Home » Hukumar Tace Fina-Finai Da Dab’i Ta Jihar Kano Ta Haramta Shirya Duk Wata Muhawara A Tsakanin Mawakan Addini

Hukumar Tace Fina-Finai Da Dab’i Ta Jihar Kano Ta Haramta Shirya Duk Wata Muhawara A Tsakanin Mawakan Addini

Editor
7 views
A+A-
Reset

A wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaka bangaren nishadi da na addini, Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya sanar da haramta duk wata nauyin muhawara daga mawakan addini a Jihar Kano, ba tare da izinin hukumar ba.

Wannan mataki ya biyo bayan wata muhawara da aka gudanar ba tare da izinin Hukumar ba tsakanin a Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, wacce hukumar ta bayyana ta a matsayin karya dokokin aikinta.

A yayin da yake kaddamar da kwamitin bincike wanda Mal. Isha Abdullahi, Daraktan Ayyuka na Musamman na hukumar zai jagoranta, Abba El-Mustapha ya bayar da wa’adin sa’o’i 24 ga mawakan da wanda suka jagoranci muhawarar tasu dasu bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.

Hukumar ta ce shirya irin wadannan muhawarori ba tare da sahalewar ta ba, ya keta dokar data kafa Hukumar, kuma ka iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka aikata hakan.

Abba El-Mustapha ya jaddada kudurin hukumarsa na ci gaba da kula da ayyukan mawaka da masu nishadantarwa a fadin jihar bisa doka da ka’ida. Ya kuma bukaci al’umma da su zauna lafiya, tare da bayar da hadin kai da kawo bayanai masu amfani domin tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’adu a jihar Kano.

(Abdullahi Sani Sulaiman)

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.