Home » Rasuwar Yan Sanda A Kano Babban Rashi Ne Ga Nigeriya – Sarki Aminu Bayero

Rasuwar Yan Sanda A Kano Babban Rashi Ne Ga Nigeriya – Sarki Aminu Bayero

Editor

Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya bayyana rasuwar jami’an ‘yan sanda biyar da cewa wani babban Rashi ne, da kuma guda goma sha daya da suka samu raunuka sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a garin karfi dake kan titin Kano zuwa Zaria da a safiyar yau Talata.

Sarkin Aminu yace Rasuwar jami’an ‘yan sanda a bakin aikinsu wani babban lamari ne mai ban tausayi da ban tsoro, duba da irin gagarumar rawar da ‘yan sanda ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma musamman ma kasa baki daya. 

Yace Ayyukan da suke yi na cike da sadaukarwa ga al’umma wanda ya baiwa ‘yan kasa damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

 Sarki Aminu data nan said ya mika ta’aziyyar sa ga babban sufeton ‘yan sanda na Kasa, da Mataimakinsa Mai Kula da shiya ta daya dake Kano da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, da iyalai da ‘yan uwan ​wadanda suka rasu tareda yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yasa sun huta.

Ga wadanda suka jikkata kuwa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa daga raunukan da suka samu da kuma kiyayewar faruwar haka nan gaba.

Daga nan sai sarkin ya shawararci Jama’a musamman masu ababen hawa da masu amfani da ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kodayaushe kan manyan hanyoyi domin ci gaba da ceto rayukan ‘yan kasar da faduwar haddura.

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.