Daga Ahmed Ilallah
Jahar Kano da Jahar Rivers, jahohi ne masu muhimmanci a siyasar Nijeriya, saboda yawan al’umarsu, yanayin siyasarsu da kuma tattalin arzikin su.
Tabbas, a ce jama’iyya mai mulki a Nijeriya bata da ko daya daga cikin wannan jahoji abin takaici ne, dukkanin gwamnonin wannan jahohi da sauran manyan zababbu na Jama’iyar PDP da NNPP ne.
Rigimar jahar Kanon da Rivers, wanda zargi ya shigo cewar gwamnatin tarayya ta Jama’iyar APC na amfanin da karfin jami’an tsaro ta fito da na fito gwamnonin wannan jajohi, yayin da suke daukan mataken kawo sauye-sauye a jahar su.
Sa soka da sakin da yake barazana da tsaro a wannan jahohi, wanda wannan ya kawo zargin, yunkurin gwamnatin APC da kakabawa wannan jahohi dokar ta baci, dama kawar da gwamnonin su gefe, ya kawo sabon shafi a siyasar Nijeriya.
Rigimar jahar Rivers wanda ta samo asali daga sabanin Tsohon Gwamna jahar Nelson Wike da magajin sa Governor Fafura.
Ko a wannan makon ma, an samu rasa rayukan mutane har da yan Sanda, bayan karewar tsofaffin Shugabannin Kanan Hukumomi, da kuma nada sabbin da gwamnan ya nada, a kan shiga da barin office tsakanin bangarorin hiyu.
Tsoffin Shugabannin da suke biyayya da Tsohon Gwamna Wike sun yi tirjiya da kin barin office din Kananan Hukumomin.
Kafin wannan lokacin, daman a jahar a baya anyi ta rigima tsakanin wannan bangarori guda biyu, harma 27 daga cikin Yan Majalissun Jahar suka sauya sheka daga Jama’iyar su ta PDP zuwa APC, da kuma yunkurin tsige Gwamnan Jahar.
Wannan rigimar ta jawo abubuwa da yawa, da suka hada da rushe majalissar jahar da chanja mata matsugunni, ga kuma shari’oi daban daban.
Ita kuma Jahar Kano wanda yunkurin da Majalissar Dokokin Jahar ta yin Dokar Masarautar Kano ta 2024 wanda ta rushe Masarautun Kano guda hudu da kuma chire Sarkin Kano na 15 da nada Sarki Muhammad Sanusi.
Sabanin a bin da a ka saba gani, bayan shigar da Karan da bangaren tsohon sarkin su kayi, sai gashi, wannan bangaren sun sami tsaro mai karfi da ga jami’an tsaron gwamnatin Tarayya, wannan mataki ya raba sarautar Kanon biyu, wanda ba dan al’umar jahar sun maida hankalin su ba da tabbas rigima ta barke a tsakanin su.
Gannin yadda shugaba Tinubu ya ki maida hankali wajen kawo karshen wannan rigingimu da sulhuntawa a matsayin sa na Shugaba, yana saka ayoyin tambaya a kan manufofin wannan gwamnati a kan wannan jahohi.
Shin wannan rigingimu suna da alfanu ga Jama’iyar APC mai mulki?
Wannan mataki da dabaru na marawa wani bangare da karfin jami’an tsaro, kan iya nuni da wata manufa ta siyasa daga gwamnatin APC, wanda kan iya fusata mutanen wannan jajohi na ragewa gwamnatin tarayya farin jini dama kara gishiri a rashin tsaron da musamman Arewacin Nijeriya yake ciki.
A nazari na siyasa wannan danbarwa ko rikici a Kano da Rivers, kawai zai dadawa wasu tsirarune dan biyan bukatar siyasar su, amma ba muaradin al’umarsu da zaman lafiyar dimokaradiyya ba.
A shari’un da Kotun Koli ta yanke a kan zabinkan gwamnoni a baya, tayi nuni da martaba zabben da alumna suka yi a demokaradiyya, makmakon togewa da wasu tsarabe tsarabe na bin gababin aiwatar da doka. Wanda a zahiri ana sanya su ne domin bawa wanda bashi da nasara damar jayayya.
Tabbas Shugaba Tinubu in baiyi karatun ta nutsu ba a kan wannan rigingimu to yana nema ruguza gadon sa ne a kakar zabe mai zuwa a 2027.