Home Opinion Ga Wadanda ke Alankata Garin Kwankwaso da Cewar Inyamuri ne ya Kafashi, ga Kadan Daga Tarihin Garin

Ga Wadanda ke Alankata Garin Kwankwaso da Cewar Inyamuri ne ya Kafashi, ga Kadan Daga Tarihin Garin

- Tarihin Mallam Ibrahim Dabo da Kuma Alakarsa da Garuruwan Kanwa da Kwankwaso Dake Ƙaramar Hukumar Madobi, Jahar Kano

by Isiyaku Ahmed
0 comment
Kano

Daga Abdulbaqee B. Ango (Gidan Fulani Kwankwaso)

Fulanin garuruwan Kanwa da Kwankwaso na da nasaba ko alaƙoƙi fiye da guda goma da Mallam Ibrahim Dabo (1819-46) Sarkin Kano na biyu a daular Fulani.

Wadannan alaƙoki sun kasance kamar haka:

1. Mallam Mamman Ɗan Hawa da sauran ‘yan uwansa kamar yadda za mu kawo su daga baya, sun kasance ‘ya ‘yan Shehu Umaru ne. Shi kuma Mallam Mahmudu mahaifin Mallam Jamo da Mallam Ibrahim Dabo sun kasance ‘ya yan Mallam Abdulmalik ne. Shi Shehu Umaru da Abdulmalik wa ne da ƙane, ma’ana mahaifinsu guda, da ake kira Modibbo Ibrahim Ƙwairanga ɗan Mallam Muhammadu Nafate, kuma dukkanin su an haife su ne a garin Dange-Shuni da ke yankin Gobir a wancan lokacin.

Mallam Ibrahim Kwairanga an bayyana cewar ya auri qanwa a wurin Muhammadu Fodi, wato mahaifin Shehu Usman dan Fodio kenan.

2. Bayan da sukayi ƙaura zuwa yankunnan qasar Kano gabanin Jihadin Shehu Usman Ɗanfodio, sun zauna a ɓangaren Kudu maso Yammacin Kano da suka haɗa tun daga ƙasar Lambu, Yalwan Ɗanziyal, Cishema ya tsallaka Kogi zuwa Kwankwaso da Kanwa. Mallam Mahmuda (Mahaifin Mallam Jamo da Mallam Ibrahim Dabo) ya zauna a unguwar Raɗawa da ke a garin Cishema, har zuwa rasuwar sa kuma bayan ya rasu an binne shi can, qabarinsa ya nan har zuwa yanzu. Su kuma ‘yan uwansa su Mamman Hawa da sauransu, da kuma shi ɗan  Mallam Mamuda  (wato Mallam Jamo) sun zauna a garuruwan Kwankwaso da Kanwa.

3. Mallam Jamoh ɗan Mahmuda (kuma ɗan’uwa ga Ibrahim Dabo) ya kasance wakilin wannan jinsi na Sulliɓawa, a Kwamitin SHURA ko Kwamitin ƘOLI na harkar aiwatar da Jihadi a Kano, ma’ana ‘yan uwansa sun amince da ya jagorance su a duk harkokin na jihadi. Mallam Jamo yayi aiki tare da jagororin sauran gidajen hijira guda bakwai da suka haɗa da Mallam Yunusa Dabon Danbazau daga Dambazawa, Mallam Jibir da Mallam Goshi daga Ba’awa/Yolawa, Mallam Bakatsine daga Joɓawa, Mallam Danzabuwa daga Danejawa, da kuma Mallam Usman Bahaushe daga al’ummar Hausawa.

4. Bayan rasuwar Mahmuda a garin Cishema, Mallam Mamman Dan Hawa ya ɗauki Ibrahim Dabo lokacin yana yaro yaci gaba da zama da shi acan garin Kwankwaso.

5. Lokacin da Mallam Ibrahim Dabo ya kai matsayin matashi yayi yawace-yawacen karatu da yakaishi ga Qasashen Nupe, Borno da kuma Zazzau, duk alokacin yana hannun Mamman Hawa. San da Mallam Ibrahim Dabo yakai munzalin aure Mallam Mamman Hawa ya ɗauki ‘yar sa Naiwa ya aura masa, wato a matsayin auren saurayi da budurwa kenan. Wannan auren kuma, babban ƙaninsa Mallam Yusuf Turaki Gandi ne ya ɗaura shi.

6. Daga cikin ’ya ‘yan da Mallam Ibrahim Dabo ya haifa da matarsa Naiwa akwai Dan­­-Lawan Yusuf, Chiroma Mamuda, A’isha Kumbota (wadda ta dalilin ta ne akasami asalin sunan garin Kumbotso) kuma ita ta auri Madaki Nayaya inda ta haifi Madakin Kano Kwairanga, sai dan autan ita Naiwa wato Zubairu.

