Home » Gaskiya Nagartar MutumKashi Na 1

Gaskiya Nagartar MutumKashi Na 1

Editor
70 views
A+A-
Reset

Farfesa Usman Yusuf


Shekaru uku da na yi a matsayina na Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa wato NHIS a takaice, ba karamar fafatawa na yi ba har a bainar jamaa da gungun masu bakin cin rashawa da ke zaune a Legas wadanda ake kira da Health Maintenance Organisations (HMOs) da ke (rarrabawa da kuma iyakance asibitocin da suke gudanar da tsarin inshorar lafiya da kuma kudaden su), da suka kwashe tsawon lokaci, suna rike da makogwaron tsarin samar da kudaden kula da lafiya na Nijeriya, da kuma masu kare su koyan kanzagin su da ke cikin gwamnati.

Suna gano cewa ba da ni ba zan lamunci wannan taasa ta rashawa da suka yi dumu-dumu a ciknta ba, sai suka kafa mun kahon zuka, suka biya wasu karnukan farautarsu kudi, suke ta rubuta wa dukkan hukumomin yaki da rashawa (EFCC da ICPC), da Majalisar Dokoki ta Tarayya (NASS), da Fadar Shugaban Kasa, koke-koke da korafe-korafe a kaina. Suka yi tsayin daka ba dare ba rana, suna ta biyan kudi ana ta mun gangamin batanci a kafofin watsa labaru, da tsara zaman sauraron jamaa a Majalisar Dokoki ta Kasa.

Saboda haka da na ga jami`an hukumar EFCC da ke yaki da laifuffuka na tattalin arziki suka zo wajena cikin kaya masu duhu, na san cewa zaune ba ta kare ba, ci gaba da fadana ne da rashawa a NHIS da kuma wani yunkuri da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi domin rufe bakina.

Wannan ya tuna mun da kalaman nan da ke cewa “going to the mattresses” a cikin littafin Mario Puzo “The Godfather,” da ke nufin in kwana da shirin fada, irin fadan da na yi a zamanin da nake hukumar NHIS.

A lokacin da fadan ya yi zafi, na samu damar da ba safai da kowa ke iya samu ba, na yi ido hudu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari daga ni sai shi, kuma wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma na kusa da shugaban kasa (na sakaya sunansa), shi ne ya tsara wannan ganawar tawa da shugaban kasa ba tare da na sani ba.

Zan iya tunawa na shaida wa Shugaban Kasa, “Mai Girma Shugaban Kasa, kai ka nada ni wannan matsayi ba tare da ka san ni ko wani ya yi kamun kafa a madadina ba; na yi alkawari ba ga kai ba, illa ga mahaliccinmu cewa zan rike hannu bibbiyu amanar da aka ba ni, na roki Allah Ya taimake ni.”

Na tunatar da shi cewa duk da yana da karfin ikon ya kore ni a duk lokacin da ya ga dama ba tare da sai ya fadi dalili ba, zan yi fada ba dan kadan ba, da duk wani yunkuri da wani zai yi na zubar mun da kimata da mutuncina, da ni na yi tsayin daka a rayuwata wajen nemar wa kaina.

Har ila yau na shaida masa cewa mai dakita da yayana suna ta matsa mun in ajiye mukamin saboda kamar yadda suka bayyana, babu amfanin yi wa kasar da ba a taba gode maka aiki. Na musu bayanin cewa zan ci gaba da wannan fada har sai na ga karshensa saboda ba na so in tafi in bar iyalaina da wata dauda ta rashawa.

Yana zaune ya yi shiru yana kallona, watakila yana ta tunanin daga wacce duniyar wannan mutumen yake ne wanda da alama bai san dawan garin ba, wato bai san yadda Nijeriya ta canza ba. Ya ce tabbas yadda abubuwa suka tabarbare kenan a Nijeriya. Ya shaida mun cewa duk abubuwan da nake gani za su ginu tare da karfafa mun halayyana zuwa gaba.

