Iyalan wani Ma’aikacin Hukumar KAROTA, Yahaya Idris Ismail Barista wanda ya rasa ran sa tayi masa kisan gilla wanda ake zargin Direban wata motor daukar kaya yayi masa yayin da yake gudanar da aikin sa, sun yi kira ga Gwamnatin Jahar Kano da ta bi masa hakkin sa.
Al’amarin ya faru ne ranar laraba da daddare da misalin karfe 2.30am 24 ga Watan April, 2025 yayin da Yahaya Idris Barista da wasu abokan aikin sa, suke gudanar da aiki a titin Maiduguri road
dake Mariri anan birnin Kano.
Yahaya Idris Barista yayi kokarin tsayar da Direban motar Container, Koda Ya tsaya shigar Barista cikin motor ke da wuya Direban motar ya daga da shi, inda ake zargin Direban da dabawa Yahaya Barista wuka a ciki, al’amarin da yayi sanadiyar rasuwar Jami’n Karota, Yahaya Idris Barista.
Akan haka, iyalan Marigayi Yahaya Ismail Idris Barista suke rokon Mai Girma Gwamnan Jahar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf da kuma Hukumar KAROTA dasu bi kadin wannan kisan gilla da aka yiwa Dan Uwan su har sai an tabbatar da adalci tare da biyan diyyar ran Yahaya Barista.
Mai magana da yawun ‘Yan Uwan Yahaya Barista, Abdul Yakubu Muhammad shine yayi Kiran lokacin da ayarin suka kai ziyara ga Shugaban Hukumar KAROTA na Jahar Kano, Hon. Faisal Mahmud a ofishin sa.
Mal. Abdul Yakubu Muhammad Ya baiyana Marigayi Yahaya Idris Barista da cewar mutumin kirki ne wanda Ke gudanar da aiki bilhakki da gaskia.
Yace ya rasu ya bar Mata biyu da ‘ya’ya bakwai, don haka suke rokon Gwamnati da Hukumar KAROTA dasu duba wannan al’amarin.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Ya baiwa iyalan Marigayi Yahaya Ismail Idris Barista tabbacin cewar Hukumar zata tabbatar da adalci tare da gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Kuliya.
Hon. Faisal Mahmud daga nan yayiwa iyalan Marigayi Yahaya Ismail Idris Barista ta’azziyar wannan babban rashin, tare da alkawarin yin adalci.