Ƙaramar Hukumar Sumaila ta gudanar da wani muhimmin taron jin ra’ayin al’umma domin tattara shawarwari da gudunmawar jama’a wajen tsara kasafin kudin shekarar 2026.
Taron ya gudana ne ranar Juma’a a fadar Hakimin Sumaila, inda ya haɗa shugabannin al’umma, kungiyoyin fararen hula, jami’an gwamnati, da sauran masu ruwa da tsaki.
A jawabin sa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Sumaila, Alhaji Farouk Abdu Sumaila, ya jaddada muhimmancin samar da damar da jama’a za su bada gudunmawa wajen tsara kasafin kudi. Ya ce wannan taro na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewa an yi la’akari da bukatun al’umma a cikin kasafin kudin shekarar 2026.
Anasa jawabin Daraktan Mulki na Ƙaramar Hukumar Sumaila, Alhaji Baffa Bello Gaya, ya yaba da irin gudunmawar mahalarta taron tare da jaddada muhimmancin gaskiya da rikon amana wajen gudanar da harkokin ƙaramar hukuma.
Wakilin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kano, Alhaji Bashir Hamza Baba, ya jinjinawa wannan shiri tare da bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da goyon baya wajen samar da tsarin mulki mai maida hankali kan jama’a.
Shugaban Sashen Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga , Alhaji Aminu Abdullahi, ya gabatar da bayanin fasaha game da tsarin kasafin kudi, inda ya yi kira ga mahalarta su bada shawarwari masu amfani don jagorantar ƙaramar hukuma wajen tsara kasafin kudin shekarar 2026.
Taron ya ƙare da zaman tattaunawa, inda mahalarta suka bayyana bukatunsu musamman a fannin lafiya, ilimi, gine-gine da walwalar matasa.
Sa hannu: Murtala Umar