Home » Sarkin Kano Aminu Ado Yayi Kira Da A Dunga Taimakawa Magidanta Wadanda Basu Da Halin Ciyar Da Iyalansu

Sarkin Kano Aminu Ado Yayi Kira Da A Dunga Taimakawa Magidanta Wadanda Basu Da Halin Ciyar Da Iyalansu

Isiyaku Ahmed

Daga Abubakar Balarabe Kofar Naisa

Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya jagoranci taron saukar karatun alkur’ani mai girma na dalubai 51 dake makarantar Madarasatu  Muhammadiyya Islamiyya, Rijiyar Lemo Kano.

A karon farko tun bayan komawarsa gidan sarauta dake Nassarawa a birnin Kano, mai martaba sarkin kano ya jagoranci taron saukar alkur’ani mai tsarki na dalibai 51.

Taron wanda aka gudanar dashi a safiyar ranar litinin dinnan a fadar mai martaba dake Nassarawa, Sarkin ya bukaci daliban da suka sauke karatun alkur’anin mai girma su fadada neman iliminsu domin amfanar al’uma.

Sarkin ya jaddada bukatar iyaye su cigaba da baiwa yara tarbiyya da kula da neman iliminsu domin samun al’uma tagari.

Da yake jawabi akan hakkin da malamai yake akansu kuwa Sarkin ya tunasar dasu cewa ya zama wajibi su rike amanar da Allah ya dora musu na tarbiyantar da daliban da kuma basu ilimi mai inganci.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.