Home » Daga “Kisan Ƙare – Dangi Da Aka Ce Ana Yi Wa Kiristoci” zuwa “Yunƙurin Juyin Mulki”: A Dai Yi Taka-Tsantsa

Daga “Kisan Ƙare – Dangi Da Aka Ce Ana Yi Wa Kiristoci” zuwa “Yunƙurin Juyin Mulki”: A Dai Yi Taka-Tsantsa

Stallion Times
8 views
A+A-
Reset

Na Farfesa Usman Yusuf

Wannan muƙala ta yi batu ne a kan ƙullalliyar da aka ƙulla cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare-dangi a Nijeriya, da jita-jitar cewa an kitsa yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.

“YI WA KIRISTOCI KISAN ƘARE-DANGI”

Nijeriya a `yan kwanakin nan, ana tayi mata yamaɗɗin ƙarya da ɓata mata suna a kafafun labaru na ƙasashen duniya, inda ake mata zargi mara tushe cewa gwamnati tana ba da goyon baya ana yi wa Kiristoci kisan ƙare-dangi a kasar.

Wannan labari na karya ya bazu bayan da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya gabatar da jawabi a wajen zama na 80 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ya gudana 9-28 ga watan Satumba, 2025, inda ya fito fili ya fayyace matsayin Nijeriya a hukumance, na goyon bayan ƙirƙiro ƙasar Falasdinawa mai zaman kanta.

Matsayin na Nijeriya a wajen taron ya baƙanta wa babbar kamun kafan da Israila take yi wa Amurka, wacce ta ƙunshi ɗaiɗaikun jamaa masu kuɗin gaske da ƙungiyoyi da suke ƙarfafa tsare-tsare da manufofi da suke fifita kafuwar ƙasar Israila da adawa da waɗanda suke kallo a matsayin maƙiyan buƙatun Israila.

ƙungiya mafi girma ta Amurka wacce take kare muradun Israila, wacce take da mambobi fiye da mutum miliyan baƙwai, ita ce Christians United for Israel. Kwamitin hulda da jamaa Israila da ke Amurka: American Israel Public Affairs Committee (AIPAC) a taƙaice, shi ma wani gungu ne mai ƙarfin gaske ayan kamun ƙafar kafa Israila. Israila na samun ƙudaden gudanar da gangami na mambobin da suke cikin manyan jam`iyyun siyasa guda biyu na Amurka.

Wata muhimmiyar ƙungiyar wannan fafutukar kafa ƙasar Israila ita ce Christian Evangelical lobby, wacce take da rinjaye ko iko da ƙurun a jihohin da kiristoci suka mamaye da ke kudancin Amurka. Idan ɗan takara yana so ya ci zaɓe daga ƙamar hukuma zuwa matakin shugaban ƙasa – dole ɗan takaran ya zama yana da ƙyakkyawar alaƙa da waɗannan ƙungiyoyi guda biyu da suke kan gaba wajen mara wa Isra`ila baya.

Saboda haka kalaman `yan siyasa irin su Sanata Ted Cruise wanda AIPAC ke samar masa da kuɗaɗen ɗaukar nauyinsa kuma yana son zama shugaban kasar Amurka, ba wani abu ba ne illa neman goyon baya daga waɗannan ƙungiyoyi guda biyu masu ƙarfin gaske.

Wasu ƙungiyoyi na Coci-Coci da Kiristoci da ke Nijeriya, sun daɗe suna yaɗa labarun ƙarya cewa ana tsananta wa kiristoci tare da kashe su da cikakken goyon bayan gwamnati. Su kuma wadannan Coci-Coci da ƙungiyoyi su yi ta samun maƙudan kuɗaɗe daga ƙungiyoyi na Amurka da ake yaudara da wadannan ƙareraki.

An fi dagewa wajen yaɗa irin waɗannan ƙareraki musamman idan Musulmi ne yake shugabancin Nijeriya.

Yadda yanzu Nijeriya ba ta da wakilci na jakadanci a duk faɗin duniya, ya sa ƙasar ba ta samun wakilci a duniya, kuma kowa ke iya samun damar yaɗa irin waɗannan ƙareraki kuma a dinga amincewa da su.