7. Wasu dalilai sun sa Mallam Ibrahim Dabo yayi ƙaura daga Kwankwaso zuwa wurin ɗan’uwan mahaifinsa wato Sarkin Kanwa na farko, Abubakar. Cikin dalilan da magabata suka bayyana mana da yasa hijirar Mallam Ibrahim Dabo daga Kwankwaso zuwa yankin Kanaburai na ƙasar Kanwa, shine yadda baijin daɗin zama da amaryarsa Naiwa ba, saboda izza da wasu halaye irin nasu na mata da take nuna masa. Kanaburai da wani ɗan kwazazzabo ne, kudu daga cikin garin Kanwa. Har zuwa yanzu akwai wani wuri a wajen da akayi ittifaƙin ƙabarin wani (Waliyi) bawan Allah ne anan, kuma lokacin baya can ana ganin wani haske na tashi cikin dare daga ƙabarin. Lokutan baya ana zuwa har wurin neman tabarraki musamman lokutan fari idan an fita roƙon ruwan sama, kuma Allah yasa ana dacewa.

Daga bisani, Mallam Ibrahim Dabo kuma, ya sake yin hijira zuwa cikin birni  wurin ɗan ‘uwansa Mallam Jamo a lokacin nan yana Sarkin Dawaki Maituta. Hakan yasa ake masa laƙani da Dabon Kanwa, don a bambanta su da Sheik Mallam Yunusa da akema lakani da Dabon Dambazau a wancan lokacin.

8. Turaki Gandi yayi ma Mallam Ibrahim Dabo ƙwarƙwara da Hadiza ‘yar Mallam Suleiman Barinje anan Kwankwaso wadda kuma ta haifa masa ‘ya ‘ya ciki har da Suleimanu Kurma. Shi dai Suleimanu Kurma ya sami lalurar kurumta ne bayan rasuwar mahaifinsa, dai-dai lokacin da shima yana cikin sahun gaba na ‘yan takarar neman sarautar Kano a wancan lokacin. Da lalurar ta same shi yayi ƙaura gaba ɗaya da iyalansa ya koma Cishema. Kuma har yanzu akwai zuriyar sa acan garin na Cishema.

9. Bayan rasuwar Mallam Ibrahim Dabo, da kuma kammala yakin Basasar Kano (yaqin da ya gudana tsakanin Jikokin Mallam Ibrahim Dabo zamanin Sarkin Kano Muhammudu Tukur 1883-5) wasu daga cikin jikokin sa da suka haɗa da Mahmuda da Abdulkadir ( wato ‘ya ‘yan Muhammadu Bello ɗan sa Sarkin Kano Muhammadu Tukur) sun sake komawa cikin dangin su a Kanwa da Kwankwaso, har yanzu wadannan zuriya na nan suna zaune a garin na Kwankwaso. Mahaifin wannan marubuci Adamu, jika ne a gurin Muhammadu Maude ɗan Usman ɗan Mahmud ɗan Muhammadu Bello ɗan Sarkin Kano Muhammadu Tukur.

10.  A shekarar 1903, Sarkin Kano Alu ya bada da umarnin tsare Madakin Kano Kwairanga a garin Kanwa. Hakan ya faru ne lokacin da wata taqaddama ta kaure a tsakanin su akan hanyar su ta zuwa Sokoto, dai-dai lokacin da suka tsallake Kogin Challawa, wato bayan tafiya kadan daga cikin Birnin Kano. Dalilin taqaddamar shine, lokacin da Turawa ke qoqarin shigowa Kano Sarkin Kano Alu ya yanke shawarar barin garin don yaje ya haxu da Sarkin Musulmi dake kan hanyar sa ta yin Hijira zuwa kasar Makka, a qoqarin sa shima na guje wa haɗuwa da Turawan.

Madakin Kano Kwairanga wanda yake ɗa ne awurin A’isha Kumbota ‘Ya a wurin Mallam Ibrahim Dabo, wato shi jikane a wurin sa kenan, ya bayyana ra’ayin sa na cewar ba kamata yayi su gudu su bar garinsu (Kano) don tsoron Turawa ba, abun da ya kamata shi ne su tsaya don qoqarin kare garinsu, Allah barshi idan ma an kashe su akan hakan, sunyi shahada kenan. wannan sa-in-sa bai yiwa Sarkin Kano Alu daɗi ba, saboda haka yayi umarnin tsare Madaki anan garin na Kanwa. Duk dacewar bayan kwanaki a tsare Madaki ya samu ya sulale cikin dare inda akace ya sami nasarar haɗuwa da Sarkin Musulmi, lokacin da yakai wajajen qasar Gombe. Shi kuma Sarki Alu, Turawa sun sami nasarar kamashi a wannan tafiya yayin da suka ɗauke shi zuwa Lokoja.

