Home » Yaduwar Yunwa Da Mace-Mace: Shirun Namu Fa Ya Yi Yawa, Wannan Ba Da’a Bace Ko Abun Aminta

Yaduwar Yunwa Da Mace-Mace: Shirun Namu Fa Ya Yi Yawa, Wannan Ba Da’a Bace Ko Abun Aminta

Isiyaku Ahmed
9 views
A+A-
Reset

Farfesa Usman Yusuf

A ranar Talata, 19 ga watan Agusta na 2025, `yan Nijeriya suka wayi gari da bakin labarin wani hari da mahara suka kai kauyen Gidan Mantau da ke yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina da ya yi sanadiyyar kisan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba su 55 da ke kauyen.

Wadannan yan taadda da aka ce sun kusan su 100 bisa babura, sun shiga kauyen ne da asubah, suka harbe bayin Allah su 30 da ke cikin gudanar da Sallar Asuba a wani masallaci, sannan suka ci gaba da yin harbi kan mai uwa da wabi a kauyen, inda suka kashe mutanen kauyen su fiye da 25.

An ce sun yi awon gaba da wasu mutanen kauyen da ba a iya tantance yawan su ba kamar shanu, aka tafi da su tungar yan taadda domin neman kudin fansa.

An ce sai da suka kafa shinge daban-daban domin hana shiga ko fita kauyen a lokacin da suke cin karen su babu babbaka har na tsawon awanni.

Ina yan sanda, da Sojoji, da jamian sintirin kare aluma da gwamnatin jihar ta tanadar, gwamnatin jiha da ta tarayya, wadanda ainihin babban aikin da ke kan su kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar shi ne kare rayuka da kyautata jin dadin alumar kasa?

Gwamna dai ya tafi kasashen waje domin hutun da ya saba zuwa na kowacce shekara, amma kuma, jira-jira, mataimakinsa, wanda shi ne mukaddashinsa, ya rubuta wata wasika zuwa ga Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Kasarnan, wanda ya tafi ziyarar aiki kasar Japan kuma bai mika ragamar mulki hannun Mataimakin Shugaban Kasa ba.

Saboda haka an bar mutanen Gidan Mantau da na jihar Katsina, da a yanzu suka zama fagen kashe-kashe da yan taadda ke ta yi, su yi ta kansu har sai Shugaban Kasa ya dawo.

Babu wata kumbiya-kumbiya: gwamnatin jiha da ta tarayya da duka hukumomin sun gaza bangaren kare mutanen Gidan Mantau da na jihar Katsina, inda a yanzu haka kananan hukumomi 24 cikin 34 na jihar (kashi 70 cikin kashi 100) ke karkashin hare-hare na yan fashin daji. Abin mamaki shi ne a yanzu haka an fi samun tsaro da kwanciyar hankali a jihar Barno fiye da jihar Katsina.

Lokaci ya yi da za a amince da hakan a daina kawo uzuri da karfafa gazawa kamar yadda ake ta maimaitawa.

Fiye da shekara shida ke nan ina ta nanata cewa akwai lokacin da sojoji suke da nasu takamemen aikin, ba ta amfani da soja ba ne za a iya yakar fashin daji kuma yakin da ake yi da ayyukan fashin daji, ba za a taba samun galaba ko nasara a fagen daga ba. dukkan matsaloli da suke da nasaba da matsalolin tsaro, lamari ne na gida, kuma dole a samu bakin zaren magance shi a gida wato cikin al`uma.

Shugabbani na siyasa, da soja, da na leken asiri da ke babban birni jiha da na tarayya sun ki su mayar da hankali wajen fahimtar wadannan matsaloli na cikin gida wato unguwanni ko yanki da kuma sanya masu ruwa da tsaki da suke wadannan wurare wajen lalubo hanyoyin magance matsalolin.

Shi ya sa manya-manyan tsare-tsare da ake yi daga Abuja, da ba a sanya mutane na wuraren da matsalolin suke addaba, suka kasa haifar da, da mai ido shekara da shekaru, kuma ba za su taba yin wani tasiri ba.

Gwamnatoci a dukkan matakai da hukumomin tsaro, sun ci gaba da yin kunnen-uwar-shegu da gaskiyar da ke cewa babu yadda za a yi a samu zaman lafiya da tsaro a Nijeriya ba tare da an magance batutuwa na zamantakewa da suke iza wutar matsalar tsaro kamar su fatara, da yunwa, da jahilci, da rashin aikin yi a tsakanin matasa, da rashawa da rashin shugabanci na gari mai adalci.

Lokaci ya yi da ya kamata a canza salo saboda lamura a kasa sai ci gaba da tabarbarewa suke yi kuma al`umar kasa sun yi matukar fushi.

