Home Opinion Tunawa da Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu a Tarihin Wasanni a Jihar Kano

Tunawa da Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu a Tarihin Wasanni a Jihar Kano

by Editor
0 comment
Queen Elizabeth 11

Jamilu Uba Adamu

Sarauniyar Elizabeth wacce tarasu a satin da ya gabata Sarauniya ce wacce ta dade akan karagar mulki. Ta hau karagar mulki a Shekarar alif dari tara da hamsin da biyu, tana shekaru Ashirin da biyar kacal a duniya bayan rasuwar mahaifinta Sarki George VI (Sarki Geoge na Shida).

Sarauniyar Elizabeth ta shafe shekara saba’in da kwana dari biyu da Sha hudu tana mulki, Wanda hakan ya maida ita Sarauniyar da tafi kowace Sarauniya mace dadewa akan karagar mulki a tarihi. Dan haka an samu cigaba da tarihi daban-daban a zamanin mulkinta.

Anan jihar kano,tarihin al’amuran wasanni ya tabbatar dacewar  masarautar Ingila da mulkin mallakar datayi  Bayan cinye Kano da yaki da  turawan mulkin mallaka sukai a Shekarar 1903.

A Shekarar 1908 (shekaru biyar bayan cinye Kano da yaki) turawan mulkin mallaka suka samar da wajen wasanni su da shakatawa  a Kusa da gidajen kwanan su a unguwar Bompai.

Wanann wajen wasanni shine na farko da aka Samar yazama dandalin wasanni da shakatawa na turawan mulkin mallaka.

Kuma a tarihince kawun Sarauniya Mai Rasuwa Elizabeth, wato prince Edward (daga baya yayi sarautar kasar ta Ingila)  ya taba kawo ziyara filin wasan dake Bompai (Kano Club) a Shekarar 1927 (shekaru casa’in da biyar kenan yanzu) haryanzu kujerar da yazauna a wanann ziyara da yakawo tana nan a wanann filin Wasa.

Sarauniyar Elizabeth Mai Rasuwa itama dai ta taba kawo ziyara a Jihar Kano a cikin watan fabairu na shekarar alif dari tara da hamsin da shida (shekaru sittin da shida yanzu) a Wannan ziyara data kawo jihar Kano anan ne ta kafa ginin farko da aka cigaba da ginin filin Wasa na festival stadium (yanzu wanann fili ake Kira da Sani Abacha stadium , a Kofar Mata)

Wanda kafin zuwan nata filin ya kasance wajen dandalin wasanni na gargajiya.

Duba da Wannan tarihi da Sarauniya ta kafa a wannan filin wasanni dake Kofar mata, tarihin wasanni a Jihar Kano ba zai manta da gudunmawar da Sarauniya Elizabez ta kafa ba, musamman bisa la’akari da tarihin da filin ya Kafa daban-daban a harkokin wasanni da aka gudanar a cikin sa.

Za a iya tuntubar marubucin a jameelubaadamu@yahoo.com

You may also like

Leave a Comment