Sakamakon wadannan labaru na ƙarya da kafofin yada labaru na duniya suke yaɗawa a game da Nijeriya, maimakon Shugaba Tinubu ya zama mai haɗa kan al’umma a matsayinsa na jagoran ƙasarnan da ke cikin wani yanayi, kawai sai ya hau jirgi ya tafi Jos babban birnin jihar Filato, ya yi wata ganawa ta sirri da shugabannin Kiristoci. Zuwa yanzu dai bai tuntubi wani shugaba na al`umar Musulman Nijeriya da aka tasa a gaba ba.

Al`umar Musulmin Nijeriya ba su ji daɗin hakan ba, kuma a gaskiya waɗannan ƙareraki marasa tushe da wasu waɗanda ba sa son a zauna lafiya suke ta fakewa da rigar addini suke yaɗawa, suna ci musu tuwo a ƙwarya.

Ainihin burin su shi ne yin abin da masu ɗaukar nauyin su daga ƙasashen ƙetare suke so, wato haifar da rarrabuwa tsakanin Musulmi da Kiristocin Nijeriya, musamman a arewa, da kuma cinna wa Nijeriya wuta, kawai domin cimma burin su na neman abin duniya.

Da na ga wannan labari yana yawo koina a soshiyal midiya, sai na ce na kuwa taba ganin hakan, a lokacin da na wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar na III, a wajen taron shekara-shekara karo na biyu na duniya a kan `Yancin Walwalar Addini da ya gudana a Washington, DC, babban birnin Amurka, a ranar 28-30 ga watan Yuni, na shekarar 2022.

Na rubuta wata muƙala a game da irin abubuwan da na ji a wajen taron, wacce aka wallafata a jaridar Daily Trust ta ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2022 mai taken : Message From Washington DC.

Na yanke shawarar sake wallafa wannan muƙala daidai yadda take a wancan lokacin da aka fara wallafata, fiye da shekaru uku da suka gabata.

SAƘO DAGA WASHINGTON DC

DA AKA WALLAFA A RANAR 4 GA WATAN YULI, 2022

Wata babbar girmamawa ce a gare ni, a nemi in wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Saad Abubakar na III a wajen taron shekara-shekara karo na biyu na babban taro na duniya a kanyancin walwalar addini wato International Religious Freedom (IRF) a Washington DC, Amurka a ranar 28-30 ga watan Yuni, na shekarar 2022. Mai alfarma bai ba wani jawabi da ya tsara domin in gabatar a wajen ba, saboda haka duk abin da na fada ko na rubuta, amsa ce ga abin da na ji na kuma karanta a wajen taron.

An ba da rahoton cewa taron shi ne taro mafi girma a duniya da ya mayar da hankali a kan ɗaukaka ci gaban walwalar addini a duniya da masu halartarsa suka haura mutum 1,200 a wannan shekarar.

Muhimmin abin da aka fi mayar da hankali a kan sa a taron na bana shi ne yancin gudanar da addinin a koina cikin fadin duniya da gwagwarmayar da mutane da dama suke fuskanta a game da gudanar da addininan su.

An fito fili ana musayar ra`ayi a game da addini, da imani, abubuwan da suke kunno kai a tsakanin mutane da suka yi imani saboda jahilci da rashin fahimta.

WAKILAN NIJERIYA: Daga gidauniya zama lafiya ta duniya wato Global Peace Foundation; Mai Alfarmar Sarkin Musulmi wanda na wakilta, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Samson Olasupo Adeniyi Ayokunle, Bishop Sunday Onuoha, Bishop na cocin Methodist kuma daya daga cikin shugabannin Kungiyar Kyautata Fahimtar Juna Tsakanin Mabiya Addinai daban-Daban (Interfaith Dialogue Forum), Ms Anne Marie Briggs, John Joseph Hayab, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya Reshen Jihar Kaduna da Ms. Sarafina N`kenta. Sai karin wasu ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane masu zaman kan su daga Nijeriya da Amurka da suka halarta.