Arewacin Nijeriya tana dab da aukawa cikin yanayi mafi muni na yunwa a wannan lokaci na rayuwarmu. Muddin ba a dauki matakan gaugawa cikin hanzari ba, zai iya kazancewa shigen irin wanda aka gani a matsananciyar yunwar da ta auku a Itofiya ta shekarar 1983 zuwa 1985, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da miliyan daya, karin wasu miliyoyin suka zama `yan gudun hijira, da kuma yunwa.

Abin takaici ma shi ne ba fa fari ko yaki ne ya haddasa wannan yunwar ba, illa tsare-tsare na tattalin arziki marasa kan gado da gwamnatin Shugaba Tinubu ta bullo da su tare da hadin bakin wasu gwamnoni da ba su san ciwon kan su ba, da ke jihohin da lamarin ya shafa.

A kasar da ba ruwanta da fari ko yaki a hukumance, tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatin Tinubu sun yi sanadiyyar miliyoyin `yan Nijeriya, yawancinsu mata da yara kwana da yunwa, da rashin tabbacin idan gari ya waye za su farka su samu na karin kumallo.

A asibitoci a dukkan sassan kasar nan, a yanzu yunwa ce ake fara dubawa a yara da manya, musamman mata majinyata, ko da kuwa me aka gano yake damun su.

Wannan mummunan lamari ya sa mutane da dama na Arewa ke da tunanin cewa da gangan gwamnatin Tinubu ke aiwatar da tsarin jefa `yan Arewa cikin yunwa, da danniya a siyasance da kuma tattalin arziki.

Kasashen duniya da hukumomi na agaji irin su Majalisar Dinkin Duniya, da Kwamitin Agaji na Duniya na Red Cross (ICRC), da Medecin Sans Frontieres /Doctors Without Frontiers (ICRS) wato likitoci da ke aiki a koina fadin duniya, da kuma na baya-bayan nan Vatican wato fadar Paparoma, su ma sun ce tabbas akwai bukatar daukar matakan gaugawa a kan wannan balai.

Kungiyar Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ankarar cewa a shekarar da ta gabata, ta lura da akwai karuwar kashi 200 na yawan majinyata da ake kwantarwa a asibitoci sanadiyyar yunwa ko rashin abinci mai gina jiki, kuma cibiyoyinta na ciyarwa da ke Arewacin Nijeriya sai ci gaba da cika makil suke yi da majinyatan, yawancinsu mata da yara, da ake warkar da su a kan katifu da aka shimfida a kasa.

A kwanan nan ne Jaridu guda biyu na Nijeriya suka wallafa wani rahoto daga kungiyar ta MSF a game da yadda yunwa ta yi katutu a Arewacin Nijeriya.

A bangon shafinta na farko ta ranar Juma`a, 25 ga watan Yuli na shekarar 2025, jaridar Daily Trust ta ba da rahoton cewa a kullum sai an kwantar da yara 400 da ke fama da tsananin rashin abinci mai gina jiki a cibiyar ciyarwa ta MSF da ke jihar Kabbi da ke Arewa maso yammacin Nijeriya.

Har ila yau jaridar Punch ta wannan rana, ta ba da rahoton cewa MSF ta tattara alkaluman yara 652 da suka rasu sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki a watanni 6 na farko na shekarar 2025 a jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin kasar nan.

A wani rahoton da jaridar Daily Trust ta buga a ranar 9 ga watan Yuli na shekarar 2025, kungiyar agaji ta Red Cross Society ta bayyana cewa a halin yanzu haka akwai yara su fiya da miliyan biyar da kusan rabi (5.4m) da ke fama da karancin abinci a jihohi 9 na Arewacin Nijeriya da matsalar tsaro ke ta addaba, wato jihar Barno, da ta Adamawa, da Yobe, da Sakkwato, da Katsina, da Zamfara, da Neja, da Binuwai da kuma jihar Kano.

Abin da gwamnatin Tinubu ta iya yi a kan hakan shi ne ta nuna cewa sam ba haka lamarin yake ba.

Maimakon ta ce tabbas akwai wannan gagarumar matsala, tare da daukar matakan gaugawa na ceton rai, da kauce wa wannan bala`I da ke kunno kai, ta tsaya kawai tana ta kare kanta, alhali ga zahiri ana gani baro-baro.

Shugaba Tinubu bai taba boye cewa kansa kawai ya sani ba, sai kuma burinsa, duk sauran to sai dai su biyo baya.

A lokacin da yan Nijeriya ke fama da tsananin talauci, da tsadar rayuwa, da yunwa, da tabarbarewar tsaro, inda daruruwan rayuwa ke salwanta a kullum a dukkan sassan kasar nan, ba abin da Shugaba Tinubu ya mayar da hankali a kai illa sake neman a zabe shi a shekarar 2027 maimakon ya yi kokarin kawo saukin wahalhalun da tsare-tsarensa ke ci gaba da jefayan kasa a ciki.

