Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yakai ziyarar jajantawa Yan kasuwar Kantin Jim kadan da dawowarsa daga ziyarar aiki da yaje Abuja.
Dubun dubatar Masoya da magoya baya ne sukayi cincirundo domin raka mai Martaba Sarkin kasuwar ta Kantin kwari.
Da yake jajantawa wadanda suka gamu da ibtila’in gobarar, Sakin Kano Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya mayar da asarar da akayi a kasuwar tareda addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.
Sarki Aminu ya kuma godewa Jami’an Hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Jami’an tsaro da Kungiyar Yan kasuwar da dai daikun al’uma bisa yadda suka bada dugunmawa wajan tabbatar da kashe gobarar.
Daga nan sai ya bukaci Yan kasuwa da sauran al’uma su cigaba dayin addu’oi domin kiyayewar afkuwar irin wannan ibtila’i tareda neman samun sassaucin al’amura na rayuwar yau da kullum.
Mai Martaba Sarkin na Kano yakai ziyarar aiki ne babban Birnin Tarayya Abuja tareda halartar wasu tarurruka, inda daga dawowar sa ne ya zarce domin yin jaje ga Yan kasuwar.