11. Sannan kuma, bayan da aka naxa Abbas sarauta, ya yansa Tafidan Kano Mamman ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, yayi ƙaura zuwan garin na Kwankwaso shima. don gudanar da harkar noma da kiwo. Ya tare da iyalansa, wato matansa, ‘ya ‘yansa, ƙwarakwaransa da bayin sa a wannan gari. Ya zauna anan gabas da gari, kusa da gidan Fulani.

Daga zuriyar sa akwai Muhammdu Sani sai Umaru (anayi masa lakabi da Imamu) da kuma Abdulkadir (da akewa lakabi da Galadima, wato saboda Galadima Abdulkadir na wancan lokacin kenan). Daga baya jikokin su da suka haɗar da Garba Sango sun sake yin ƙaura daga Kwankwaso zuwa cikin birni, kuma sunan zaune wajen Kofar Na’isa har zuwa yanzu.

Ƙarin bayanai, wato su dai asalin Fulanin Kwankwaso (waɗanda su suka kafa garin) sun haɗar da Mallam Mamman Hawa, Mallam Yusuf Turaki Gandi, Mallam Suleiman da kuma Usman. Sannan sai Mallam Abubakar da Mallam Jamo da kuma Mallam Wurno da su kuma su ka matsa gaba kaɗan suka kafa garin Kanwa. Don haka akewa Kanwa kirari da “Kanwa kafin Jamo”.

Kufan Gida Mamman Hawa shine a yanzu ya zama gidan sarautar garin Kwankwaso inda dagatan Kwankwaso ke zama a halin yanzu. Mamman Hawa ya kasance shine Sarkin Fulani na farko a garin na Kwankwaso daga shekarar 1808-1842. Akwai wata shaharriyar waƙa ta Bakandamiya ta Mallam Mamman Dan Hawa kamar haka:

“Shehu Salihu yaji ga Hashimu,

Shehu Hashimu yaji ga Mamman Tukur,

Mamman Tukur yaji ga Mamman Ɗan Hawa,

Wanda shikuma yaji daga Shehu Mujaddadi,

Uban Rufa’I uban Isan Kware.

Cewar lokacin rikicewar Duniya,

In ya gabato kowa ya sani. Mai shi a hana masa godiya,

Mai babu ko ahana masa dangana” haka nan waqen dai yaci gaba, kuma shaharraiyar waqa ce duk kasar Hausa har izuwa wannan lokacin.

Shi kuma babban qannin sa Mallam Yusuf Turaki Gandi ya kafa gidan sa ne anan qofar gabas, kuma shine ake kira da Gidan Fulani har izuwa yanzu. Kufan gidan ɗan uwansu Suleiman, shine rukunin gidajen da ake kira da zaure bakwai, annan yammacin garin na Kwankwaso, wato kusa da gidan shi Mamman Ɗan Hawa kenan.

Kufan gidan Usman kuma shine inda aka gina sabon asibitin garin Kwankwaso a halin yanzu. Dukkanin zuriyar su, sun a nan kuma suna cigaba da rayuwa a wannan gari na Kwankwaso da kuma wasu sassa dabam-dabam na Kano da ma wasu jihohin.

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, waɗannan ‘yan uwa Fulani jinsin Sulliɓawa da muka lissafo su, sun samo asalin su ne daga Kasar Dange-Shuni da ke yankin Gobir a wancan lokacin wato kasar Sokoto a yanzu. Kuma mun yi bayanin cewar, lokacin da guguwar Jihadi ta fara kaɗawa a zamanin Shehu Usman Ɗanfodio ‘yan uwansa fulani sun fantsama wurare da Ƙasashe dabam-dabam don koyar wa da kuma yaɗa Addinin Musulunci a wancan lokaci. Su waɗanna ‘yan uwa dama wasu sun zaɓi su yiwo ƙasar Kano. Akan hanyar su ta zuwa Kano kuma, sun zauna tare da kafa wani gari da ake kira Zandan a kasar Katsina. Don haka har izuwa yanzu akwai unguwa da ake kira Zandan anan yamma da cikin garin Kwankwaso

Zuwan su Kano sun kasance sun zaɓi su zauna kudu maso yammacin Kano, daga yankin Lambu, Yalwan Danziyal, Chishema har aka tsallaka Kogi zuwa Kwankwaso da Kanwa. Munyi bayani a baya dangantakar Abdulmalik da Shehu Umaru (wato cewar su ‘ya ‘ya ne a gurin Modibbo Ibrahim Ƙwairanga). Ma’ana shi Abdul Malik wane kenan ko ƙane a wurin Shehu Umaru, (mahaifin su Mamman Hawa, Yusuf Turaki Gandi, Suleiman, Abubakar da Wurno).

