Home » IHRC-RFT Nigeria Ta La’anci Yin Amfani Da Court Order Wajen Hana Adalci

IHRC-RFT Nigeria Ta La’anci Yin Amfani Da Court Order Wajen Hana Adalci

Editor
22 views
A+A-
Reset

Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Ƙasa da Ƙasa (IHRC-RFT), reshen Najeriya, mai matsayin shawara na musamman a gaban Majalisar Dinkin Duniya (ECOSOC Special Consultative Status), ta bayyana matsanancin damuwa kan yadda ake yawan yin amfani da Court order a matsayin hanyar kaucewa hukunci da kuma kaucewa bincike bayan aikata zalunci ko cin zarafi.

A halin yanzu a Najeriya, ya zama ruwan dare ganin wasu masu laifi suna gaggauta samun Court order domin hana jami’an tsaro cafke su ko gudanar da bincike a kansu. Wannan mummunan dabi’a ta lalata amincin tsarin shari’a, ta rage karfin hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu, sannan ta raunana amincewar jama’a ga doka da oda. Ma’aikatan tsaro da ma wasu alkalan kotuna su da kansu sun riga sun nuna rashin jin daɗinsu kan wannan matsala.

IHRC-RFT ta bayyana cewa ba ta yi kira da a haramta Court order gaba ɗaya ba. Abin da muke nema shi ne a tabbatar cewa ana bayar da irin waɗannan umarni bisa adalci, gaskiya da daidaito, ta yadda ba za a bar wani ya yi amfani da doka a matsayin makami na tauye wa ‘yan ƙasa hakkinsu ba.

Wannan cin zarafin tsarin shari’a ya sabawa yarjejeniyar kare hakkin ɗan adam ta duniya (Universal Declaration of Human Rights, UDHR), musamman:

Sashe na 7: “Duk mutane daidai suke a gaban doka, kuma suna da hakkin kariya daga wariya a kowane hali.”

Sashe na 8: “Kowane mutum yana da hakkin samun cikakkiyar kariya daga kotunan ƙasa masu iko idan aka take masa hakkin da kundin tsarin mulki ko doka ta ba shi.”

A matsayin wani mataki na fafutuka, IHRC-RFT ta riga ta aika wasiƙa zuwa ga Ministan Shari’a da Babban Mai Shari’a na Ƙasa (Chief Justice of Nigeria) domin su:

  1. Gudanar da bincike cikin gaggawa kan yadda ake amfani da umarnin kotu Court order ta hanyar da ba ta dace ba a faɗin ƙasar nan.
  2. Ƙarfafa matakan kariya domin tabbatar da cewa umarnin kotu ba sa zama kayan hana adalci.
  3. Haɗa kai da majalisar dokoki, bangaren zartarwa da hukumomin tsaro don kare mutuncin tsarin shari’ar Najeriya bisa ka’idojin kare hakkin ɗan adam na duniya.

IHRC-RFT ta jaddada cewa wajibi ne a ɗauki mataki cikin gaggawa domin dawo da amincewar jama’a ga tsarin shari’a na Najeriya da kuma tabbatar da cewa ƙasar ta ci gaba da mutunta haƙƙoƙin ɗan adam da martabar kowane ɗan ƙasa.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.