Home Opinion Ya Cancanta A Yaba Wa Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan

Ya Cancanta A Yaba Wa Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Jamilu Uba Adamu

Akwai lokacin da ya kamata, ya kuma dace a yaba wa wanda kuka yi abin a yaba masu.

Haka ne ya sa na ga dacewar yin wannan rubutun don dacewar na yaba wa mutumin kirki, mutumin ƙwarai, mai taimakon matasanmu ƴan asalin jihar Kano, wato shugaban hukumar ƙwallon kafa ta jihar Kano, Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan.

Ga waɗanda suka san Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan, sun san tarihin gudunmawar da ya bayar (tun kafin Allah Ubangiji ya kai shi matsayin da yake riƙe da shi a yanzu) a tsawon lokaci mai yawa wajen haɓaka ƙwallon ƙafa a jihar Kano, kuma har kawo yanzu da yake kan matsayin shugaban hukumar wasan ƙwallon ƙafa ta jihar Kano.

Kamar yadda na shaida da kaina, kuma na taɓa rubutawa a cikin wani rubutun da na taɓa yi a kan wannan bawan Allah mai kishin jihar Kano, da yan asalin jihar Kano, a wata haduwa da muka taɓa yi da shi wacce wannan haɗuwa da muka yi ita ce ta farko da muka taɓa yi da shi a garin Aba da ke jihar Abia a cikin filin wasa na Enyimba. Ina faɗa masa daga Jihar Kano nake ya karɓe ni cikin farin ciki tare da annashuwa. Ya riƙe hannuna ya zaunar da ni kusa da shi muka kalli wasan ƙwallon ƙafar tare. Wannan karrama mutanen da sanin darajar ɗan’adam a cikin halinsa yake.

Kullum ƙoƙarin da yake na taimaka wa matasan ƴan ƙwallon ƙafa na Jihar Kano wajen bunƙasa wasan ta hanyar ɗaukar nauyin gasar wasan ƙwallon ƙafa daban-daban a dukkanin lokuna da unguwannin da ke cikin ƙanana n hukumomi 44 da ke jihar Kano abun yabawa ne ƙwarai, kasancewar hakan yana samar da hanyar cigaban wasan ƙwallon ƙafa daga tushe, da zaƙulo zaratan matasa ƴan asalin jihar Kano masu basira.

Abin farin ciki ne; abin a ƙara yaba wa Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan wajen irin gudunmawa da taimakon da yake bai wa matasan ƴan wasan ƙwallon ƙafa ƴan asalin jihar Kano waɗanda suka samu damar wakiltar ƙasa Najeriya da waɗanda aka gayyata zuwa sansanin ƴan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa rukunin ƴan ƙasa da shekara ashirin (U-20), da kuma gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afirka da aka kammala.

Duk mai bibiyar wasannin ƙwallon ƙafa dai ya kalli matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Alhassan Yusuf, ɗan asalin jihar Kano a gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afirka, kuma tabbas duk wani ɗan asalin jihar Kano, musamman masu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa, na matuƙar farin ciki da wannan abin alfaharin.

A yanzu haka yan wasan ƙwallon ƙafa guda huɗu ƴan asalin jihar Kano da suka haɗar da Ibrahim Abdullahi Carrick, da Sulaiman Idris Manu, da Yusuf Abdullahi, da Rabi’u Abdullahi (Fele) suna sansanin horaswa na ƙungiyar ƙasa Najeriya ta ƴan ƙasa da shekara ashirin (U-20).

Samun wannan nasarar shigar yaranmu na Kano zuwa wannan mataki ba ƙaramin abin farin ciki ba ne a wurin duk mai kishin cigaban ƴan wasan ƙwallon ƙafa na Jihar Kano, amma abin yabawar  bisa samun wannan cigaban shi ne Dakta Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan, duk kuwa da cewar shi ba mutum ba ne da ke son a yaba masa. To amma wannan yabo ya zama dole.

Dakta Sharu ƙoƙarin da yake wajen samar wa matasanmu cigaba abu ne da zai wahala ya ɓuya, kuma na tabbatar tarihi zai masa adalci, musamman cigaban da ake samu a ƙarƙashin jagorancinsa na shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta jihar Kano.

Fatan Allah Ubangiji ya bashi ikon ci gaba da wannan taimakon matasan da yake. Allah Ubangiji ya ƙara bashi ƙarfin gwiwa da karsashin taimaka wa Jihar Kano da ƴaƴanta a harkokin wasan ƙwallon ƙafa. Amin.

You may also like

©2024. Stallion Times Media Services Ltd. All Rights Reserved.