Daga Ahmed Ilallah
Kananan Hukumomin Jahar Jigawa, da suka samu kansu a da da yanzu, a lokacin da suke cin gashin kai, da kuma a yanzu da suke karkashin kulawar jaha.
Cigaban da ake samu a yanzu yafi na da, ci gaban al’umar da aiyukan raya Kasa, tabas gwamnati baya da na yanzu sun taka rawar gani.
Kamar yadda ya ke faruwa a yanzu, Shugaban Kasa ta hannun Babban Lauyan Gwamnati, sun maka Jahohin Kasar Nan 36 gaban babbar Kotun Kasa, don Kananan Hukumomin suna shugabancin su da karbar kudaden su kai tsaye ba tare da zuwa ta hannun jahohin su ba, kamar yadda ya ke a yanzu.
Wannan ya biyo bayan korafe korafe da jagororin Siyasa sukeyi da kuma wata bukata ta musamman ta mutanen Kudu Maso Yamma na son a chanja fasalin Nijeriya, ta yadda kowanne yanki zai zamanto mai cin gashin kanta, kamar yadda a ke rade-radi.
Wannan daukan mataki a kan nemawa Kananan Hukumomin yanci, yana da ga cikin somin tabin wannan tsari.
Amma fa mu sani, a kwai jahohi da dama da a yanzu sun fi samun cigaba a wannan tsari da ke ciki, na gudanar da Kananan Hukumomi karkashin kulawar Jahohi.
A yau Kananan Hukumomin Jahar Jigawa suna kan gaba wajen aiyukan raya Kasa da cigaban al’ummah.
Ko a yanzu, Hukumar Kula da Kananan Hukumomi, karkashin jagororin Ahmed Garba MK, ta nada kwamitin da kawo tsari da chanja fasalin aiyuka da gudanarwar Kananan Hukumomin, domin dacewa da bukatuwar al’ummah da dun chanjin Zamani.
Wannan da daga cikin kulawar da Jahar Jigawa take domin inganta mulkin Kananan Hukumomin.
A yau babu wata headquarters ta Karamar Hukuma a Jahar Jigawa da bata da a kalla hanyar mota ta zamani sama da kilometers 15.
A yau a Jigawa duk wata mazabar kansila ta na da karamar asibiti wato Primary Health Center.
Harkar samar da ruwan sha, tsabtace muhalli da sauran manyan aiyukan al’ummah, Kananan Hukumomin Jahar Jigawa sunyi fice.
Koma mai ake bukata game da mulkin Kananan Hukumomi shine, a samu amana da sanin makamar aiki, domin duk ana yi ne domin al’ummah.
Amma da a yanzu a shaidu na samun gagarunin cigaba, musamman a irin jaha ta Jigawa.