Gaskiyar ita ce babu wani asibiti a Nijeriya da ke aiki kamar yadda ya kamata, shi ya sa wadanda suke da hali ko kumbar susa suke zuwa kasashen waje idan ba su da lafiya. Sai dai yawancin `yan Nijeriya, musamman marasa karfi da ke cikinmu, ba su da irin wannan zabi.

Tsarin kula da lafiya na Nijeriya ya tabarbare, saboda yana fuskantar manya-manyan matsaloli, inda dakunan kwanciya da ke asibitoci tamkar abatuwa, su kuma kananan asibitoci matakin farko aka yi watsi da su. Masu bakin cin rashawa “wadanda ke tsakiya” da ake kira HMOs sun zama su ne uwa su ne makarbiya sun karbe tsarin samar da kudade bangaren lafiya, sai yadda suka dama za a sha, su kuwa majinyata da masu samar da ayyukan kula da lafiya sun koma abin tausayi.

Ma`aikatan lafiya suna ta yin tururuwa suna kaura zuwa kasashen ketare saboda halin da asibitocinmu suke ciki, ga rashin kayan aiki, ga karacin albashi.

Miliyoyin `yan Nijeriya sun dakatar da shan maganin da ake bukata su dinga sha saboda sun musu tsada, sun koma ga magunguna na gargajiya, da suka yi sanadiyyar karuwar matsalolin da suke da nasaba da cututtuka da kuma mace-mace.

Tunda daga lokacin da Shugaban Kasa Tinubu ya hau mulki, duka asibitocin da ke sassan kasar nan suke ta fama da karuwar yara marasa lafiya da ake ta kwantarwa sakamakon matsananciyar yunwa (Marasmus da Kwashiokor). Wannan alama ce ta tsanani da bakar yunwar da ake fama da ita a kasar nan saboda tsananin fatara, da farashin abubuwa da ya yi tashin gwauron zabi da karancin kudin.

Yayan talakawa suna ta mutuwa babu gaira babu dalili sakamakon cututtukan da za a iya rigakafin su, kamar su bakon-dauro, cututtuka na numfashi, da nimoniya, da sankarau, saboda rashin samun kula da lafiya kamar yadda ya kamata.

Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa NHIS, hukuma ce da ke iya yin tasirin gaske ga rayuwan miliyoyin `yan Nijeriya tare da rage dinbin matsalolin da suka yi wa bangaren lafiya na kasar nan dabaibayi.

Aikina a matsayina na Babban Shugaban Hukumar ta NHIS shi ne kara yawan `yan Nijeriya da suke da inshorar kula da lafiyarsu, ba batun sai suna da karfin aljihu ko babu, ko ba kudi a hannun su, za a duba lafiyarsu, tare da tafiya tare da kowa daga hukumar NHIS, da HMOs (wato wadanda suke a tsakiyar tsarin) da asibitoci kowa ya yi aikinsa tsakani da Allah: sannan abu mafi muhimmanci, shi ne zama mai rikon amanar da aka danka mun: dukiyar mutanenmu.

A lokacin da na kama aiki a watan Agusta na 2016, babu wani da ke cikin wannan ma’aikatar da zai iya fada manik takamemen yawan kudin da hukumar ta NHIS take da su, da kuma inda aka ajiye su. Saboda haka na dauki wani kamfanin binciken kudi mai zaman kansa, domin binciko mun dukkan asusun da NHIS take da su.

Tunda farko sai da Gwamnatin Tarayya ta bai wa dukkan ma`aikatu da hukukomin gwamnati (MDAs) umarnin su kwashe duka kudaden su, daga bakunan kasuwanci, zuwa asusun gwamnati, tilo (TSAs) da ke Babban Bakin Nijeriya (CBN) daga lokacin zuwa karshen watan Satumba na shekarar 2015. Wato kusan shekara guda kafin in kama aiki.

