Home » Jami’ar MyLes Dake Kasar Ghana Zata Karrama Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Da Digirin Girmamawa

Jami’ar MyLes Dake Kasar Ghana Zata Karrama Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Da Digirin Girmamawa

Editor
5 views
A+A-
Reset

Da yake bayani lokacin da Suka ziyarcrshi a fadar sa dake Gidan Sarki na Nassarawa Shugaban Jami’ar MyLes Isma’ila Sani Muhd Yace sunzo Nigeria ne domin Sanar da Sarkin wannan shiri da suke dashi na bashi Digirin Girmamawa.

Yace Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya cancanci Bashi Duk wata Lambar yabo da Girmamawa kasancewarsa Mai kishin al’umarsa da jajircewa da tafi da harkokin Mulki cikin adalci da kaunar al’umarsa da Kuma kaunar Zaman Lafiya.

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa tawagar da sukazo daga Jami’ar MyLes dake Kasar Ghana inda ya basu tabbacin Hadin Kai da goyon baya akan dukkan abunda Suka Sa a gaba.

Alhaji Aminu Ado Bayero Yace wannan Digirin Girmamawa da zasu bashi ba wai nasa ne kadai Yace na Masarautar Kano ne da alumar Jihar Kano baki Daya.

Sarkin ya bayyana irin Kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen guda biyu inda ya bukacesu dasu cigaba da kulla alakar cigaban harkokin ilimi da cigaban al’umar Najeriya da Kuma Ghana.

Daga nan Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya gode musu bisa wannan Ziyarar da Kuma Sanar dashi Shirin da Jami’ar takeyi na bashi Digirin Girmamawa.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.