Home Sports Tarihin tsoffin yan wasan da suka taka rawar gani a kwallon kafa a tarihin Jihar Kano

Tarihin tsoffin yan wasan da suka taka rawar gani a kwallon kafa a tarihin Jihar Kano

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Daga Jamilu Uba Adamu

Waiwaye akace shine adon tafiya, Kuma Masu iya magana kance “Tuna baya shine roko”

Jihar Kano tun lokaci Mai tsaho ta shahara ta Kuma Kafa tarihi mai yawa a harkokin wasanni, musamman Kwallon Kafa ba anan arewa Kadai ba a duk ma fadin tarayyar Najeriya.

Amma sai dai ba kasafai masu kula da harkokin wasanni suke damuwa da ajiye tarihin wasanni ba. Dan haka nema mafi yawan masu bibiya da shawa’rar wasannin na Wannan zamanin basu da cikakken sanin tarihin abun da ya faru a baya na gameda rawar da jihar ta taka a wasan Kwallon Kafa ba.

Bisa Wannan dalili ne, naga dacewar rubuta Wannan dan takaitaccen tarihin wasan na Kwallon Kafa a wannann shafin.

A Kamar dai yadda tarihi ya nuna, wasan Kusa da na karshe a shekarar 1970 Yan wasan Kwallon kafar da suka wakilci jihar Kano a gasar kofin kalubale na Kasa, Wanda aka fafata a filin Wasa na Liberty dake garin Ibadan, tsakanin Yan wasan Kwallon kafar Kano XI da Kungiyar Kwallon Kafa ta Warri Wolves.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Warri Wolves ce tai Nasara akan Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano da ci biyu da daya 2-1.

Amma sai dai kamar yadda tsohuwar Jaridar New Nigeria ta ranar litinin biyar ga watan janairu na shekarar alif dari tara da Saba’in (1970) ta rawaito cewar duk da rashin nasarar Kungiyar Kwallon kafar ta Jihar Kano, sun taka rawar gani da nuna kwarewa a wasan Kwallon Kafa, Wanda Yan kallo na Garin Ibadan baza su taba mancewa ba, dan sunga iyawa da kwarewa a wajen Yan wasan na jihar Kano.

A cikin Yan wasan da tarihi bazai mance da su ba a wannan fafatawa a garin na Ibadan sun hada da; Mai tsaran raga Ayuba Abdul, Labaran, Godwin, Sagir Garba, Ayo Fagge, Captain Solomon, Idris Aloma Fagge, Ibrahim Abba Fagge, Bala Hobe, Sale, da Koci Sidi Fagge.

Dan wasa Ibrahim Abba Fagge (Tsohon daraktan hukumar Wasanni na Jihar Kano) ne ya samu Nasarar sa Kwallo daya da Kungiyar ta Kano ta jefa a ragar Warri Wolves, ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaran raga, a minti na Saba’in a wasan.

Haka Kuma tarihi ya bayyana cewar Babban Bako na musamman a Wannan Rana ya kasance Gwamnan Mulkin Soja na Mid-Western States, Samuel Ogbemudia, tareda Kwamishinan sa na tattalin arziki da cigaban al’uma.

Tarihi ya tabbatar Jihar Kano ta taba lashe wannan gasa dai a karon farko ne a shekarar 1953.

Alhaji Muhammadu Dan Wawu shine yake jagorantar al’amuran wasanni a wancen zamani, kamar yadda tarihi ya tabbatar. (Allah ya gafarta Masa)

Karin Bayani: an samu mafi yawan wanann tarihi a sashin wasanni na Jaridar New Nigeria kamar yadda aka bayyana a Tarihin.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00