Kada ku bari wani ya yaudare ku, halin dimuwa da jamiyyar APC ta shiga ayan kwanakin nan da ya rage shekarar biyu a gudanar da babban zaben 2027, alama ce a fili ta kidimewa saboda sun hango faduwa a zaben.

Har ila yau wata dabara ce ta tilasta wa yan adawa su nuna kan su, domin Tinubu ya ji dadin rikirkita musu jamiyyunsu, da tura musu karnukan farauta na gwamnati, su bi su da bi-ta-da-kulli, da talauta su, ta amfani da kudaden da aka tara sakamakon cire tallafin mai. Sai dai mafi muhimmanci, shi ne kokarin kawar da hankalin `yan Nijeriya daga gazawar da mulkin Tinubu ya yi.

Babbar kasada ce ga dukkan wani dan siyasa ya yi wa kansa katanga da tushen zaben sa, sai dai wannan shi ne ainihin abin da Shugaba Tinubu ya aikata a cikin wannan shekaru biyu da yayi a mulki.

Yana ta fadan da babu riba da Arewa da jamaarta, yankin da shi ne ya ba shi kuria kashi 62 cikin kashi 100 na jimillar kuri`un da ya samu.

Ga wasu misalai nan don tabbatar da hakan;

Nada Yarbawa da yake ta yi ba kunya ba tsoro a gwamnatinsa da hukumomi na gwamnatin tarayya, ya saba wa sashe na 14(3) da na (4) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.

Sashe na 14(3) na cewa ya kamata mutanen da ke cikin gwamnatin tarayya da hukumominta su kasance akwai daidaito na wakilci da raba-daidai.

Wannan ke daukaka hadin kai, da tabbatar da biyayya, da hana wani yanki ko kabila danne wani yanki ko kabila.

Sashe na 14(4) ya fadada wannan tsari zuwa matakan jiha da na kananan hukumomi, tare da jaddada bukatar rungumar bambance-bambancen da ke nan da kuma daukaka tafiya tare da kowa ya san ana damawa da shi.

Sashe na 153 (1) ya kafa Hukumar Tabbatar Da Daidaito ta Gwamnatin Tarayya a matsayin hukuma domin tabbatar da an kiyaye da hakan kamar yadda aka zayyana a Sashe na 14.

An dora wa hukumar alhakin tabbatar da daidaito wajen rabon mukamai da ayyuka na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki daidai-wa-daida a sassa daban-daban na Nijeriya.

Kabilar Yarbawa ta Tinubu ita ke rike da iko da dukkan ginshikan tattalin arzikin Nijeriya ciki har da Maaikatar Kudi, da Babban Bankin Nijeriya, da mukamin Babban Akanta na Tarayya, da kamfanin mai na NNPCL, da hukumar tara kudaden shiga FIRS, da Hukumar Kwastam, da Hukumar Bunkasa Tattalin Arziki na Cikin Ruwa irin su (NPA, da NIMASA, da Shippers Council ta masu safara ta jiragen ruwa), da Bankin Maritime da ya shafi lamuran jiragen ruwa, da Bankin Masanaantu (BOI), da PENCOM mai tafiyar da kudaden fansho da sauransu da suke da damar gaske.

Babbar barazana ce ga tsaron Nijeriya da hadin kanta a matsayinta ta kasa a ce kabila daya tilo, cikin fiye da kabilu 300 da ake da su a kasar nan, ke rike da ikon tattalin arzikinta.

A karkashin Shugaba Tinubu, tafiyar da tattalin arziki ya zama yana cike da kumbiya-kumbiya an rasa gane kan gadonsa.

An sanar da `yan Nijeriya cewa cire tallafin mai zai sa a samun wadataccen kudin gudanar da ayyuka na ci gaban zamantakewa, da rage yawan ciwo bashi da Nijeriya ke yi. Amma zuwa dai yanzu akasi aka samu.

Wannan gwamnati a shekaru biyun da ta yi, ta ciwo bashin kudi fiye da wanda gwamnatin Buhari ta ciwo a shekara 8, kuma babu abin da za a iya nunawa cewa ga abin da aka yi da kudin.

Babu abin da za a nuna an yi da kudaden da aka tara sakamakon cire tallafin mai, ko kudaden da aka tara daga FIRS mai tara kudaden shiga, ko kwastam, ko NNPCL, ko tattalin arziki na cikin ruwa wato Blue Economy, wadanda dukkansu Yarbawa dangin Shugaban Kasa ne suke rike da su.

