Home » IHRC-RFT Najeriya Ta Goyi Bayan Tilasta Ma’aikatan Gwamnati Su Yi Amfani Da Makarantu Da Asibitocin Gwamnati

IHRC-RFT Najeriya Ta Goyi Bayan Tilasta Ma’aikatan Gwamnati Su Yi Amfani Da Makarantu Da Asibitocin Gwamnati

Editor
11 views
A+A-
Reset

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (IHRC-RFT), reshen Najeriya, na bayyana cikakken goyon bayan ta ga kudirin da Hon. Amobi, dan Majalisar Wakilai na Tarayya, ya gabatar, wanda ke neman tilasta wa dukkan ma’aikatan gwamnati su rika kai ‘ya’yansu makarantun gwamnati da kuma amfani da asibitocin gwamnati.

Wannan kudiri ya zo a kan kari, yana cike da adalci da kishin kasa. Shekaru da dama masu rike da mukaman gwamnati sun guji amfani da cibiyoyin gwamnati, lamarin da ya janyo koma baya, rashin inganci da rashin kula. Headmaster yana kai dansa makarantar kudi.

Likita na gwamnati yana gudun asibitin da yake aiki. Kwamishina, Minista suna tafiya kasashen waje domin neman lafiya. Yaya za a samu gyara a haka?


Kudirin Hon. Amobi Godwin Ogah, Dan Majalisa Mai Wakiltar Isuikwuato/Umunneochi Federal Constituency, Abia State, zai kawo daidaito da gaskiya a shugabanci. Idan jami’an gwamnati za su rika fuskantar matsalolin da talakawa ke fuskanta, to dole ne su gyara tsarin.

Wannan kudiri yana da alaka kai tsaye da Dokar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (UDHR):
Sashe na 25: Yancin samun lafiya da walwala.

Sashe na 26: Yancin samun ilimi kyauta da mai inganci.
Sashe na 21: Iko ya rataya a kan yardar jama’a.


IHRC-RFT na kira ga Majalisar Tarayya da su mara wa wannan kudiri baya domin a zartar da shi da gaggawa.

Najeriya na bukatar shugabanni masu shiga halin da talakawansu ke ciki.

Wannan mataki ne ga kasa mai adalci, hadin kai, da shugabanci na gaskiya.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.