Home » Karamar Hukumar Sumaila Ta Kaddamar Da Aikin Gina Hanya Daga Gani Zuwa Gari Dambazau

Karamar Hukumar Sumaila Ta Kaddamar Da Aikin Gina Hanya Daga Gani Zuwa Gari Dambazau

Stallion Times
6 views
A+A-
Reset

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sumaila, Farouk Abdu Sumaila, ya kaddamar da fara aikin gina muhimmiyar hanya da za ta haɗa Gani da Gari Dambazau domin inganta sufuri da cigaban tattalin arzikin yankin.

farouk abdu sumaila yace aikin hanyar yana cikin shirin gwamnatin ƙaramar hukumar na ci gaba da inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da kyawawan hanyoyi, bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma sauƙaƙa zirga zirga tsakanin al’ummomin yankin.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Sumaila, Alhaji Adda’u Aminu Liman, ya yaba da wannan muhimmiyar nasara tare da bayyana cewa aikin zai taimaka wajen inganta rayuwar jama’a ta fuskar sufuri, kasuwanci, da samun sauƙin zuwa cibiyoyin kiwon lafiya da ilimi.

Shi ma Kansilan Mazabar Gani, Rabiu Adam Bagagari, ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙaramar Hukumar bisa cika dogon burin al’ummar Gani da makwabtansu na samun hanyar mota mai kyau. Ya kuma tabbatar da cewa al’ummar yankin za su ba da cikakken haɗin kai domin ganin an kammala aikin cikin nasara.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne tare da halartar manyan baki da suka haɗa da shugabannin gargajiya, wakilan al’umma da jami’an gwamnati, waɗanda suka yaba da irin namijin kokarin da gwamnatin Ƙaramar Hukumar ke yi wajen tabbatar da ci gaban ƙauyuka.

WhatsApp channel banner

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.