Yadda gwamnonin jihohi da yan Majalisa na Tarayya, da wasu Malaman Addini suka zamayan amshin shata, da ko inkular da `yan boko suka yi, ya sa Shugaba Tinubu ya yi nasarar jefa Arewa cikin kangin yunwa da wahalhalu, kuma da ma ya lafiyar giwa, an ci gaba da amfani da yunwa a matsayar makamin yakar Arewa da kuma danne mutanenta.

An karkata ga gudanar da ayyukan ci gaba a shiyyar siyasa ta asalin Shugaban Kasa ta Kudu Maso Yammacin Kasar nan da kuma kabilar Yarbawa. Kudirorin dokar haraji da aka amince da su kwanan nan, an tsara su ne musamman domin fifita jihar su shugaban kasa wato Legas, da ware sauran sassan kasar.

Arewa na kallon Tinubu a matsayin Kwamandan Askarawan Nijeriya na farko da ya yi watsi tare da nuna halin ko in kula da matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin.

Baccin farfaganda ba dare ba rana mai ban takaici da masu gudanar da lamuran tsaronsa ke ta yadawa, cewa wai tsaro yana ci gaba da inganta, alhali ba haka lamarin yake ba, wannan yana kara wa Shugaba Tinubu bakin jini, da bacin rai a tsakanin mutanen Arewa.

Ba abin mamaki ba ne yadda Shugaba Tinubu ke rikon sakainar kashi da kuma nuna wasu yan lele ne da batun jihohi dayan kasa da matsalar tsaro da balaoi suka shafa.
Bayan kisan-gilla da aka yi a Yelwata ta jihar Binuwai, Shugaban Kasa ya kai ziyara tare da dukkan Manyan Hafsoshin Tsaro da Sakatarem Gwamnatin Tarayya, inda ya yi jawabi a wani taro na `yan siyasa.

Ita ma mai dakinsa ta ziyarci jihar Binuwai da ta Filato, inda ta ba da gudunmawar Naira Biliyan 1 ga wadanda harin `yan fashin daji ya shafa a kowacce jiha.

Su sauran daruruwan mutane da yan fashin daji dayan Boko Haram suke kashewa a kullum, ko wadanda suka mutu ko rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar da ta auku a Mokwa ta jihar Neja, da Maiduguri su ba mutane ba ne ke nan, su ba su cancanci agajin nata ba.

Wannan so na karya da aka nuna wa mutanen jihar Binuwai da jihar Filato, an yi ne saboda Shugaba Tinubu da Mai Dakinsa, a yanzu saboda gwiwarsu ta yi sanyi, suna zawarcin Kiristocin Arewa ne, don samun kuri`unsu a shekarar 2027 bayan watsi da su da ya yi a fadi-tashinsa na yakin neman zaben Shugaban Kasa a 2023.

Ziyarar da Seyi dan Shugaban Kasa ya kai Arewa a lokacin Azumin Watan Ramadan, gwamnonin jihohi sun masa kyakkyawar tarba, ziyara ta rashin mutuntawa da ya kai wa shugabannin addini da sarakuna, da rawar da ya dinga takawa, yana raba wa matasa dafaffiyar shinkafa kamar wasu `yan gudun hijira, ko wadanda aka ci da yaki, wani abu ne da ake masa kallo a yankin a matsayin cin zarafi ga addinin musulunci, da shugabanni da mutanen yankin.

Hada husuma a Masarautar Kano, da kuma barin husumar ta ki ci ta ki cinyewa, da rage karfin ikon Lamidon Adamawa, ana kallon hakan a matsayin cin mutuncin masarautu na gargajiya da ke arewa.

Yadda ba kunya ba tsoro tare da hadarin gaske ake ta ribibin da rige-rigen mayar da kasar Nijeriya mai bin jamiyya daya tilo, da kuma yadda aka tsara kunna wutar rikici a dukkan jamiyyun adawa, ciki har da sabuwar jaririya a fagen, ADC na haifar da jin haushin gwamnatin tarayya a Arewa.

Ana kallon shagalin da gwamnoni da Shugaban Kasa ke yi na Omo-Logo a jihohin arewa da ya ziyarta, a daidai lokacin da mutane suke fama da yunwa da fushi, a matsayin rainin wayau da rashin hankali.

A duk inda na yi wa matasan Nijeriya jawabi, ina tunatar da su cewa matasa ne suke gina kasa, ba tsofaffi ba, tare da yin kira a gare su, su bijire wa kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na rarraba Nijeriya ta fannin kabilanci da na addini domin cimma burin sa na son zuciya na samun kuri`a.

Usman Yusuf Farfesa ne na Nazarin Cututtuka Da Suka Shafi Lafiyar Jini da Kuma Dashen Bargo.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.