BAYANAN DA `YAN MAJALISUN DOKOKI NA AMURKA DA NA BIRTANIYA SUKA YI A WAJEN

Na yi matukar kaɗuwa da na ji yan majalisun dokoki na Amurka da jamian gwamnati da suka yi ritaya suna ta maimaita ambaton sunan Nijeriya a wannan kawance kamar sunan su ƙasar Sin (China) da Fakistan, da Afghanistan a matsayin daya daga cikin ƙasashen da suke kan gaba wajen hana `yanci da walwalar addini, inda suke zalunta da tsananta wa Kiristoci da Coci-Coci.

WASIƘA ZUWA GA BABBAN SAKATAREN HARKOKIN WAJE NA AMURKA DA SANATOCI 5 NA AMURKA SUKA RUBUTA.

A ranar 5 ga watan Yuni na 2022, Sanatoci guda biyar na Amurka suka rubuta wa Babban Sakataren Harkokin Wajen Amurka wasiƙa da ke neman ya dakatar da shawarar da ya yanke ta cire sunan Nijeriya daga cikin jerin sunayen ƙasashe da ake da damuwa ta musamman da su wato (CPC) a takaice. Sanatocin sun yi wadannan ƙorafe-ƙorafe a wasiƙar tasu:

i. “Kawai da zarar ka ambaci cewa kai kirista ne, sai ka zama abiin kisa a sassa da dama na Nijeriya

ii. An kashe kiristoci `yan Nijeriya su fiye da 4,650 saboda imanin da suka yi da addinin su a 2021

iii. A shekaru biyu a jere Nijeriya ta zama kasa mafi tsananin haɗari a doron ƙasa ga Kiristoci.

iv. Gwamnatin Nijeriya ta gaza wajen kare yancin walwalar addini da kuma kare kiristociyan ƙasa.

v. Gwmnatin Nijeriya na shiga kai tsaye, cikin zalunci da tsananta wa Kiristoci ta dokokin hana aikata sabo.

Tsokacina: A matsayina na dan ƙasar Amurka, abin ya yi matukar ba ni kunyar wadannan sanatoci za su iya rattaba hannunsu a wannan takarda alhali suna da matukar masaniyar akwai kuɗaɗe da kayan aiki a gare su, da za su iya nemo gaskiyar lamari. A gaskiya a gani na an rubuta wannan wasiƙar ce kawai domin daɗaɗa wa jamaarsu masu gajeren tunani ba tare da laakari da ainihin gaskiyar lamari ba.

BAYANAN DA WASU `YAN NIJERIYA DA KUNGIYOYIN KIRISTOCI SAKA YI A WAJEN

Haka nan akwai firgitarwa idan aka ji bayanan da wasu `yan Nijeriya suka yi a wajen kamar yadda aka takaita su a ƙasa:

i. Yan Taadda Fulani da Kanuri (Barebari) suna ta kai wa Kiristocin Nijeriya hari tare da kashe su.

ii. Musulmi masu ɗauke da makamai suna harar Kiristoci da Coci-Coci da gangan da cikakken hadin bakin gwamnati

iii. Dokar hana sabo da ta ba da damar kashe Deborah Yakubu Samuel a Sakkwato

iv. `Yan Matan Chibok da a yanzu haka suka kwashe shekaru 8 a hannun ƙungiyar Boko Haram

v. Leah Sharibu da a yanzu haka ta kwashe shekaru 4 a hannun Boko Haram saboda ta ƙi ta watsar da addinin kirista ta zama musulma

vi. Bishop na Cocin Katolika na jihar Ondo ya gabatar da wani bayani da ke neman duniya ta taimaka, bayan ikirarin da ya yi cewa a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni na shekarar 2022, wasu Fulani yan taadda ɗauke da makamai sun yi wa masu ibada su a ƙalla 40 da ke yankinsa na cocin katolika na St Francis da ke Owo kisan gilla.

vii. Wani Lauya Kirista ya sanar da taron cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wata doka da ke buƙatar masu waazin addinin kirista kawai, su nemi lasisi tukuna kafin su yi waazi.

viii. Wani zargi da ke cewa Hukumar Zabe ta ƙasa (INEC) ta samar da rumfunan zaɓe fiye da 20 a Jumhuriyar Nijar domin bai wa Musulmi da ke waccar kasa damar zaben dan takara Musulmi Bafulatani dan Nijeriya.

ix. Barazanar ballewa daga Nijeriya idan ba a sake zama an tattauna a kan Nijeriya ba.