Mallam Mahmuda yayi yawon makaranta har izuwa ƙasar Borno, don haka ganin ƙwazonsa a fannin karatu da ilmi yasa Malaminsa Goni Bukar ya bashi auren ‘yar sa Halima kuma itace ta zamo mahaifiyar Mallam Ibrahim Dabo, don haka da yawa wasu al’ummar suke mashi kallon wai shi Kanuri ne. Wasu ma sun ce shi bazazzagi ne ko kuma Banupe, saboda zama tare da kuma yawon neman Karatun da ya kai shi izuwa ƙasashen su, wato ƙasar Kwasallo (a Zaria) da kuma Gulu (can yankin Nupawa wato ƙasar Bidda).

Amma dai maganar gaskiya shine Mallam Ibrahim Dabo Bafulatani Basulliɓe wanda aka haifa da shi da sauran wadanda muka lissafa a ƙasar Dange-Shuni ta Sokoto. Kuma tarihi ya nuna Kakkani ko Kakannin-kakannin su ma zuwa ƙasar Dange-Shuni sukayi daga Birnin Fez na kasar Morocco, can ma zuwa sukayi idan salsalar su ta tuƙe a birnin Silsilo na ƙasar Senegal. Hakan yasa ake musu laƙabi da Banu-Silsilo ta yadda akasamu wannan kalma ta Sulliɓawa kenan.

Lokacin da su Mamman Hawa za suyiwo kaura daga Dange Shuni zuwa Kano, Mahaifin Mallam Ibrahim Dabo baya gida yana Maiduguri, amma matar sa Halima tana nan a nan garinsu wato Dange-Shuni, kuma a dai dai lokacin tana ɗauke da tsohon cikin Mallam Ibrahim Dabo don haka ba ayo ƙaura da ita ba. Amma bayan haihuwar matarsa, dai dai lokacin da ya dawo gida daga Borno, Mamuda ya yanke shawarar bin ko tarar da ‘yan uwan sa da suka yi ƙaura zuwa Kano. Ya samu nasarar cimmu su a wani wuri da suka zauna don yi sansani ko zango, kuma a wannan lokacin matar jagoran tafiyar ta haifi ɗa namiji mai yalwan gashi; don suma ta lulluɓe masa duk jikinsa, don haka suke kiran yaron da suna ‘Rinji-Sunƙuru’ saboda sumar sa, hasalin kiran ƙauyen kenan da suna Rinji, kuma har yanzu kauyen na nan a ƙasar Gora Ƙaramar hukumar Madobi.

Bayan sun cimma shawarar ƙara matsawa gaba, alƙaluma da taurari sun nuna musu, su nemi tsakanin Koguna guda biyu, inda zasu zauna da iyalansu tare da sauran zuriyar su masu zuwa nan gaba. Gurin da ruwa ba zai musu wahala ba da su da zuriyarsu, kasancewar su manoma kuma makiyaya.

Waɗannan Koguna sune kogin da ya ratsa ta ƙasar DanShayi dake karamar hukumar Rimin gado, ya bi ta Challawa zuwa Tamburawa da kuma kogin Kura, don haka dalilin zaman su kenan tsakanin garuruwan Kanwa da Kwankwaso.

Sun ɗan zauna a yankin garin da ake kira a halin yanzu Kafin -Agur, kuma sun iske shi Agur ɗin wani Ba’azbine ne kuma yana kiwon raƙuma, kasancewar su makiyaya kuma manoma har sun ɗan samu takun saƙa dashi. Daga nan ne, zasu zo suyi saran daji, don kafa wannan gari na Kwankwaso idan dare yayi sai su koma Kafin, a haka har sai da suka kammala saran garin tsaf.

Lokacin da suke saran wannan garin, daga cikin ‘yan uwansu da suka haɗa da Abubakar, Wurno da Mallam Jamoh sun bada shawarar a ƙara dan matsawa kaɗan zuwa gaba, inda shi jagoran tafiyar Mallam Mamman ƊanHawa yaƙi amincewa da shawarar, har ya ƙara da cewar “Kun Ku So” “Kun Ku Ƙi”wato da lafazin Sakkwatanci, ma’ana ‘Ko Ku So” “Ko Ku Ƙi” anan zamu zauna dalilin kiran sunan garin KunKuso kenan, shine aka gurɓata sunan zuwa Kwankwaso bayan dogon lokaci.

