnatin tarayya da gwamnonin mu na jahohi da ma shigabanni arewa su tashi don neman mafita ga wannan matsala.

You may also like

©2024. Stallion Times Media Services Ltd. All Rights Reserved.