Kungiyar International Human Rights Commission–Relief Fund Trust (IHRC–RFT) ta Najeriya ta yi kira ga gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, da al’umma baki ɗaya da su ɗauki matakan da suka dace wajen inganta rayuwa da jin daɗin tsofaffin jami’ai, ma’aikata, da sauran mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar ƙasa.
A cikin wata sanarwa yau, shugaban IHRC–RFT Nigeria, Jakada Abdullahi Bakoji Adamu, ya sanya wa hannu domin tunawa da Ranar Jarumai ta 2025 (Veterans’ Remembrance Day), kungiyar ta bayyana tsofaffin jami’ai a matsayin “tushe na zaman lafiya, tsaro, da cigaban ƙasa,” inda ta jaddada cewa sun sadaukar da lokacinsu, ƙarfinsu, da lafiyarsu domin kare ɗaukakar da haɗin kan Najeriya.
Jakadan Adamu ya nuna damuwa kan yadda yawancin tsofaffin jami’an ke fuskantar ƙalubale bayan ritaya, ciki har da ƙarancin fansho, rashin kulawar lafiya, da sakaci daga hukumomin da suka taɓa yi wa hidima.
“Wasu daga cikin waɗannan jarumai na fama da rashin abinci, magani, ko abin da za su dogara da shi a rayuwa ta yau da kullum,” in ji shi. “Ba wai kawai mu riƙa tunawa da su sau ɗaya a shekara ba — ya zama wajibi mu ɗauki matakai na zahiri ta hanyar shirye-shiryen tallafi, kulawar lafiya, da nuna godiya ga waɗanda suka yi wa ƙasar hidima da gaskiya.”
Ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su ƙarfafa tsarin tallafin tsofaffi, tare da kiran kamfanoni da masu hannu da shuni su taimaka wajen shirye-shiryen da za su inganta rayuwar waɗannan tsofaffin ma’aikata.
Jakadan Adamu ya yi addu’a ga tsofaffin jami’an ƙasar, yana neman Allah Ya ba su lafiya, ƙarfi, da sakamako mai yawa bisa sadaukarwarsu.
Ya ƙare da cewa, “Girmama tsofaffin jarumai tamkar girmama tarihin ƙasa ne.”
