Mulkin Demokaradiyya da ya kasance mulkin zabin al’ummah domin ciyar da su gaba, sai ga shi a tsawan wannan lokacin su mutanen wannan yankin tamkar baya suka ci.
Siyasa da mulkin Dimokaradiyya ya sanya musifa da rashin kyakkyawar makoma ga al’umar wannan yankin.
Duk al’amuran wannan yankin sun dawo baya, kamar tsaro, ilimi da harkar lafiya, hatta ababan more rayuwa irin su hanyoyin mota, laying dogo duk baya a ka ci.
A yau noman da a ke tunkaho da shi a Arewa aiyukan ta’addanci ya hana shi, wannan ya taimaka wajen sanya mutanen wannan yanki cikin yunwa da talauci.
Koda a ziyarar da Dattijan Arewa suka kaiwa Shugaba Tinubu a jiya, Tinubun yayi musu shagubai da matashiya. Tinubun yace ba abin yarda bane masifar talaucin da ke damun Arewacin Nijeriya da lalacewar abubuwan more rayuwar a yankin.
Shugaba Tinubun ya nuna damuwa da yawan yaran da basa zuwa Makaranta. Yayi kira da Dattijan Arewan da su ja hankalin Gwamnonin jahohin su a kan suna zama a jahohin su don yiwa mutane aiki.
Wannan karara ya nuna koma bayan da Arewacin Nijeriya ta samu, wanda a baya babu wani Shugaba ko daga wane yankin wannan kasa yake da zai yi mana wannan shagube.
Wai shin me yasa demokaradiyya ta jawo mana komabaya? Shin su waye ke da wannan alhakin?
Kafin komawa kan wannan tambayoyi, ko da ba muyi tambishi ba, kowanne mutumin da ke Arewacin Nijeriya ya san yadda al’umar wannan yanki suke cikin bala’in talauci da tsadar rayuwa gama wayanda suke dan samun taro, sisi.
A wannan lokacin ne ran mutanen Arewacin ya zama banza, don tsananin rashin tsaro. Abin takaicin a hannun yan uwan su, da sunan Addini ko fashin daji.
Kamar yadda Shugaba Tinubun ya fada, halin da yara suke ciki a halin yanzu da rashin kulawar iyaye da rashin zuwan yara Makaranta.
Babban tashin hankalin shine, shigar da wannan yara aiyukan ta’addanci na fashin daji da Boko Haram.
Kan tambayar mu ta baya, zai yi wuya a ce wannan hali da Arewacin Nijeriya ya shiga, kusan dukkanin yayanta na da laifi, kama daga daga talakawan da ke zabar shugabannin da ke jagorar su.
Manyan masu laifin sune shugabannin siyasar wannan yankin, musamman Gwamnonin jahohin yankin. Sun kasa hada kawukan su don yin aiki tare wajen warware matsalolin da ke samun su, irin su rashin tsaro, almajiranta da tattalin arziki.
Abin takaicin shine, ko da gwamnatin da shude, sai da tsohon Gwamnan Kaduna ya koka rashin samun hadin kai da sauran Yan uwansa Gwamnoni makwamtan sa don shawo kan rashin tsaron da ke addabar su.
Shugabannin siyasar wannan yankin a kullum biyan bukatar su ta Siyasa da kashin kai suke sanya wa a gaba fiye da bukatuwa da makomar al’umar su.
Babu wata taswira ta hadaka da hangen nesa da wannan yankin ya ke da shi don gani an samu moriyar demokaradiyya ga mutanen yankin.
Duba da yadda sauran yankuna wannan kasa suke ci gaba, ya zama wajibi wannan yankin ya mike don ceto al’umar ta.