AN YI SHIRU A KAN WADANNAN

i. Yan Fashi daYan Boko Haram sun fi yi wa Musulmi kisan gilla fiye da Kiristoci.

ii. Wadannan kungiyoyin yan taadda sun kashe Musulmi masu waazi fiye da Kiristoci Masu Waazi

iii. Musulmi masu riƙe da sarautu da aka kashe ko sace, sun zarce yawan na Kiristoci da aka yi wa haka

iv. Masallatai da yan taadda suka kona ko lalata, sun haura yawan Coci-Coci da aka yi wa haka.

v. Musulmi ciki har da yara da wadannan yan taadda suka sace, sun haura yawan Kiristocin da aka yi wa haka

vi. Jihohi da Musulmi suke da rinjaye wadannan yan taadda sun fi ƙarfi a cikin su, fiye da jihohin da Kiristoci suke da rinjaye.

vii. Matsalar tsaro ta fi talauta `Yan Nijeriya Musulmi fiye da Kiristoci

viii. Ga Harira Jubril Bafulatana Musulma mai tsohon ciki daga jihar Adamawa tare da yayanta ƙanana su 4 da `yan aware na Inyamurai (ESN) suka harbe su da bindiga a lokacin da suke tsaye suna neman mota a Karamar Hukumar Isulo Orumba ta Arewa da ke jihar Anambara.

ix. Wani Gwamna daga Kudu Maso Kudu ya girta cewa jiharsa jihar Kiristoci ce kuma ya rushe masallatai.

x. Fulani Makiyaya masu bin doka da aka fille musu kai, aka kashe musu shanu, aka banka wa rugagen su wuta, aka fatattake su daga kudu don kawai saboda da su Musulmi ne.

xi. Dokar da ta saba wa kundin tsarin mulki da jihohin kudanci 17 suka kafa da ta hana Fulani Musulmi Makiyaya shiga jihohin domin, kawar da su daga kasar da suka gada tun kaka da kakanni.

xii. Ga direbobin manyan motoci da masu tsire da aka ƙona su aka kashe su a kudu maso gabashin ƙasar nan.

xiii. Haramta wa `yan mata Musulmi sa hijabi a makarantun wasu jihohin kudu.

KAMA HANYAR KOMOWA GIDA DAGA WASHINGTON DC

i. An sanar da duniya ƙarairakin cewa ana kisan Kiristoci kuma ana zaluntar su a Nijeriya

ii. Yan majalisun dokoki na Amurka da na Birtaniya suna da murɗaɗɗen raayi a kan addini a Nijeriya

iii. Kungiyoyi masu ƙarfin kamun ƙafa na addini da ke Nijeriya tare da taimakon ƙawayen su na ƙasashen ƙetare, sun kwashe shekaru suna yaɗa ƙarya a game da Nijeriya, ga mutane da shugabannin ƙasashen turai.

iv. Matsalar Nijeriya ba ta addini ba ce illa ta rashawa da rashin shugabanci na gari daga shugabanninmu ko da kuwa a wanne addini suke.

v. `Yan Nijeriya da ke Nijeriya ne kaɗai za su iya magance matsalar Nijeriya ba a Landan, ko Washington ko can wani waje ba.

vi. Akwai bukatar Musulmi `Yan Nijeriya mu rƙa faɗin namu labarin da kan mu na zahiri ta amfani da kalaman mu, da ayyukanmu a gida da kuma ƙetare.

vii. Akwai buƙatar gwamnatin Nijeriya da jakadunta da suke ƙasashen waje, su zanta da abokanmu da ƙawayenmu na ƙetare, domin gyara wadannan labarun ƙarya da ake baza wa.

viii. Shugabannin dukkan addinai, suna da muhimmiyar gudunmawar da za su ba da a ci gaba da zama masu isar da saƙonnin alheri da kuma sasantawa.

ix. Nijeriya kasa ce kyakkyawa da ke da dinbin alkawura da wadatacciyar dama ga kowa da kowa.