Su Abubakar da basu aminta da zama nan ba, sai suka ƙara gaba zuwa inda yanzu ake kira Kanwa. Abubakar da Mallam Jamoh suka kafa garin, hasalin kirarin da ake ma garin kenan da Kanwa kafin Jamoh, duk da cewar daga baya Mallam Jamo ya koma gidan mahaifinsa a Cishema. Shi kuma ɗan uwan su Wurno sai ya ware yayi gidansa a wurin da ake kira Jamardawa yanzu, itama unguwa ce a ƙasar Kanwa. Asalin kiran wurin da Jamardawa, shine anayi musu laƙabi ne da suna ‘Jama’ar dawa’ wato waɗanda basu cikin gari kenan, shine har wurin ya koma Jamardawa.

Ita kuma ƙasar Kanwa ta sami asalin sunan ne, da alokacin da su Abubakar (Sarkin Kanwa kenan na fari) ya kawo ma ‘yan uwansu ziyarar nan Kwankwaso, sai suka ce masa, kaga muka ce kuzo mu zauna tare amma ku kun ware. Sai ya mayar musu da martani cewar to can inda muke ‘Kanwa Mukazauna’ ma’ana ba su zauna akan kowa ba ai. Dalilin da su ‘yan uwansu suke musu shaguɓe da cewar mutanen Kanwa, har kuma sunan kauyen ya koma Kanwa kenan.

Bayan da Mallam Ibrahim Dabo ya koma Kanaburai a Kanwa, kullum zaizo ya taɓa ɗan kasuwancin sa anan cikin garin Kanwa, ya bada karatu tare da jagoranci salloli anan gidan ɗan uwan mahaifinsa, Sarkin Fulanin Kanwa Abubakar idan anyi isha’i kuma ya koma can gidansa a Kanaburai.

Da ɗan uwansa Mallam Jamo ya koma cikin birni, kuma ya sami Sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta, sai ya nemi Mallam Ibrahim Dabo ya koma zama tare dashi. Ya nemi shawarar dan uwan mahaifinsa, Sarkin Kanwa Abubakar inda yayi masa bayanin kudurin sa na komawa gun dan uwansa acikin birni, tare da cewar da yardar Allah zai nemi Sarautar Kano in lokaci yayi. Sarkin Kanwa Abubakar yayi masa kyakkyawar fata tare da addu’ar Allah ya cika masa burinsa. Ya ƙara da cewar idan har Allah ya tabbatar, mudai a tabbatar mana wannan Sarauta tamu ta Sarkin Fulani Kanwa.

Bayan Mallam Ibrahim Dabo ya koma cikin Birni ya samu jagoranci a masallacin Jalli dake Yakasai, inda ya ke limanci tare da koyar da karatu. Sai Allah yayiwa limamin Galadanci rasuwa, wadda kuma shine limamin Gari a wancan lokacin, sai Sarkin Kano Mallam Suleimanu ya naɗa shi a matsayin limamin Galadanci kuma limamin Gari. Biyayyar sa da jarumtar da ya nuna a yaƙin da akayi a ƙasar Zazzau, tare da kusancin da Mallam Jamo da kuma irin goyon bayan da gudunmuwar da Mallam Jamo ya rika ba Sarki Suleimanu wajen tafiyar da mulkinsa (a lokacin da wasu daga gidajen Hijira suka ja da baya daga Fada) yasa Mallam Ibrahim Dabo ya shiga ran Sarki Suleiman. Hakan yasa Sarki Suleiman ya rubuta takarda zuwa Sarkin Musulmi cewar bayan ransa babu wadda ya fi dacewa da mulkin Kano kamar Dabon Kanwa wato Dabon Mallam Jamo. Kuma hakace ta kasance. Yadda Mallam Ibrahim Dabo har ya zama Sarki kenan a Kano.

Marubuta da dama sunyi rubuce-rubuce akan rayuwar Mallam Ibrahim Dabo, amma mafiya yawa sun fi mai da hankali ne, a rayuwarsa ta bayan ya zama Sarkin Kano. Haƙiƙa an shaida cewar cikakken Malami ne mai matuƙar taƙawa, tawari’u da kuma tsoron Allah. Sannan ga jarumta, hikima da fasaha tare da iya mu’amula da mutane.

Allah ya kai rahama ƙabarin sa tare da sauran dukkanin magabatan mu. Amen.

You may also like

Leave a Comment