Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya, IHRC RFT, reshen Najeriya, tana bayyana tashin hankalin ta da Allah-wadai bisa yawaitar sace-sacen ɗalibai da ake yi a makarantu a faɗin ƙasar nan.
Aukuwar hare-haren da aka kai a makarantu uku cikin mako guda na nuna cewa wannan lamari ba bazata ba ne, akwai tsari, shiri, da kuma alamar cewa akwai hannun wasu a cikin lamarin.
Rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaro daga wasu makarantu kafin sace yaran, kamar yadda Gwamnan Jihar Kebbi ya yi korafi a bayyane, na nuna wata babbar gibin tsaro da ke bukatar bincike. Wannan ba za a kira shi da haɗari kawai ba. Alamu sun nuna wani shiri ne, ko muce wani wasan kwaikwayo ne da wata ɓoyayyiyar manufar da ake aiwatarwa a bayan fage.
Wadannan munanan hare-hare kan yara sun karya dokokin bil’adama da dama, kundin tsarin mulki, da kuma duk wata ka’ida ta adalci da kariya ga rayuwa.
An Karya Dokokin Duniya Da (UDHR) Da Kundin Tsarin Mulkin Nigeria
- Dokar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (UDHR)
Mataki na 3 tace: Kowane mutum na da ‘yancin rayuwa, ‘yanci da tsaron jikinsa.
Sace yara ya keta wannan hakki kai tsaye.
Mataki na 25(2): Uwayen yara da kananan yara suna da hakkin kulawa ta musamman.
Wannan yake nuna cewa Najeriya na da nauyin tabbatar da tsaron kowane yaro.
Mataki na 26: Kowane mutum na da ‘yancin ilimi.
Idan makarantu sun zama wurin farautar ‘yan ta’adda, to an tozarta hakkin ilimi.
- Kundin Tsarin Mulkin Najeriya (1999, wanda aka gyara)
Sashe na 14(2)(b): Tsaro da walwalar jama’a su ne babban aikin gwamnati.
Kaga kenan dole gwamnati ta dauki alhakin duk wata gazawa da ta janyo irin wadannan hare-hare.
Sashe na 33: Yana kare hakkin rayuwa.
Sashe na 34: Yana kare mutuncin dan Adam, ciki har da yara.
Sashe na 18: Yana tabbatar da ilimi a matakai daban-daban tare da kariyarsa.
Yawaitar sace dalibai ya saba wa wadannan tanade-tanade gaba ɗaya.
Matsayin IHRC-RFT Nigeria Chapters
- Wannan Lamari Ba Karamin Laifi Bane – Akwai Tsari da Shiri
Tsarin kai hare-hare a lokaci ɗaya yana nuna:
Akwai siyasa a cikin lamarin,
Akwai wata manufar ɓoye,
Akwai yunƙurin tayar da hankalin jama’a da gwamnatin kasa.
Yadda aka kai hare-haren a kankanin lokaci yana nuna akwai alamun tambaya.
Jama’a na da hakkin sanin gaskiya.
Babu wani dalili, siyasa, addini, yau da gobe, da zai halatta cutar da yaro.
Bukatunmu Gurin Gwamnatin Taraayya
- Ayi Gaggawar Ceto Yaran Nan Take
Muna kira ga:
Shugaban Kasa,
Mai Ba da Shawara Kan Tsaro,
Hafsan Tsaro,
Da dukkan hukumomin leken asiri,
su kaddamar da aikin ceto cikin hanzari kafin lokaci ya kure.
- A Kafa Kwamitin Bincike Mai Zaman Kansa
Don gano:
Dalilin janye jami’an tsaro,
Wanda ya bayar da umarni,
Ko akwai siyasa a cikin lamarin.
- A Hukunta Duk Wanda Aka Samu Da Hannu
Ko jami’in tsaro ne, ko dan siyasa, ko farar hula—duk wanda ya taimaka ko ya amfana daga wannan mummunan aiki.
- A Kara Kare Makarantu a Fadin Kasa
Da:
Jami’an tsaro na musamman (School Protection Units),
Na’urorin tsaro (CCTV, ƙararrawa),
A shigar da al’umma na kwarai cikin harkar tsaro don samun rahotanni cikin gaggawa.
Kira Na Kaeshe
Najeriya ta kai matakin haɗari.
Ba za mu zura ido yara suna zama kayayyakin siyasa ba.
Yara sune makomar Najeriya, ba abun farauta ga Yan taadda ba.
Saboda haka muna yin wannan kira da babbar murya:
Mun gaji da jin dalilai – muna buƙatar aiki.
Mun gaji da kuskuren tsaro – muna buƙatar kariya.
Muna buƙatar a dawo da yaranmu lafiya – YAU, BA GOBE BA.
Hukumar IHRC-RFT Nigeria tana tare da iyayen da abin ya shafa, kuma muna kira ga gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa, gaskiya, da adalci.
