Home » Hukumar Shari’ah ta Kaddamar da Kwamatoci Domin Kawo Sauye-sauye Game da Cigaban Shari’a a Kano

Hukumar Shari’ah ta Kaddamar da Kwamatoci Domin Kawo Sauye-sauye Game da Cigaban Shari’a a Kano

Editor

Hukumar Shari’ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta Sheikh Malam Ali Dan Abba a yau Laraba ya jagorancin taron kaddamar da kamitocin da zasu dauki gabarar kawo sauyi a jihar Kano kan abin da ya shafi shari’ar Musulunci a jihar.

Dan Abba yayi maraba da manyan baki da hukumar ta gayyata kuma suka sami damar halartar zaman, manyan bakin da suka sami damar zuwa sun hada da Barr Mujiburrahman tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar (Ungoggo Branch Kano) kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi Musulmi ta Kano, Kano sai Baba Jibo Ibrahim mai magana da yawun kotuna ta jihar Kano sai wakilin shugaban gidajen gyaran hali da tarbiyya ta Kano sai wakilin kwamishinan yan sandan jahar Kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa da sauran mambobi na hukumar da manyan limamai.

Daga bisani Mal Dan Abba ya fadi makasudin wannan zama da samar da wadannan kwamiticin, wanda yace babban kalubalen da zamu fara sawa a gaba shine Sulhu kamar yadda shugaba sallahu Alaihi Wasallama yayi, sannan iyaye su saka ya’yan su a gaba wajen tsaida sallah, domin tsaida sallah shine babban jigon magancewar wadannan matsalolin da aka ciki a wannan jihar na shaye-shaye, kwacen waya, tabarbarewar tarbiyya raba da yawan cinkoso a gidajen gyaran hali, matsalolin aure da sauran matsaloli da ake fuskanta, in da ya tabbatar da faɗin Allah na cewar tsaida sallah na hana alfasha da sauran miyagun ayyuka.

“Allah ya karfafi Sulhu don haka muma zamu bada karfi akansa sosai da sosai”

Hakazalika yayi kira ga limamai da ladanai kan samun hadin kai idan dai Allah aka nufata, a karshe yayi fatan wadannan kwamitoci da aka samar na

-Da’awa

-Sulhu

-Tantance limamai da ladanai

-Bita da wayar da kan al’umma kan addini

Da fatan zasu kawo cigaba da hadin kan al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya kamar yadda mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake da fata a garesu.

A karshe yayi kira ga al’umma da Iyaye wajen bada hadin kai da goyon baya, idan wata matsala ce kafin kuke ko ina ku zo wannan hukuma da izinin Allah za a warware ko wacce irin matsala cikin sauki.

A nasa bangaren shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kano Barasta Mujiburrahman yace yaji dadin wannan gayyata da aka masa , kuma a saninsa tun daga lokacin Malam Ibrahim Shekarau ba a taba wata gwamnati a jihar nan da take kokarin habaka Shari’a ba sai wannan gwamnatin ba.

A baya mun yi irin wannan kokarin kafa kwamitin Sulhu a kananan hukumomi lokacin Malam Yahaya Farouk Chadi a lokacin ina sakatare na hukumar Hisba wanda a gaskiya anyi ayyukan sulhu kala kala wanda da Allah yasa an cigaba da wannan tsarin da ba haka muke ba yanzu da Kano ta wuce haka.

Yayi kuma kira ga gwamnan Kano kan inganta wannan hukuma ta Shari’a kamar yadda take a baya da sauran hukumomin addini na Kano.

Yayi kuma kira da Allah ya kawowa Kano zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Shima Baba Jibo Ibrahim ya yaba da wannan gayyatar da aka musu kuma ya tabbatar da cewar kwamatin sulhu da aka yi a cikin wadannan kwamiticin zai taimaka wa bangaren sharia a jihar gaya, kuma yayi alƙawarin cewar hukumar kotuna ta jihar Kano zata shigo cikin wannan kwamiti don tabbatar da wannan kwamiti wanda duk sulhun da aka yi hukumar kotuna zata buga tambari wanda ya zama doka kenan, maganin masu ganin cewar kwamitin bashi da hurumin tursasawa ko masu taurin kai.

Shima babban daraktan gidan Dr Sani Ashir ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah yadda Manyan baki suka amsa kiran nasu, kuma yayi kira ga yan kwamati da aka daura wa nauyin da su dubi Allah wajen gudanar da wannan aikin da Allah ya dora musu.

Shima gwani Hadi Kwamishina na ɗaya a hukumar ya godewa Allah ya kuma yi kira da al’ummar jihar Kano da su zamo ababen koyi da alfahari da su a ko ina haka zalika yayi kira ga malamai akan su guji nitso a cikin daudar duniya.

Karshe dai taro ya tashi cikin jin dadi da annashuwa

Da kuma rokon Allah ya tabbatar da nasarorin da ake nema.

Sunayen Yan kwamatin

Kwamatin sulhu

1. Ibrahim Inuwa                       (Limamin Ja’en)           Chairman

2. Ibrahim Lawan Karaye          DPRS                                 Vice Chairman

3. Aliyu Umar kibiya                   (Limamin Kibiya)          Member

4. Nana Aisha Muhammad       ACEO                                Member

5. Legal Adviser                                                                       Member

6. Abubakar I. Sulaiman              PEO                                Secretary

Kwamatin DA’AWA

1. Kabiru Na’ibi Karaye                Board Member           Chairman

2. Muhammad Abu Musa                      DIP           Vice Chairman

3. Nasiru Aliyu Harazimi             Board Member           Member

4. Abubakar Sani Madatai          Board Member           Member

5. Yawale Sulaiman Gulu             Board Member           Member

6. Zainab Sani Matori                                                           Member

7. Hamisu Murtala Gwarzo                                                Secretary

Kwamatin Tantance limamai da ladanai

1. Muh’d Mukhtar Mama Darma   Board Member Chairman

2. Yusha’u Abdullahi Bichi                  DIE              Vice Chairman

3. Muhammad Abu Musa                  DIP                          Member

4. Naziru Saminu Dorayi                     Board Member Member

5. Adamu Ibrahim                                                                Member

6. Adnan Nasir Koki                                                             Secretary

Kwamatin Bita da wayar da kan al’umma kan addini

1.Malam Abubabakar Sharif Bala     Board Member   Chairman

2. Sani Zarewa                                         DSD            Vice Chairman

3. Mahbub Sarki                                      DISA                         Member

4. Abdullahi Hassan                                                                 Member

5. Balarabe Aliyu                                                                       Member

6.Maryam Lawan                                                                     Member

7. Sani Musa Muhammad                                                      Secretary

You may also like

Leave a Comment

We strive to publish high-quality news content and report stories/news that inform, educate, entertain, and hold leaders and institutions accountable while upholding the ethics of journalism to safeguard trust in news reportage.

 

Content does not represent the official opinions of Stallion Times unless specifically indicated.

Edtior's Picks

Latest Articles

Copyright 2024. All Rights Reserved. Stallion Times Media Services Ltd.

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.