Home » Arewa Na Rugujewa Yayin Da Tunannin Al’al’umar Su Ya Koma Jayayyar Sarauta Da Malanta

Arewa Na Rugujewa Yayin Da Tunannin Al’al’umar Su Ya Koma Jayayyar Sarauta Da Malanta

Isiyaku Ahmed

Ahmed Ilallah

Ko shakka babu in kace, a fasalin Nijeriya a yanzu babu yankin da yake cikin talauci, kalubalai, ta’addanci kamar Yankin Arewa. Arewan ma Arewa-maso-Yamma, wanda kusan jahohin su biyar a cikin bakwai, suna cikin masifar rashin tsaro, bala’i, karfin talauci da tashin hankali.

Bayan Tsohon Shugaban kasa Buhari ta hannun tsohon Ministan Aiyuka, wanda kuma shine tsohon gwamnan jahar Legas Fashola ya samar da manyan aiyuka a yankin su, kamar gina titunan dogo a cikin garin Legas, Legas zuwa Ibadan, manyan tituna da makamantan su.

A wancen lokacin kuma jahohin Arewa-maso-Yamma irin su Katsina, Zamfara, Kaduna suna cikin bala’in Yan ta’adda, wanda ya ruguza dan cigaban da suke da su.

Ko a wannan lokacin ma, da Shugaba Tinubu ke mulki, yankin kudu yafi yankin Arewa zaman lafiya, bunkasar tattalin arziki, da walwalar al’ummah. Ko a wannan zangon ma a tarihance ba a taba bada kwangilar gina titi mai tsadar da ya kai, sabon titin Lagos zuwa Clalaba ba. Amma fa har yanzu ba a kai ga kammala titin Kano zuwa Abuja ba.

Abin takaicin, a lokacin da duk wani mai kishin wannan yankin ya kamata su nutsu, Masu Mulki mu, Sarakunan mu, Yan Bokon mu, Yan Siyasa, Matasa da talakawan mu, domin samawa wannan yankin saukin masifar da take ciki, da kuma dora yankin a kan tsanin cigaba da bunkasar tattalin arzikin mutanen yankin.

Sai gashi a na wasa da kwakwalen mutanen wannan yankin an barsu da fada marar dalili.

Kash! Duk ilimi da siyasar Yan Arewa, sai gashi sun bige da jayayyar sarakunan gargajiya, na wasu muhimman garuruwa, abin kamar wasan kwaikwayo, daga danbarwar sarakunan kano, wanda har yanzu danbarwar bata kare ba. Daga nan kuma a ka tafi Katsina da Sokoto duk wata jayayya ce marar tasiri a kan rayuwar mutanen wannan yankin.

Sai gashi b agama wannan danbarwar ba, sai gashi hankalin mutanen yankin, musamman ma Malaman su masu fada a ji, sun maida hankalin su da tunanin a kan hayaniya Samoa Agreement da LGBT, wanda a fakaice kawai a na bullo da wadannan abubuwan ne don kautar da hankalin mutanen yankin a kan matsalolin su.

Lokaci na sake kure mana, sai gashi, kawai sanarwar yunkurin matasa na yin zanga zanga a kan matsin rayuwa da kasa take ciki, ya sake dulmiya tunanin manyan mu, musamman ma Malamai a ka hakikancewa dayin damaliya a kan halacci ko akasan yin zanga zangar.

Wanda kawai wani sabon salon masu mulikin zamani ne, na aro ko sayen tunanin wannan maluman don su taimaka, wajen kawar da tunanin mutane a kan halin da suke ciki.

A bin haushin a wannan karon shine, yadda reni da zubar da darajar a tsakanin wannnan maluman da mabiyan su ke sake fitowa fili. Harma a na zargin da ko sun karbi na goro ne a refe kofar da suka yi da jami’an gwamnatin Tinubu.

Koma dai ke faruwa, in har bamu maida hankali ba, wannan zamanin ma zai iya shudewa ba tare da an assalawa yankin Arewacin Nijeriya komai ba.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.