Kamfanin binciken kudin ya mika mun rahotonsa na karshe a watanni uku na karshen shekarar 2017. Rahoton ya nuna cewa bankunan kasuwanci guda goma sha uku, sun ki tura fiye da Naira Biliyan Dari da ke asusun hukumar NHIS, zuwa asusun na TSA, da ke Babban Bankin Nijeriya CBN, da ke nuna sun saba wa umarnin Gwamnatin Tarayya.

Manyan jamin gwamnati da na yi wa magana domin su taimake ni wajen kwato wadancan kudade da suka makale ciki har da shugaban hukumar gudanarwa ta hukumar na wancan lokaci, Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole; da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele; da Babban Shugaban Maaikatan Fadar Shugaban Kasa marigayi Abba Kyari da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya. Duk wannan haka tawa ba ta kai ga ruwa ba.

Bugu da kari, Babban Akanta na Kasa ya cire jimillar Naira Biliyan 10 (Naira Biliyan Biyar-Biyar cirewa biyu) daga asusun tilo na NHIS ba tare da ya tintibe ni ba ko neman izini daga wajena a matsayina na Babban Shugaban Hukumar ba. Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta ki yarda da duk wani kokarin da na yi na in ganta domin tattauna wadannan kudade da aka diba ba da izini ba. Sai ni kuma na kai karar ta wajen Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya BD Lawal, wanda ya kira ta, a gabana, ya ce mata, ta gan ni, amma ta ki har zuwa lokacin da ta fice ba shiri daga gwamnatin Shugaban Kasa Buhari.

A lokacin daya daga cikin lokuta biyu da aka dakatar da ni daga mukamina, wani mutum da ya gabatar da kansa a matsayin Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da laifuka da suka shafi tattalin arziki ya kira ni a waya. Ya nemi in je Hukumar. Ina isa aka kai ni wani dakin taro inda ya jera manyan jamian Hukumar. Ya shiga, bayan mun gaisa tare da gabatar da jamian, sai ya nemi in bai wa wadannan jamiai dukkan takardun bayanai da suke da nasaba da asusun NHIS, da HMOs, ko Bankuna, ko wata kungiya ko wani mutum suka rike ba bisa kaida ba. Daga nan ya fice daga dakin.

Kuma gaskiya kamar yadda ya nuna, hukumar EFCC a karkashinsa ta bi lamarin kuma ta soma kwato biliyoyi na kudaden NHIS daga hannun bankuna da HMOs ta bin abubuwan da suke cikin takardun da na bayar. A wata wasika zuwa ga Babban Sakataren Hukumar NHIS da ta zo bayana, da ta shafi kwato kashi na farko na kudin NHIS, Mukaddashin Shugaban shi da kansa ya sa wa wasikar hannu kuma ya ambaci suna na, da yabawa da kokarin da na yi wajen ganin an kwato kudaden hukumar.

Da a ce shugabannin hukumar EFCC na yanzu za su mayar da hankali su kamanta wancan jajircewa, da sun gano abubuwan da nake da su a takardun tarihi mai shekaru tara da ke Hukumar, a game da fadan da na yi da rashawa a zamanina a hukumar ta NHIS.

Ya kamata kwato kudaden NHIS (Da a yanzu ake kira da NHIA) da har yanzu suke bankuna ba bisa kaida ba, da HMOs suka kimshe su, domin a kwato a yi amfani da su wajen kyautata wayan Nijeriya, ya zama abubuwa na hamzari, da fifiko ga EFCC.

Muna Rokon Allah Ya Ci Gaba Da Yi Mana Jagora, Domin Yin Abin Da Ya Dace Da Kuma Kasancewa A Hanya Madaidaiciya.

Usman Farfesa ne Bangaren Nazarin Cututtukan Da Suka Shafi Jini, da Dashen Bargo.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.