Home » Kano: Karamar Hukumar Nassarawa Ta Dauki Nauyin Dalibai 21 Don Karatu A School of Nursing, Midwifery Kazaure

Kano: Karamar Hukumar Nassarawa Ta Dauki Nauyin Dalibai 21 Don Karatu A School of Nursing, Midwifery Kazaure

Isiyaku Ahmed
7 views
A+A-
Reset

Karamar Hukumar Nassarawa ta dauki nauyin dalibai sama da ashirin da daya (21) don karatu a School of Nursing and Midwifery, Kazaure, dake Jihar Jigawa kan miliyoyin Naira har zuwa kammala karatunsu.

Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, Amb. Hon. Yusuf Shuaibu Imam Ogan Boye, ne ya bayyana hakan yayin bikin bankwana da daliban da suka tafi makarantar domin fara karatunsu.

Amb. Yusuf Shuaibu Imam Ogan Boye ya jaddada muhimmancin karatu da sadaukarwa, inda ya shawarci daliban da su jajirce domin samun sakamako mai kyau. Ya kuma tunatar da su cewa, Karamar Hukumar Nassarawa ta zuba jari mai yawa a rayuwarsu, don haka kada su bayar da kunya.

“Karamar Hukumar Nassarawa ta kashe miliyoyin Naira wajen tallafa muku domin ku samu ilimi mai inganci. Ina fatan zaku kasance jakadun gari nagari a duk inda kuka je,” in ji shi.

A nasa jawabin, Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Nassarawa, Hon. Ado Muhammad Hotoro (Mai Kaba), ya yi kira ga iyayen daliban da su rika bibiyar ci gaban ‘ya’yansu domin tabbatar da cewa sun zama jakadun nagari masu halaye na kirki da ladabi.

Ya kara da cewa za a rika gwada daliban a duk bayan watanni shida domin tantance masu kwazo da jajircewa. Saboda haka, ya bukaci iyaye da su kara dagewa wajen karfafa gwiwar ‘ya’yansu.

Daga Sharif Zahraddeen Usman

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.