Home Opinion Tsadar Kudin Aikin Hajji Na Bana: Shin Ya Kamata Gwamnatin Tarayya ta bawa Mahajjata Tallafi?

Tsadar Kudin Aikin Hajji Na Bana: Shin Ya Kamata Gwamnatin Tarayya ta bawa Mahajjata Tallafi?

by Editor
0 comment

Ahmed Ilallah

A wannan rana ce da karfe 12 na rana, Hukumar Alhazai ta Nijeriya zata rufe karbar kudin maniyatan Aikin Hajji na bana, wanda a bana yayi tashin da bai taba irin sa ba a tarihin Nijeriya, amma ya kamata mu lura, shekaru masu yawa daman kudin Aikin Hajji karuwa yake a duk shekara.

A bana duk wanda ya yi ajiyar kudin sa a Hukumar Alhazan na Naira Miliyan 4 da digo 9, zai cikasa Naira Miliyan 1,918,032.19, saboda haka zai biya kudin da ya kai N6,818,032.19K, duk kuma wanda bai yi ajiya ba kuma, zai biya N8,225,464.74 in zai tashi da ga Jahar Adamawa  ko Borno, N8,254,464.74 ga wanda zasu tashi da sauran Arewacin Nijeriya, sai N8,454,464 ga wanda zau tashi daga Kudancin Nijeriya. Hukumar Alhazan tayi wannan lissafi ne a kan chanjin Dalar Amurka na N1,474 a kan Dallar.

Duk wannan  abun babu wani mamaki, ganin yadda Nijeriya ta samu kanta a tsanin karayar tattalin arziki da hahhawar firashi da faduwar darajar Naira, hatta gayan Burodin da muke saya Naira 300 a baya, a yau ya koma Naira 700 koma fiye da haka.

Shin daidai ne a matsawa Gwamnati ta bada tallafi ga Maniyata don su sami saukin sauke Farali?

Kamar yadda mutane suke ta kiraye kirayen a kan gwamnati ta sanya baki ko hannu, wajen samun saukin zuwa Hajjin, wasu ma na ganin cewa, tunda a yanzu Shugaban Kasa da Mataimakinsa dukka Musulmai ne, kuma lokaci yayi da za a ci gajiyar Muslim-Muslim Ticket, don haka a ke matsawa sai gwamnati ta duba da lamarin ta wajen bada tallafi. Gaskiya yin wannan tunani kuskure ne.

Ya kamata mu tuna fa, a cikin tsare tsaren tattalin arzikin da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bijiro da su, a kwai maida chanijin kudi iri daya, sabanin na baya da gwamnati na da nata, yan chanji na da nasu. Ya kamata mu sake lura kamar haka:

Na farko, ya kamata ma mu fahimci umarnin da Allah yayiwa Musulmai a kan zuwa aikin Hajji. Hajji, kamar yadda Malamai suka sha gaya mana, yana daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma kawai ya wajabta ne a kan wanda Allah ya horewa, ma’ana wanda Allah ya arzutta shi da dukiyar zuwa.

A cikin saukin addinin musulunci, Allah baya dorawa rai abun da bazata ta iya yi ba, kuma Allah baya sanya rai ta dauki abin da bata ikon iya dauka ba. Duk wanda bashi da hallin zuwa Hajji ba dole bane a kan sa. Allah (SWT) yana gaya mana “Allah baya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya tsirfinta, kuma a kansa akwai  zunubin abin da yayi ta aikatawa ……………………, Ya Ubangijinmu! Kadda Ka Sanya mu daukar abin da babu iko gare mu……………….” Qur’an 2/286.

Sabo da haka babu wani abin tashin hankali ko damuwa ga Musulmi a irin wannan yanayi, shi dai ya kiyaye niyar sa, yaji tsoron Allah, yabi dokokin Allah, ya nemi Allah ya bashi kudin zuwa, duk taskar arziki Tasa ce.

Na biyu, ya kamata mu sani fa, Nijeriya ba kawai ta Musulmai bace, kuma zaman Shugaban Kasa da Mataimakin sa Musulmai ba zai sanya a fifita ta suba a kan sauran yan kasa, aikin gwamnati ta samar da Hukumar da za tan a tsarawa Musulman yin irin wannan aikin tun da ya shafi kasa da kasa, kamar yadda ya za ta samarwa sauran mabiya wani addinan irin wannan hukuma don suma zuwa tasu ibadar.

A zahirin gaskiya, a zamantakewa ta Nijeriya babu adalci ga Gwamnatin  Tarayya ta bawa wanni yankin al’ummah ko addini wani tallafi, sai dai in har yin hakan maslaha ce ta kasa baki daya, ba wai  domin kawai su suke mulkiba, ko kuma su sukafi yawa ba.

Ya kamata mu sani fa, ba kawai Musulmai bane suka zabi wannan gwamnati, babu wani mai addini a Nijeriya da bai zabe ta ba. Ana bada tallafi ne in har kowane dan Kasa zai amfana da irin wannan tallafin, misalign irin na Man Fetur da aka cire ko na noma ko ilimi ko kasuwanci.

Ya kamata mu fahimta cewa addinin Musulunci mai sauki ne, Allah yana dora mana abun da za mu iya ne, kuma baya kama mu a kan abun da yafi karfin mu.

 

You may also like

©2024. Stallion Times Media Services Ltd. All Rights Reserved.