“YUNƘURIN JUYIN MULKI”
Ana tsaka da wannan mawuyacin hali ne na ci gaba da faɗaɗa gibi na rashin aminta da yarda da juna bangaren addini a ƙasa, da da masu yada ƙaryar ana yi wa Kiristoci a Nijeriya kisan ƙare-dangi, sai aka wayi gari a Nijeriya da labarin wasu hafsoshin soja sun yi yunƙurin juyin mulki.

Shalkwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce sam atabau babu gaskiya a rahotannin da ake ta yaɗawa na yunƙurin juyin mulki, amma kuma ta fitar da sanarwar cewa an kama hafsoshin soja 16 kuma ana bincike a kan su, saboda aikata rashin da`a da batutuwa na rashin samun ƙarin girma.

Musanta batun da Shalkwatar Tsaron ta yi, ba ta wani kwantar da hankalin al`umar ƙasa ba; illa ma haifar da ƙarin raɗe-raɗin da suka sa sojoji suka rasa ƙarfin tarbe labarun da suke ta kai komo a soshiyal midiya. Ya kuma haifar da ƙarin tambayoyi fiye da samun amsoshi.

Babbar tambayar da ke cikin zukatan yan ƙasa ita ce shin da gaske ne an yi yunƙurin juyin mulki ko ba a yi ba? Me ya sa Hukumar Tsaro ta Lamuran Sirri (DIA) a taƙaice ce ke tafiyar da batutuwan na daa da rashin samun ƙarin girma, alhali wadannan dalilai da Shalkwatar Tsaro ta bayar na kama jami`n sojan su 16, mun san cewa batutuwa ne da akan tafiyar da shi a matakin Sashe.

Me kuma yan Nijeriya za su iya tunani a game da raɗe-raɗin da ake yi cewa wasu daga cikin hafsoshin sojan da aka kama, maaikata ne a ofishin Babban Mai Ba Da Shawara na Musamman Bangaren Tsaro (ONSA)? Me ya kawo batun hafsoshin soja da ke ofishin ONSA su yi juyin mulki?

Jerin sunayen hafsoshin soja 10, da aka ba da rahoton suna cikin 16 da aka kama, yana ta yawo a soshiyal midiya; shalkwatar tsaron ta kama bakinta ta yi gum a kan sahihancin sunayen.

9 daga cikin hafsoshin 10 da ke cikin jerin sunayen, wato kashi 90, dukkan su daga Arewacin kasarnan ne. Ina fatan Shalkwatan Tsaron ba tana sa ran mu amince da wannan jerin sunayen a matsayin gaskiya ba ne.

Ana nufin duk wannan jita-jita ce da kuma wani shiri da aka kitsa domin rage hafsoshi da suka fito daga wata shiyya ta siyasa ta kasarnan, da ake mata kallon tana adawa mai zafi da jam`iyyar da ke mulki a daidai lokacin da zaben 2027 ke ci gaba da karatowa?

A ranar 24 ga watan Oktoban nan na 2025 aka maza aka hanzarta sauya Manyan Shugabannin Hafsoshin Tsaro, matakin da ke ƙokarin gaskata rahotannin da soshiyal midiya take ta yadawa cewa an yi yunƙurin juyin mulki.

Sai dai kamar yadda ya saba, Shugaba Tinubu ya ci gaba da ajandarsa ta nada Yarbawa a muƙamai, inda ya maida gurbin dan arewa da ke riƙe da muƙamin Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS) da dan uwansa Bayer, wanda shi ne ya kamata a soma kora saboda waɗanda ake zargi da yunƙurin juyin mulkin, daga sojojin da yake yi wa shugabanci ne.

Gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne, ya kamata wannan tsoro na juyin mulki, ya farkar da Shugaban ƙasa Tinubu in ma bacci yake yi to ya farka, cewa akwai fa rashin gamsuwa a tituna, da gidaje, da kasuwanni, da azuzuwa, da ofisoshin gwamnati, da barikoki, da kuma fagen daga. Adalci da mulki na gari ne kadai zai kawo sauƙin matsalolin Nijeriya amma ba saukar da Manyan Shugabannin Hafsoshin Tsaro ba.

Usman Yusuf Farfesa ne a Fannin Nazarin Cututtuka da Suka Shafi Jini da kuma Dashen Bargo

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.