Home Sports Yan Wasan Kick-boxing na Jihar Kano Sun Nuna Bajinta

Yan Wasan Kick-boxing na Jihar Kano Sun Nuna Bajinta

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Jamilu Uba Adamu

Yan wasan kick-Boxing na Kano sun samu nasarar zama matsayi na biyu a gasar da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Wasanni ta Jihar Kano Mallam Ibrahim Salisu Galadima ya futar

Ya bayyana cewar; Jihar Kano tai nasara a da samun Zinare guda hudu, azurfa guda biyu, da tagulla guda takwas.

Yan wasan, sun samu kyautar kudi naira dubu Ashirin, Dubu Goma da naira dubu biyar.

Jihohi Goma Sha daya (harda mai masaukin baki) ne suka shiga wannan gasa , Wanda ragowar suka hada da jami’an hukomomin damara daban-daban na Kasa.

A yayin da yake karbar Yan wasan na jihar Kano da sukai  nasara a wasannin na kick-Boxing a ofishin sa, Babban jami’an da ke jagorantar hukumar Wasanni,Kuma Uba a harkokin wasanni dattijo Alh Ibrahim Galadima, ya yabawa Yan wasan bisa hazakar da suka nuna, a wanann gasa, yace yan wasan sun samu nasarar lashe gasannin wasan kick-Boxing na Kasa sau har biyu Wanda aka gudanar a Jihar Delta da kuma Babban Birnin tarayya Abuja.

Alh. Ibrahim Galadima Kuma bada tabbacin cewar Yan wasan guje-huje, tsalle-tsale tareda motsa jiki na jihar Kano zasu hallarci Wasannin da a za gudanar na bikin wasanni da za a gudanar Garin Asaba, jihar Delta a anan gaba.

Yayi Kira ga Yan wasan da su cigaba da nuna  ladabi da jajircewa.

Shima ana sa jawabin, jami’i Mai kula da harkokin wasanni na kick-Boxing din, Mallam Nasiru Abdullahi, yayi godiya ga hukumar Wasanni ta Jihar Kano bisa damar da hukumar Wasanni ta basu Dan Hallarta wannan gasa da sukai. Ya Kuma yi alkawarin cigaba da daga darajar jihar Kano akoda Yaushe.

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00