Home » Fiye da mutum 473 za su amfana da shirin koyan sana’a da bayar da jari a Tarauni

Fiye da mutum 473 za su amfana da shirin koyan sana’a da bayar da jari a Tarauni

Editor
10 views
A+A-
Reset

Daga Adamu iliyasu Hotoro

Fiye da mutum 473 ne maza da mata, daga sassan karamar hukumar Tarauni za su amfana da shirin koyon sana’o’i Dinkin jakunkuna, takalma,belt, makeups ,gyara da hada solar ,gyaran computer, dakuma gyaran wayar hannu.tare da basu tallafin jari,shirin wanda Babban Mai Ba Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Hukumar Karma, Abdullahi Sabo Abubakar, ya samar tare da hadin gwiwar Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Kano.

Yace shirin,an tsara shine don karfafa tattalin arzikin iyalai da rage yawan rashin aikin yi ga mata da matasa wanda shirinzai ba wa mahalarta damar koyon sana’o’in zamani da na gargajiya, da kuma samun horo kan yadda ake tafiyar da kasuwanci cikin nasara.

Haka kuma duk wanda aka koyawa sana’ar za a bashi jari bayan kammala karbar horon domin su fara fadada harkar sana’oinsu dakuma kware a cikinta.

Abdullahi Sabo Abubakar ya bayyana cewa wannan shiri yana daya daga cikin tsarin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen inganta rayuwar jama’a ta hanyar samar da ilimi, sana’a, da jari ga al’umma.

Mai bawa Gwamna shawara Abdullahi Sabo Abubakar yace wannan shirin koyar da sana’o’in hadin Gwaiwa ne da hukumar ilimin manya ta jihar Kano karkashin jagorancin shugabar hukumar, Dr Binta Abubakar, yace an zabi karamar hukumar Tarauni ne a matsayin daya daga cikin yankunan da za su fara amfana da shirin, tare da fatan wannan shirin zai zama ginshikin bunkasar tattalin arziki da ci gaban rayuwa ga Alummar yankin,inda ya godewa Gwamna Abba Kabir yusif bisa yadda yake basu damar gudanar da aikace aikace a kowanne lokaci.

A jawabinta Shugabar hukumar ilimin manya ta jihar Kano, Dr Abubakar yace wannan hukumar tana iyaka kokarinta wajan fadakar da Alumma musanman matasa da manyan wadanda basa zuwa makaranta da koyan sana’a domin horar dasu dakuma basu jari domin su zamo masu dogaro da kansu.

Shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure wanda yasami wanilcin mataimakin sa Khalid Ayuba ya godewa babban mai bawa Gwamna shawara kan Hukumar Karma Abdullahi Sabo Abubakar da shugabar hukumar ilimin manya ta jihar Kano, Dr Binta Abubakar bisa zabar karamar hukumar Tarauni domin zakulo matasa da mata domin basu horon sana’ai ,inda yabada tabbacin karamar hukumar Tarauni zatayi duk Mai yuwuwa wajan ganin matasan hadin Kai da goyen baya ayayin karbar horar dasu sana’oi’in.

Taron dai yasami hallartar mataimakin shugaban jamiyyar NNPP Muntari unguwa uku da daukacin masu bawa hallartar masu bawa shugaban karamar hukumar Tarauni shawara siyasa Aliyu sani Zaki, harkokin mata Binta sani.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.