Ahmed Ilallah
Maigirma Gwamna a matsayin mu na Yan Jigawa, kuma kunnuwa da bakunan ku, a doran sa kai, bayan ji, saurare da fahimtar al’amuran wannan gwamnati, a wannan karon ma an bani sako zuwa gare ka, a matsayin ka jagora na gari ga al’umar jahar Jigawa.
A karshen makon nan, na samu kiraye kiraye har ma da ziyarar mutane daban daban, daga cikin su a kwai mutanen da suka ajiye ko kammla aikin su a gwamnatin Jahar Jigawa, wato wayanda suka yi ritaya, sama da watanni wasu ma sama da shekara.
Tabbas a cikin bayanan da muka yi da wasu a kwai abin tausayi, ganin cewa, mutum ya bar aiki sama da wata goma sha, babu fansho, babu gratuti ga kuma yanayi na halin rayuwa da yan kasa suke ciki.
Kamar yadda na fada a baya, ina tausaya wa Maigirma Gwamna a kan wasu aiyuka da ya gada, wanda suke cike da kalubale, kuma suke bukaratar gyaran da zai dau tsawan lokaci, wannan hukuma ta fansho (State and Local Government Contributory Pension Scheme) tana ciki, ko da a baya ma, an sha magana a kan wannan batu.
Koda yake, Maigirma Gwamna ya kudiri aniyar gyara a kan duk abubuwan da ya gada, da mai kyawu da ma masu damuwa.
Tabbas Maigirma Gwamna bai boye damuwar sa ba, wajen kawo karshen wannan matsala ta hukumar fansho, a watan farko na maigirma gwamna ya kafa kwamiti don gano matsalolin wannna hukuma da magance su.
Amma abin da ya kamata mu sake faimta shine, ita hukumar pension ta Jigawa, hukuma ce mai zaman kanta bisa doka, tana tattara Adashen Ma’aikata daga albashin su da kuma kaso na gwamnati, hukumar ce zata samar da yadda za a sarrafa kudin, domin samun riba.
Wannan hukuma ita kuma ta ke biyan ma’akatan hakkokin da suka hada da gratuti da fansho na wata-wata, da zarar sun yi ritaya. Doka ta bawa wannan hukuma iko da yancin gudanar da harkokin ta wajen tattarawa da biyan hakkin ma’aikata.
A ka’ida ma’aikaci baya wuce watanni uku, bayan ya bayar da sanarwar ritayar sa a aiki, zai soma samun hakkokin sa, sai gashi a hankali, ma’aikatan kan wuce shekara ma ba tare da an biya su hakkokin su ba.
Matsalolin da suka hada da yawan ritayar ma’aikata da kuma kasa daukan ma’aikatan a jaha da kanannan hukumomi kamar yadda kwamatin da maigirma gwamna ya kaffa suka bayyana, shi ya kawo wa wannan hukuma tangardar da tasgaron da ta sami kanta a ciki a yanzu.
A wattanin baya bisa tausayi na Maigirma Gwamna, ya arawa wannan hukuma kudi har Naira Biliyan biyu, domin biyan wayanda suka yi ritaya suke jira a biya su hakkin su.
Ko da a watan May, a lokacin bikin ranar ma’aikata maigirma gwamna ya sake cewa zai bawa wannan hukuma Naira Biliyan Daya.
Maigirma Gwamna ga sakon wadannan mutanen domin ka sake tausaya musu kamar yadda yake cikin burin ka na kautatawa dukkanin al’umar jahar Jigawa, domin mutanen nan suna cikin wani hali na abin tausayi.
Maigirma Gwamna kamar yadda muka bada shawara a baya a kan a duba iyuwar sanya ma’aikatan da suka yi ritaya a kan jadawalin karbar fansho kafin a biya su gratuti, wannan kan iya rage musu tsananin wahala da za su shiga yayin da suka bar aiki.